BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

Da maganar ƙara auren nasa da auren be fi wata biyu ba akayi komi aka gama, Amaryan sa Fahima ta tare a sabon gidan da mahaifin shi yagina masa tare da Uwar gida Zubaida
Itama dai tunda tazo ɗin bata taɓa koda ɓatan wata bane, har sanda itama tashafe shekara ɗaya curr kafin Allah yabata Ciki, zo kuga murna wajen Familyn baki ɗaya don kowa ya ƙosa yaga yaran Haris, iyayen sa babu wanda yakai su murna, haka akai ta tattalin Fahima da ɗan tayin cikin ta
Sai dai tunda tasamu cikin babu lafiya, yau suna asibiti gobe suna gida, yana watanni uku tayi ɓarin sa wanda har sai da aka dangana ga asibiti saboda yanda take zuban jini ta fita hayyacin ta gaba ɗaya, haka aka ɗauke ta ranga-ranga aka nufa Hospital da ita duk hankalin su a tashe.
______________________
A wannan lokacin itama Saleema ashe ciki ya shiga jikin ta, duk yanda kaso da dabara Allah idan yariga yaƙaddara abunsa to babu yanda zakayi, duk maganin hana ɗaukan cikin da Khalil yay ta bata amma a banza gashi ta samu shigan ciki har na wata ɗaya kamar yanda idan yakai hakan take ɓarin sa wannan ma karon hakan tayi, sai dai na wannan karon yafi na kowanne baƙin wahala
Tunda aka kai ta asibiti suke sintiri su ji me zai biyo baya amma babu likitoci babu alamun su, sai da akayi kamar mintuna 30 kafin suka fito suka nemi jini, tana buƙatar jini leda huɗu saboda ta bala’in zub da jinin ta
Haka aka ɗibi na Khalil dana Abba, sai aka siya ɗaya duk aka saka mata, su kansu Likitocin basa tunanin ma ko zata iya rayuwa a yanda take, ko numfashi bata yi sai da taimakon Oxgyen
Likitan ta yarigada yayi ma su Abba bayani dole sai an juya mata mahaifa sabida idan taci gaba da samun ciki to ƙarshe rasa ta zasu yi har abada, yanzu ma basu da tabbacin ko zata iya rayuwa.
Can ɗakin da aka kwantar da Saleema, su Ummi ne suka shiga tare da Halwa, gaba ɗayan su hawaye suke yi, yanda suka ganta tamkar matacciya hankalin su ya daɗa tashi ainun, Halwa kasa jurewa tayi tarufe bakin ta tafita dasauri cikin ɗakin, wani lungu tasamu tasoma gurzan kuka kamar zata shiɗe, kuka sosai take yi na tausayin Saleema
Haris lokacin yashigo asibitin kawo ma Matar sa abubuwan buƙata tare da abinda zasu ci, tunda a ranan kwanan ta biyu a asibitin kuma har tasamu sauƙi ana saka ran sallaman su yau ko gobe
Tunda yashigo idanun sa yasauka kan Halwa da tahaɗa kai da gwiwa tana ta sharɓan kuka, sosai yaji babu daɗi aran sa, haka kawai kuma yaji yana son ganin ko wacece yasan damuwar ta, sai kallon ta yake yi kamar yaje sai kuma yashige cikin asibitin yanufi ɗakin da aka kwantar da matar sa
Ƙanwar Maman Fahiman ce take jinyan ta, su biyu ne a ɗakin
Yana shiga suka gaisa ya’ajiye kayan da yazo dashi, tunda yazauna yarinyan da yawuce tana kuka ita ce tahana zuciyarsa sukuni, daga ƙarshe sai yamiƙe yafito don zuwa wajen ta yatambayi abinda ke damunta.
[11/24/2020, 9:03 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
_Wannan shafin naku ne masoyana na cikin group ɗin Khaleesat Haydar, na gode da nuna soyayyar ku gare Ni, Allah yabiya._❤️
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Nine*
________????Yana zuwa wajen sai dai babu ita, ya dudduba amma be ganta ba don haka yakoma cikin ɗakin da aka kwantar da Fahima, dama kawai don ta tsaya masa a rai ne but tunda yaduba be ganta ba sai be sake tuna ta ba har yabar asibitin.
____________________
Halwa tana tashi a wajen komawa ɗakin tayi, sai dai tana zuwa bakin ƙofa kunnuwan ta suka jiye mata maganganun Abba dake faɗa ma Ummi matsalan Saleema ɗin, sai kawai tazame nan ƙasa tasaki kuka me sauti, daga inda take zaune tana jin kukan Ummi itama don takasa jurewa, sai da Abba yayi ta rarrashin ta yanuna mata zata iya damun Saleema idan bata dena kukan ba tunda an ce kar suyi hayaniya da zai dame ta, hakan yasa Ummi tarage kukan ta takoma kukan zuci da hawaye
Abba ne yafito yatarda Halwan anan ƙasa tana nata sharɓan kukan, gaba ɗaya idanunta sun rine sun kumbura suntum wanda kallo ɗaya zaka yi mata katabbatar ta jima tana kuka yanda har fuskarta sai da yakumbura
“Subhanallah.. Daughter me kike yi anan? Kukan me kike yi?” Yatambaye ta yana saka hannu yaɗago ta
Halwa bata iya bashi amsa ba sai ƙara sautin kukan ta da take yi, duk da kuwa ta toshe bakin ta da Hijabin ta hakan be hana an ji fitan sautin kukan ta ba
Dafa kanta Abba yayi cike da ƙarfin halin sa yace “kiyi shiru kinji? insha Allahu ƴar uwanki zata samu sauƙi ki dena kuka haka nan”.
Ya daɗe yana rarrashinta kafin yabuɗe mata ƙofar ɗakin yabata umarnin tashiga, shi kuma yajuya yatafi.
Tana shiga taƙarisa gaban gadon inda Ummi ke zaune ta tasa Saleema agaba tana zirarar da hawaye
Gefen gadon taɗan ɗofana mazaunan ta tana kallon Saleeman itama, wasu sabbin hawayen ne suka soma sintiri a face ɗin ta sabida tausayin ta, lumshe idanuwan ta tayi tabuɗe su akan Ummi da har yanzu ko ƙifta idanu bata yi, cikin rawan murya tace
“Yanzu shikenan Ummi.. baza ta haihu ba? Meyasa za’a juya mata mahaifa? Meyasa baza’a nema mata magani ba? Don Allah.. kar ayi.. gaggawan wannan..aikin”. Taƙarike maganar nata cikin tsananin rawan baki da jan numfashi
Itama Ummi numfashin taja cike da sanyin murya da idan kaji zaka san tana cikin matuƙar damuwa tace “Ni kaina bansan wani irin ciwo ne wannan dake damun ta ba, sai dai sun tabbatar mana akwai wasu tsirrai a cikin mahaifan ta da baza su taɓa bari ta raini ciki ba, sannan kuma mahaifan ta babu ƙarfi ko anyi mata aiki ba lallai ne asamu nasara ba”.
Halwa tace “Ummi idan har za’a iya dashen cikin ajikina Ni zan iya rainon mata, zan haifa mata idan har zata ga ɗan ta a duniya, a shirye nake in sadaukar da komi nawa don samun farin cikin ta”.
Ummi kallon Halwa take yi kamar bata gane me take nufi ba
Sai Halwan tasake cewa “Ummi ki duba magana ta, idan har Saleema tasan da cewa an juya mata mahaifa hakan na nufin baza ta ƙara haihuwa ba to zata shiga matsanancin damuwa, kuma kinsan tana da ciwon zuciya idan hakan yayi tasiri zamu iya rasa ta, tunda ina da hanyan taimakon ta zan rainan mata cikin in haifa mata sai in bata yaron ta”.
“Halwa idan har na amince za’a yi hakan Mahaifin ta da Mijin ta ba lallai su yarda ba, bansan me zan faɗa musu ba”.
Daga maganar Ummin sai suka yi shiru gaba ɗayan su suna tunani
A lokacin ne Mom suka zo ita dasu Dad har da Khalil dasu Sameer, gaigaisa wa akayi tare da tambayan me jiki?
itama Halwa tagaishe su suka amsa cikin farin ciki, daga haka bata ƙara cewa komi ba tana jin su suna maganan su, daga baya su Dad suka fita ɗakin yarage daga Mom sai Ummi sai ita Halwan, har sai da likita yazo kafin suka fito waje