BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50
Halwa wani kallo tayi mata sai dai batace komi ba tamiƙe taɗauki Veil ɗin ta tayi Rolling ɗin sa akanta, sai taɗau HangBag ɗinta tarataya, wayan ta a hannun ta suka fito tare da Saleeman, waje suka fice a tunanin su zasu ganshi sai dai babu shi be fito ba, a compound ɗin gidan suka tsaya suna taɓa hira har sanda sassanyan turaren sa yakawo ma hancin su cafka
Saleema kallon kyakykyawar Mijin nata tayi cike da tsananin ƙaunar sa
Ita kuwa Halwa tunda tayi masa kallo ɗaya taɗauke kanta
Zuwa yayi yawuce su yanufi wajen Farar motan sa yabuɗe yashiga
Su ma takowa sukayi har wajen motan, Saleema tabuɗe mata ƙofan tashiga tarufe mata
Tana nan tsaye har suka fice a gidan kafin taja numfashi ahankali takoma cikin gidan
Shiru cikin motan babu me motsin kirki ahaka sukai ta tafiya
Halwa ma duƙar da kanta tayi ƙasa tana faman juya wayan ta
Yayinda Khalil yake tuƙi amma hankalin sa gaba ɗaya yana kanta, so yake yi yacire duk wani abu dake cikin ransa a game da ita tunda yasan ita ɗin mallakin wani ne
Tafiya suke yi sosai babu me magana cikin su
“Ina ne gidan naki?”
Tatsinkayi sassanyan muryan sa me tsananin daɗi a kunnen me sauraro, ɗago kai tayi takalle sa kamar me tunani sai kuma taɗauke kanta tana faman maimaita maganar nasa aranta har sanda tafahimta sannan tabashi amsa
“Sabon layi”.
Kallon ta yayi kamar zai yi magana sai kuma yafasa, ya san cewa Sabon Layi ne gidan su Saleema, to amma taya ita zatace masa anan take? Sai kuma yayi tunanin maybe itama a anguwan take aure
Be sake magana ba har sanda yashigo cikin anguwan, yana jiran yaji ta nuna masa hanya ko wani gidan but shiru hakan yasaka yaci gaba da tafiya batare da ya sake tambayan ta ba
Sai da aka kawo dai-dai gidan su Saleema taga yana shirin wuce wa, takalle sa tace “Nan ne fa”.
Tsai da motan yayi kafin yayi Rivers yakoma baya yadanna horn me gadi yaleƙo sannan yabuɗe musu, tura hancin motan yayi cikin gidan sannan yayi parcking
Tana ganin ya tsaya tabuɗe motan sannan taɗan juyo takalle sa suka haɗa idanu tayi saurin janye nata cike da tsananin faɗuwar gaba
“Na gode”. Tafaɗa ahankali kafin tafice dasauri tarufe masa ƙofan tatafi
Har tashige yana kallon ta cike da mamaki aransa, yana da tarin tambayayo aran sa sai dai be san wanene zai amsa masa ba
Yasan da cewa Saleema ita kaɗai iyayen ta suka haifa bare yayi tunanin ƴar uwanta ce, sannan ma basu kama ko kaɗan, sai dai yana tunanin ko dangin ta ne
Motan sa yaja yabar gidan yanufi inda zai je.
*____________________*
Sallama tayi tashigo gidan agajiye
Umma ta’amsa mata tana kallon ta
Zuwa tayi tazauna akan tabarman da Umman take zaune
“Kin dawo?”
Gyaɗa mata kanta tayi tana me zame jakan ta kafin tace “sannu da gida Umma”.
“Yauwa Zainab da alamun dai yau kinsha wahala tunda naga kina langaɓewar nan?”
Zainab tace “uhm umma ai ba’a magana, wahala kam akwai ta, ko abinci yau ban iya ci ba tun safen nan wlh lectures yayi zafi”.
Sake kallon ta dakyau Umma tayi tace “sai kika zauna haka babu abinda kika ci? To ai dama Dole kisha wahala, ki tashi kije ɗakina ki ɗauko abincin ki”.
Miƙewa Zainab tayi don dama sosai cikin nata yake ƙwaƙulan ta, shiga ɗakin tayi taɗauko abincin tafito tazauna inda tatashi
Tana ci suna hira kuma duk na hiran makarantan ne
“Ni wlh dama zaki haƙura da karatun nan haka nan abu yaƙi ci yaƙi cinye wa, memakon ki samu miji kiyi aure sai ƙara karatun ma kike yi shi kuma ba me ƙare wa ba”.
Kumburo fuska Zainab tayi tace “Umma kema kinsan karatu nake so a yanzu, ban tashi yin aure ba shiyasa ma bana kula kowa a yanzu ɗin”.
“To wa yace miki karatu na hana aure ne? Tunda gashi kin soma ai abu me sauƙi ne Mijin naki yabar ki kici gaba, shiyasa wlh nake miki sha’awar auren Nura tunda shi yayi karatun kuma bana da haufi akan zai barki kiyi karatun ki”.
Tashi Zainab tayi tsam bayan da Umman nata tagama zayyano maganan, batace komi ba tashige ɗakin ta tafaɗa kan gado
Umma kuwa da tabi ta da kallo baki sake tayi ƙwafa tana faɗin “wawiya kawai wacce batasan me yake mata ciwo ba”.
Lumshe idanun ta Zainab tayi wasu hawaye masu zafi suka sauko mata a kunci
Ta rasa meyasaka Umman ta take magana akan Nura, meyasa Ummanta take son auren ta da Nura, taƙi tagane cewa ita baza ta iya auren sa ba, baza ta taɓa auren saurayin da Halwa take mutuwar son sa ba koda kuwa ita tana son shi”.
Hannu tasaka tana share hawayen ta tare da yin matashi da duk ka hannayen ta
Tana jin sanda Abban ta yashigo Umma take ta rattabo masa bayani, har da faɗin “wlh Malam tun wuri ayi wa tufkan hanci idan har ba so kake yi Zainab ta tsofe agida babu mashinshini ba, ga yaro son kowa ya fito yana son ta amma ita ƙiri-ƙiri ta shafe wa idanun ta toka taƙi shi akan dalilin ta na banza dana hofi, to Ni gaskiya bazan iya zuba idanu har sai sanda tagama wannan ƙaddararren makarantan ba, kawai kace ma Nura yaturo idan yaso sai taƙarisa can agidan sa yafi”.
Murmushi Abba yayi yace “Jummai Ni wannan cece kucen da kike yi banga amfanin sa ba, tunda yarinyan nan ta nuna bata son yaron nan menene na son sai ta aure shi? Duk a ƴaƴana babu wacce nayi mata auren dole bare kuma kan Autana, kibari idan har sun dai-dai ta kansu falillahil hamdu amma Ni bazan mata auren dole ba”.
Shiru Umma tayi tana gyaɗa kanta cike da takaici, ba wai don tarasa abun faɗa bane sai dai don haushin Abban da yake goya wa Zainab baya, idan da ya amince ita ana ta da tuni anyi an gama, in taje can sai su daidai ta.
Miƙe wa Abba yayi be sake cewa komi ba yaɗau buta yashiga bayi don taɗauro alwalan magariba da har an soma kira
Ita kuwa Zainab sanyi taji cikin ranta ko banza tasan Abba bazai bari ayi mata aure ba sai da yardan ta, kuma idan har itace zata amince da Nura kafin ayi musu aure to baza ta taɓa amincewa ba har abada..
*______________________*
Turo ƙofan tayi tashigo da sallama a bakin ta
Khalil dake zaune gefen gadon sa yana faman aiki acikin Lapton yaɗago yayi mata kallo ɗaya sannan yamayar da kansa yana amsa mata sallaman
Takowa tayi zuwa wajen gadon tashimfiɗa Husna akai sannan itama tazauna tana kallon sa
Shima alokacin yasake ɗago kansa yakalle ta sannan yamaida idanun sa kan Husna, tsawon sokonni biyar yana faman kallon ta kafin yace
“Wai ina Mahaifin yarinyan nan?”. Yaƙarike maganar yana aza idanun sa kan Saleema
Shiru tayi tana sad da kanta ƙasa, ba ta jin zata iya sanar masa haƙiƙanin gaskiya kuma bata san me zata ce masa ba a yanzu
Ci gaba da danna Lapton ɗin sa yayi be sake ce mata komi ba, sai can kamar mintuna biyar yasake jeho mata tambayan
“Ina Mahaifin yarinyan nan nace?”
Yanda yayi maganar ne a kausashe yasa hantan cikin ta ya yamutse, batasan sanda bakin ta yafurta “sun rabu ba”.
Cakk yatsaya da abinda yake yi yajuyo yana kallon ta
Itama ɗin shi take kallo cike da tunanin meyasaka yake son sanin Mahaifin Husnan bayan ada be taɓa tambayan ta ba?
Kau da kansa yayi yaci gaba da aikin sa
Ita kuma ajiyan zuciya tasauke sannan tagyara takwanta tana tunani aranta
“Shin meyasa nake son kawo zargi ne acikin auren mu? Meyasa zuciyata take son kawo min abinda zai hargitsa min rayuwa? Shin menene abun zargi anan?”