BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

Sai dare ita Mom tatafi gida lokacin Khalil ya dawo sai yatafi da ita

Ita kuma Halwa sai da Larai takawo musu abinci sannan suka koma tare

A ranan Ummi ta kwana ne da maganganun Halwa a ranta, sosai tahau tunanin neman mafita, daga ƙarshe kuma tayanke shawaran zata soma tuntuɓan mijin Saleema da maganar idan ya amince tasan sauran babu matsala

Da sassafe Khalil ɗin shi yasoma zuwa, Ummi batayi ƙauron baki ba tafaɗa masa komi da kuma taimakon da Halwa tace zata yi ma ƴar su

Khalil shiru yayi kawai yana sauraron Ummi har sanda tagama maganar ta, lokacin hawaye kawai take yi

Sai tausayin ta duk yakama sa, shi kansa zai so hakan sabida tsananin tausayin Saleema dake ransa, yasan da cewa idan har taji komi zata shiga wani hali sosai, ba abu ne me sauƙi ba ace baza ka taɓa haihuwa ba bare kuma fa waɗanda suke son ƴaƴan, yana matuƙar tausayinta ta yanda Allah yajarabce ta da cututtuka kala-kala, gwara shi namiji ne yana da damar da zai iya ƙara aure yahaihu da wata matar, idan har hakan shine maslaha to ya yarda zai taimaka mata, idan tasamu ɗanta ko guda ɗaya ne hakan zai sanyaya mata ranta, sannan ma ba wai wata daban ce zata rainan masa cikin ba Masoyiyarsa wacce yake matuƙar ƙauna aransa ne zata raini cikin, ko babu komi zai yi farin ciki da hakan

Don haka koda yanuna ma Ummi ya amince tayi farin ciki sosai, su biyun suka nufi office ɗin Doctor sai suka bar Halwa don alokacin tarigada tazo

Sun jima suna tattaunawa, duk da shi doctor ɗin ya nuna musu kuskuren yin hakan tunda musulunci Bata yarda da hakan ba, amma kuma duk kansu sun rigada da sun san hakan mafita kawai suke nema, ba don komi ba sai dan taimakon Saleema, sun manta da cewa haka ƙaddaran ta yake, sai dai sun san idan da lafiyan ta lau ba ta ɗauke da ciwon zuciya tabbas haka nan zata ɗau ƙaddaran ta

Kasancewar akwai kayan aikin a asibitin don haka anan suka shirya yin aikin

Doctor shi da kansa yayi ma Abba bayani kamar yanda suka shirya, kuma Ummi bata son Abba yasan da zancen, don haka Doctor yayi masa bayani akan baza su juyar mata da mahaifa ba zasu soma ɗaura ta a magani da suke sa ran za’a iya dacewa

A zahiri kuma sun shirya za’a juya ma Saleeman mahaifa batare da kowa ya sani ba sai su kaɗai ɗin, ko da nan gaba Halwa ta haifa mata yaron kowa zai ɗauka Saleeman ce tahaifa tunda sun san dama ba’a juya mata mahaifa ba, ita kuma Halwa zata koma gidan Khalil da zama ta raini cikin a sirri har tahaifa.

___________________________

Kwanan Saleema biyar kafin tafarfaɗo, tunda tafarka take kuka Ummi tayi rarrashin duniya taƙi yin shiru, duk hankalin Ummi ɗin ya tashi kar yazo wani abun yafaru da ita

A lokacin Ummi ita kaɗai ce a ɗakin

Sai doctor da yashigo yanzu yaganta tana kuka, yasoma tambayan Ummi abinda yafaru

Cikin tsananin tashin hankali Ummu tace “wlh doctor bansan meke faruwa da ita ba, yanzu tatashi kuma tunda tatashi take kuka, nayi-nayi tayi shiru taƙi yi, yanzu nake shirin kiran ka sai ga ka ka iso”.

Kallon Saleema dake kwance tana sharɓan kuka yayi, cikin tausayawa yace “Saleema meke faruwa ne me yasaka ki kuka? Ko wani wajen na miki ciwo ne?”

Girgiza kanta tayi tana kallon su da rinannun idanuwan ta wanda suka faɗa suka yi baƙi, ita kanta gaba ɗaya ta zurma ta faɗa sosai gunun tausayi

“To menene faɗa min?” Likitan yasake tambayar ta

Cikin kukan take cewa “Doctor.. cikinaa..”

Sai tasoma numfarfashi kamar ranta zai fita

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un..” Ummi tafaɗa cikin ruɗewa tana ruƙo ta tare da fashewa da kuka

Shima Doctor ɗin ya ruɗe Nan da nan yamatso da zumman taimaka mata

Sai tasake cewa “doctor.. cikina.. ya zube ko?”

Duk kan su shiru suka yi don basu san amsar da zasu bata ba, ita Ummi kuka ya hana ta magana

Sai Doctor ne yayi ƙarfin halin kwantar mata da hankali

“Don Allah Saleema ki kwantar da hankalin ki, yanzu insha Allahu mun samo matsalar ki komi zai wuce kinji? Kiyi haƙuri kar ki saka ma ranki damuwa tunda yanzu lafiyan ki muke so, Ummin ki zata yi miki bayani kinji kiyi shiru”.

Ummi ma cikin son ƙara kwantar mata da hankali tace “my Dear ki dena kukan yanzu komi yazo ƙarshe kinji?”.

Sai tasaka hannu tana share mata hawayen

Doctor yace “Sister yanzu abata ko ruwan tea ne tunda jikin ta babu ƙarfi, idan nadawo zan yi mata allura sai in saka mata Drip, ki kula da ita sosai Please”.

Gyaɗa kanta Ummi tayi sannan tace “to doctor”.

Sai da yasake duba ta tare da yin mata tambayoyi kafin yafice.

Ummi taimaka mata tayi tatashi zaune, tagyara mata pilow abayan ta yanda zata ji daɗi sannan takoma tazauna tana kallon ta, cikin tausayin ta tace “Daughter don Allah ki dena kukan haka nan, kinsan bazan ji daɗi ba idan naga hankalin ki ba’a kwance ba”.

Share hawayen ta Saleema tayi wasu na sake fitowa, cikin muryan mara lafiya sosai tace “Ummi shikenan idan nasami ciki zai dinga zube wa bazan haihu ba? Kullum haka zan riƙa shan wahala idan na samu ciki?”

Hannun ta Ummi taruƙo cikin lallami tace “kar ki damu komi ya wuce zaki haifi yaron ki kema?..”

“Taya Ummi bayan ina da matsala?” Takatse Ummin da faɗin hakan idanun ta na zirarar da hawaye

Ummi har ta buɗe baki zata yi magana Halwa taturo ƙofan tashigo, daga school tabiyo ta nan tunda dama haka take yi

Ganin Saleema zaune ya matuƙar faranta ranta, nan da nan tawashe bakin ta tanufo bakin gadon tana faɗin

“Sister kin tashi?”

Sai kuma tasauya fuska tana kallon Ummi tace “Ummi me yafaru ne meyasaka take yin kuka?”

Numfashi Ummi taja kafin tace “tunda tatashi take yin kuka sabida cikin ta ya zube”.

Kallon ta Halwa tayi kafin tariƙe ɗaya hannun ta da Ummi bata riƙe ba tace “Sister meyasa zaki riƙa saka ma kanki damuwa bayan kinsan kina fama da ciwo? Don Allah ki dena in ba so kike mu ma mushiga wani hali ba”.

Cikin rawan baki Saleeman tabuɗe baki zata yi magana sai kuma takasa sabida kukan da yataho mata, saurin duƙar da kanta tayi tana sakin kukan ahankali

Itama Halwa sai tasoma kuka tana sake riƙe hannun ta sosai

Ummi tace “kiyi shiru don Allah Saleema Allah ne yabaki cikin nan kuma shine ya’amsa ko baki yarda da ƙaddara bane?”

Shiru Saleeman tayi sai dai bata yi magana ba tana sauraron Ummi ɗin da taci gaba da maganar ta, cakk tahaɗiye sauran kukan nata tana ɗago kanta tana kallon Ummin, sai kuma takalli Halwa da tasakar mata murmushi tana gyaɗa mata kai alaman tabbaci da abinda Ummi ke faɗi

Shafa fuskar ta Ummi tayi tana murmushi tace “Halwa ta amince zata rainan miki cikin ki har tahaifa miki, sai dai ban sanar ma Abban ki ba don kar yahana, amma kuma da yardan Khalil muka yanke hukunci, yanzu kar ki bari Abban ki yaji ko kuma wani kinji? Mun yanke hukunci Halwa zata yi rainon cikin a sirri ne”.

Saleema kallon Halwa kawai take yi cike da farin ciki, tabbas bata san da bakin da zata yi ma Halwa godiya ba, kawai sai tafashe da kukan farin ciki tana faɗin

“Wlh bansan da bakin da zan miki godiya ba ƴar uwata, amma na san cewa…”

“Shiiiiiiii… Yi shiru my Sister”.

Halwa tafaɗa tana rufe mata baki, sannan taci gaba da faɗin

“Duk abinda zan miki Sister babu godiya a tsakanin mu, ke ce kika taimaki rayuwata a lokacin da narasa tudun dafawa, inda baki shigo rayuwata ba a yanzu bansan wani hali zan shiga ba, duk abinda zan yi wlh sister bazan taɓa biyan ki ba don haka kar ki soma kiyi min godiya kinji?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button