BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

.

_to nima bari in dakata anan, karku manta da_

*Like*

*Comments*

*Vote*

*Share*

_ina yin ku masoyana_ ????????????????????

[9/1/2020, 10:12 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *⚜{{F.W.A????}}*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 8*

Tafiya suke yi suna sanye da uniform, fitowan su kenan akan hanyan su tazuwa school, Halwa take bata labarin haɗuwan su da Yazeed jiya, ita kuma Zainab zai ɓaɓɓaka dariya take yi har da riƙe ciki

“Ke kiyi fa ahankali karki jawo mana mutane nan”. Cewar Halwa kenan tana kallon Zainab

“Ƙyale ni in dara, wlh kin bani dariya, hhhhh wai ke adole ga kurma, kai wlh banji daɗi ba da bana nan akai wannan draman, kawai lokaci ɗaya Allah yatoni asirin ki”.

Sai takuma kwashewa da dariya, Halwa bige mata kafaɗa tayi tana faɗin

“Ke fa tsiyata dake ba’a zancen arziƙi dake, yanzu sai kihau ma mutane wannan haukan naki, mtswww”.

Taja gajeren tsaki tana ɗaure fuska, sai lokacin Zainab taɗan sassauta dariyan da take yi tace

“Wooo kurma ta Yazeed yi haƙuri ban sakewa”.

Wani irin kallo tayi mata tace

“Gyara kalaman ki, kidena danganta ni dashi, kinsan dacewa ni ɗin mallakin Yaya Nura ne shi kaɗai, to dan Allah kidena bana so”.

Taɓe baki Zainab tayi tace

“Nafi kowa sanin haka ai, amma babu yanda Allah baya lamarin sa, yanzu sai kiga an sauya d..”

Saurin bige mata baki Halwa tayi tana faɗin

“Kull.. karki soma, wlh in kika ƙarisa sai an ji mu dani dake, Allah ni nakula ma kamar baƙin ciki kike min, to ta Allah ba ta ki ba, insha Allahu sai na zama mallakin Yaya Nura na sai dai kimutu”.

Zainab dariya tayi tace

“Hmmm yi haƙuri ƙawalli na dena, in kinso ma gobe aɗaura miki aure dake dashi, ni wlh bata shafen ba”.

Halwa tace “to ai ko bakice ba, ni inda za’abi ta shawarata wlh kafin muƙarisa wannan makarantan kawai aɗaura mana aure, domin ni a tsarina bana son nagama secondary batare da nashiga daga ciki ba”.

Baki Zainab tariƙe tana kallon ta

“Lallai Halwa kin ƙosa da yawa, amma bansan haka ba sai yanzu, to gaskiya Yakamata su Mama suyi saurin miƙa ki tun kafin aji sautin kiɗan ya sauya”.

“Ni da ma zaki taimaka min da yafi, kije kisanar mata tunda su har yanzu sun kasa sanin haka, wlh Zainab ina faɗamiki auren wuri daɗi ne dashi, kema dai ki aje wannan aƙidan naki kawai mu jone ayi mana tare ko ma huta, ko ba haka ba?” Cewar Halwa tana kallon Zainab tare da ɗage mata gira

Girgiza kai Zainab tayi tace

“A’a ke dai da kikaga zaki iya sai kiyi tayi, wai ma duka-duka nawa muke da har zamuyi aure, just 18years fa kenan, kinga ke kin riga da kin lume a soyayyan Yayan ki bazaki gane ba, amma ni bar ni sai na zaɓa Wanda naga ya dace dani, kuma wanda yafi kwantawa da ra’ayina”.

Halwa tace “ni fa nasan halin ki, be wuce kice me kyau kike nema ba, to me zai hana nahaɗa ki da Yazeed wlh zaku dace sosai, domin ya haɗu tako ina kamar dai yanda kikeso”.

“Haba dan Allah?”

“Wlh kuwa sai ma kin ganshi, nima ba ƙaramin burge ni yayi ba, sai dai kinsan tuni zuciyata ta riga ta makance ga wanin shi, babu wanda nake gani da zaifi min Yaya Nura na”.

Zainab taɓe baki tayi tace

“Na kula fa kamar ma kinfi son sa akan shi, ke dai baki da zance sai ta wani Yaya Nura, uhmmm Allah dai yanuna mana ranan, amma ni gaskiya ba yanzu zanyi aure ba, sai na yi nisa a karatuna”.

Daidai lokacin da wata keke napep tazo wucewa Halwa tatare tana faɗin

“Ameen inda gaske kike, kuma ko me zakice sai dai kice”.

Zainab batace komi ba in banda dariya da tayi, napep ɗin suka shige yaja suka tafi, a cikin motan ma hiran suke tayi har yakawo su, bayan sun sauka Halwa ce talaluba cikin jakan ta taciro gudan ɗari tamiƙa masa, har sun soma tafiya sai wata mota tasha gaban su, atare suka tsaya suna kallon motan, wani ingarman saurayi ne yafito, yana sanye da ɓakin singlate da farar wando Three qweater, jikin sa duk zanen tatue ne kai da gani kasan irin ƴan iskan nan ne waɗanda suke tsula tsiyan su cikin gari, wani shegen aski ne akan sa oho ni na manta sunan sa ma, wuyan sa duk sarƙoƙi ne har guda biyar, tun sanda yafito yazuba ma Halwa idanu yana wani irin murmushi tare da ɗage mata gira, ita kuma sai taɗauke kanta takama hannun Zainab zasu kewaya su wuce, wuf yashige gaban su yana ci gaba da bin ta da wani mayataccen kallo yace

“Babyna babu magana?”

Ko ɗago kai bata yi ba illa sake riƙo hannun Zainab da tayi tana son sauya hanya, yasake shan gaban ta yana cewa

“Wai Baby bakiyi missing ɗina bane? Meyasaka kike min haka ne? kinsan da cewa ina matuƙar ƙaunarki da sha’awanki why bazaki bani dama ba?” Yaƙarike maganar sa yana matso da fuskar sa kusa da nata still yana murmushi me ma’anoni da yawa

Ɗan ja da baya tayi tana yamutsa fuska kana tabi shi da banzan kallo, batace komai ba dai  tajuya da ninyan barin wajen gaba ɗaya sai ji tayi ya janyo mata Hijab, kiiiii sai gata tadawo gaban sa, yasanya hannu yariƙo hannun ta yana faɗin

“Common Baby sai yaushe zaki waye ne..”

Marin da tasauke mishi a fuska ne yakatse mishi maganar shi, sakin ta yayi yadafe kuncin sa da hannayen sa biyu yana kallonta cike da tsantsan mamaki, ba shi ba har Zainab sai da tatsora ta da marin da Halwa tayi mishi 

Muryan Halwan ne yakatse musu mamakinsu su duk ka biyun

“Wlh koda wasa kasake ɗaukan banzan hannunka me datti kaɗaura shi akaina sai nayi maka mafiyin wannan, banza ɗan iska”.

Tajuya zata tafi yayi saurin sake tare ta, cikin tsananin ƙunan rai kamar wanda zai kai mata duka wanda har sai da taɗan tsorata da ganin yanayin sa yace

“Ni kika mara Halwa? Ni Ko?”

Ɗan girgiza kan shi yayi yana sakin murmushin gefen baki yaci gaba

“Zan nuna miki waye Haris, wlh sai kinyi nadaman zuwanki duniya, sai nayi miki abinda har kimutu bazaki taɓa manta ni a rayuwanki ba tunda har kika iya cire hannu kikayi min abinda ba’a taɓa min ba, kijira kika me zai biyo baya”.

Yana faɗin haka yajuya dasauri yabuɗe motan sa yashige, har motan shi yayi nisa bata ɗauke idanunta kan shi ba, sosai tatsora ta da ganin yanayin sa, ita tasan waye Haris, ba ƙaramin tantirin ɗan iska bane batasan me zai biyo baya ba kamar yanda yace “tajira zata gani” amma kuma ko kaɗan batayi nadaman marin da tayi masa ba, inda tana da ƙarfin da zatayi mishi mafiyin haka to wlh sai tayi masa

Zainab ce takatse mata tunanin ta da faɗin

“Mun shiga uku Halwa me kikayi haka? Haris fa kika mara? kuma kinsan ko shi waye a garin nan, wlh sai yaɗaure kaf dangin mu babu wanda ya’isa yafiddo mu, meyasa dan Allah kikayi wannan ɗanyen aikin? Kinsan fa ba yau yasaba miki irin haka ba”.

Kallon ta Halwa tayi cike da jin haushin maganan ta tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button