BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

“Ok ganinan”.

Juya kambun motan yayi yasauya hanya, minti 15 yakawo shi babban asibitin da Sameer yake aiki, bayan yayi packing fitowa yayi yashiga cikin asibitin, direct office ɗin Sameer yazarce, yana shiga yaganshi zaune yana cike wasu takardu, hannu yabasa suka gaisa sannan yasami waje yazauna

Sameer yace “just give me 10 mint don Allah yanzu zan ƙarisa sai mutafi”.

“Babu Matsala”. Khalil ɗin yafaɗa yana gyara zaman shi kan kujeran yalumshe idanun sa

“Ka gaji ko?”

Ɗan yamutsa face ɗin sa yayi ba tare da ya buɗe idanun sa ba yace

“Sosai ma, barci kawai nake ji wlh yanzu”.

Ɗan kallon sa Sameer yayi yace

“Wai ya maganar tafiyan ka ne? Har yanzu banji kace komi ba?”

Idanuwan sa yabuɗe yana kallon Sameer ɗin yace

“Zuwa Friday zan tafi”.

Jinjina kai yayi yace

“But Yakamata kayi taka tsantsan kasan Alhaji Mubarak ba ƙaramin mutum bane, don bani da shakka duk abun da kake shirya wa ana sanar masa, Ni yanzu maganar ma da nake so nayi maka kan Nazeefa ce, Yakamata kaciro ta daga wannan gidan kakaita wajen Mom hakan zai fi”.

Khalil yace “ai jiyan nan naɗauko ta namaida ita gida na, inaga can zata zauna”.

“Kana ganin babu Matsala?” Cewar Sameer

Gyaɗa masa kai kawai yayi

“Ok amma dai Yakamata kaƙara masu gadi, don nafi tunanin in har tana gidan ka zasu fi sanin haka, sannan kuma kaga kai tafiya zakayi Yakamata kaduba shawarata”.

Shiru Khalil yayi naɗan wasu sokonni kafin yace

“Ok Bro”.

Daga haka hira suka soma duk dai akan case ɗin Alhaji Mubarak, kafin Sameer yagama suka tashi suka fice, har gidan sa yasauke sa Sameer ɗin yace

“Baza ka shiga ba?”

Girgiza kan sa kawai yayi yace

“No kagaishe min dai da auntyna, sai wani lokacin zan shigo”.

Ɗan taɓe bakin sa kawai Sameer yayi yace

“Kunfi kusa ai”.

Kafin yabuɗe motan yafice, shi kuma yaja ahankali yatafi, a bakin Gate yadakata yadanna hon aka buɗe masa yashige, bayan yayi parcking motan yabuɗe yafito riƙe da briefcase ɗin sa a hannu, yafara tafiya cikin ƙasaita yanufi cikin gidan, hannun sa yasaka yabuɗe ƙofan yana ɗan motsa bakin sa yashige, tana tsaye wajen dainning table tana jera abinci taɗago kanta takalle shi, saurin sauke kanta tayi ganin sun haɗa idanu, cike da sanyin murya tace

“Sannu da zuwa”.

Gyaɗa mata kai kawai yayi yana ci gaba da kallon ta, ahankali yasoma takowa cikin Palon kafin yace

“Ina Nazeefa?”

“Tana ciki tana barci”.

“Tasha maganin ta?” Yasake jeho mata tambayan still yana kallon ta

Lokacin itama taɗago kai taɗan saci kallon sa dasauri taɗauke kanta tace

“Tasha”.

“Ok ki tashe ta taci abinci”.

“To Sir”.

Wucewa ɗakin sa yayi, ita kuma tabi sa da kallo tana jin tsananin ƙaunar sa na ƙara shigan ta, ɗauke kanta tayi bayan da yashige tana sauke ajiyan zuciya, tasan da cewa babu yanda za’ayi tasame shi, yafi ƙarfin ta tako ina koda a mafarki ne, haƙiƙa zuciyanta tayi ganganci da takamu da ƙaunar wanda be san ma tana yi ba, tasan da cewa zuciyarta ba ƙaramin yaudaranta take yi ba da har taso uban gidan ta a matsayinta na ƴar aiki. Ci gaba da jera dainning ɗin tayi kafin tagama tashige ɗaki

Shi kuwa yana shiga ɗakin sa kayan jikin sa yasoma ragewa kafin yashige toilet, be daɗe ba yafito yasaka farar singlate da Black Three qweater yafaɗa saman gado, sosai yake jin barci kuma gashi yana jin yunwa, sai dai bazai iya tashi yaje yaci abinci ba sabida tsananin barcin da yake ji cikin idanun sa, ai kuwa yana kwanciya babu daɗewa barci yaɗauke shi

Ba shi yatashi ba sai 05:04pm, yana buɗe kyawawan idanun sa yaɗaura kan agogon dake manne jikin bango, dasauri yamiƙe yana salati, direct toilet yawuce agurguje yayi wanka yaɗauro alwala yafito, jallabiya kaɗai yazira ajikin sa yashimfiɗa dadduma yagabatar da sallan asar, lokacin da ya’idar ne yaji wani yunwa na ƙwaƙwulan cikin sa, ɗan shafa cikin nasa yayi yana lumshe idanu kafin yabuɗe su yamiƙe tsaye, gaban sif ɗin sa yanufa yaciro kayan da zai sa, kafin yakoma gaban mirror yasoma shafa Lotions, sai da yagama sannan yasaka kayan sa, riga da wando ne, rigan kalan maroon ne me hoton kan sarki, daga saman ta an rubuta THE KING da black colour, haka ma wandon sa Black jeans ne, sai yazira room slippars yafeshe jikinsa da turare sai tashin ƙamshi yake yi, wayoyin sa yaɗauka yanufi palow, babu kowa ciki yanemi kujera a ɗaya daga cikin kujerun dainning yazauna, buɗe coolar’n gaban shi yayi yaga farar shinkafa ne zalla da yankakken hanta a sama, be da sha’awan buɗe sauran, plate kawai yaɗauka yaɗibi abincin yarufe, sannan yabuɗe coolar’n dake kusa da wancan ɗin yaga miya ce na jajjage wanda yaji kifi sai tashin ƙamshi yake yi, zubawa yayi yasoma ci ahankali yana yi yana latsa wayan sa

Nazeefa ce tafito daga cikin ɗaki sanye da doguwan riga ja me kwalliyan furanni, ta yafa gyalen kayan tana tafiya ahankali kamar wacce ƙwai yafashe mata a ciki, saman kujerun Palon tanemi wuri tazauna tana kallon shi, cikin sanyin murya tace

“Yaya ina wuni”.

Sai lokacin yaɗan ɗago kai yakalle ta naɗan wani lokaci kafin yamaida idanun sa kan wayan sa yaci gaba da abin da yake yi, can kuma ya’amsa mata da

“Lafiya”.

Shiru ne yabiyo baya, sai kuma tagyara zamanta tana kallon shi, gaba ɗaya hankalinta da tunanin ta yana gare shi, komi nasa yana matuƙar burgeta, to meyasa? Take tatuno sanda suka fara haɗuwa yataimake ta duk da bata cikin hayyacin ta, wani kyakykyawan murmushi tasaki tana jin zuciyarta na mata sanyi da daɗi, memakon tariƙa kukan maraici sai dai ko kaɗan yanzu ji take yi tamkar bata rasa komi nata ba, duk sanda tatuna fuskar sa tana ji ne kamar tafi kowa Sa’a a duniya

“Wannan wani irin yanayi nake ji haka? Meyasaka nake jin sa daban da sauran maza?”

Zuciyarta tayi mata wannan tambayan, batakai ga lalubo amsan ta ba taji muryan sa me tsananin daɗi a cikin kunnen ta yana faɗin

“Kidena yawo da yawa saboda aikin dake cikin ki, kiriƙa tambayan Lubna duk abinda kikeso bana son yawan fitowa nan in ba da ƙwaƙwƙwaran dalili ba”.

Nazeefa gyaɗa masa kai tayi, sai kuma ta’amsa mishi ganin baya kallon ta yayi maganan

“To Yaya”.

Tafaɗa cike da sanyin murya kafin tatashi tasoma tafiya don komawa ɗaki, ahankali take takawa har tashige, tana shiga Lubna takallo ta sai kuma taɗauke idanun ta taci gaba da tunanin ta, itama Nazeefa samun waje tayi gefen gadon tazauna tana tunanin Brr. Khalil, daga ƙarshe tazame takwanta tana rufe idanuwanta, tashi Lubna tayi tafice zuwa kichen don ɗaura abincin dare, koda tafito idanuwanta akan shi suka sauka, sosai yau yayi mata kyau duk da ko yaushe shi ɗin me kyau ne, amma yau sai takasa ɗauke idanunta akan sa har sai da tagama ƙare masa kallo kafin tashige kichen

Ahankali yamiƙe yanufi ƙofan fita, a Compound ɗin gidan yatsaya yajingina bayan sa da bango yana lumshe idanuwan sa tare da sanya hannun sa ɗaya cikin aljihun wandon sa, shiru yayi yana sauraron bugun zuciyan sa yana tunani, ya jima awajen har sai da yaji kiran sallah kafin yanufi inda me gadi yake yayi alwala anan, tare suka jera da me gadin da sauran ma’aikatan biyu suka nufi masallaci, shi dama ba ma’abocin girman kai bane ga masu aikin sa, wani lokacin ma in yasami time wajen su yake zuwa suyi ta mishi hira shi kuma yana kallon su, duk da baya magana amma sosai yake fahimtar su, wani lokacin har yaɗan dara in suna bashi labari me daɗi, acan suka baro shi sai da yayi sallan isha’i kafin yadawo gida, Direct saman dainnig yanufa yahaɗa tea yasha, ko minti 10 be yi ba yatashi yakoma ɗakin sa, acikin ɗakin da yake aikin sa yashige, kujera yasamu yazauna yajanyo lapton ɗin sa yasoma aiki ciki, minti 5 da soma aikin nasa yamiƙe yafita, briefcase ɗin sa yaɗauko yadawo yazauna, Computer yaciro da wasu ducuments yaci gaba da aikin sa, sai da ƙarfe 12:017pm yayi kafin yadakata yarufe lapton ɗin da Computer, tashi yayi yana miƙa cike da gajiyawa yafice yanufi Toilet, alwala kaɗai yayi yafito yasauya kaya zuwa kayan barci yakwanta tare da kashe fitila.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button