BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

Taƙarike maganar tana cire hannun ta kan bakin Saleeman, idanun ta cike da hawaye
Murmushi Saleema tasaki hawaye na zirara a kuncin ta
Hannu tasaka tashare mata lokacin itama nata sun zubo
Ummi kuwa kallon su take yi cike da farin ciki, ta gode Allah da yahaɗa su da Halwa, idan ba ita ba babu wanda zai iya taimaka ma ƴar su, tabbas ta cancanci Godiya me yawa
Murmushi tayi tace “yanzu to bari in haɗa miki tea ɗin kisha kar doctor yadawo tunda hankalin ki ya kwanta”.
Kallon Ummin suka yi gaba ɗaya suna murmushi
Vowel tasoma ɗauko wa tare da ruwa tace “ki wanke bakin ki don kiji daɗin bakin, bari in taimaka miki”.
Amsar Vowel ɗin Halwa tayi tace “kawo Ummi bari in taimaka mata”.
Da taimakon Halwa Saleema tawanke bakin ta don ko kaɗan bata da ƙarfi ajikin ta, bayan ta gama tasha tea ɗin kaɗan
Doctor da yadawo yaɗaura mata Drip sannan yabata magani, babu jimawa tasoma barci tunda har da maganin barci aka bata don samun hutun ta
Sanda su Abba suka zo suka ji ta farka jikin kuma alhmadulillah sun ji daɗi sosai, tunda basu yi zaton hakan ba, amma Alhmadulillah kowa yake faɗi.
[11/26/2020, 6:00 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Ten*
________???? Satin Saleema biyu acikin asibitin kafin abata sallama tunda ta samu sauƙi sosai
A ranan da aka sallame ta Ummi tasamu Abba da maganar komawar Halwa gidan Saleema ɗin a matsayin zata zauna da ita
Abba be kawo komi akai ba ya’amince tunda shi da kansa Khalil ɗin yabuƙaci hakan kamar yanda Ummi tafaɗa masa
A ranan Halwa tahaɗa kayan ta da komi drever yakai ta gidan, ɗakin da Lubna tazauna ada nan aka gyara mata komi sai da Khalil yasauya mata na ciki
Wannan ranan kuma tazo ma Khalil cikin wani irin farin ciki, sosai yatsinci kansa a matuƙar murna kasancewar sa gida ɗaya da abar kaunar sa.
Tun daga ranan Halwa take musu komi girki, gyaran gida da duk abinda yadace, har alokacin kuma gaisuwa kaɗai ke haɗa su
Ahaka har kwanaki suka shuɗe inda Saleema tasake samun sauƙi sosai, a lokacin ne kuma suka shirya gaba ɗaya suka tafi asibiti inda za’a yi aikin saka ma Halwa ƙwayoyin haihuwar su don tahaifa musu ɗa, Ma’ana Invibrosfertilization a turance
A can suka haɗu da Ummi tana jiran su, babu ɓata lokaci Likita yahaɗa duk abinda Yakamata sannan aka shigar dasu ɗakin Theater aka yi, a lokacin ne kuma aka juyar ma Saleema da mahaifa batare da ta sani ba, tunda ita a tunanin ta duk aikin da za’a yi ne wajen saka ma Halwa ƙwan haihuwar ta
Har yanzu basu faɗa mata za’a juyar mata da mahaifa ba sai zuwa nan gaba idan hankalin ta ya kwanta sanda Halwa tahaifa mata yaron ta, hakan zai sa baza ta wani tada hankalin ta ba.
****** ****** ******* ***** *******
*TWO MONTHS AGO*
A cikin wannan watannin sai ga Halwa ta soma Laulayin ciki, koda suka je asibiti an tabbatar musu tana ɗauke da cikin dagaske har na tsawon watanni biyu
Zo kuga murna wajen Saleema da Khalil, sosai suke tsananin murna, ita dai Halwa sai dai tataya su da murmushi
Tun daga ranan kuma sai yazamana babu abinda Halwa take yi sai zaman hutu idan taje makaranta ta dawo, Khalil da kanshi wani lokacin yake kai ta school idan tana da lectures ɗin safe, sai drever kuma yaɗauko ta
Sun saba sosai dashi tunda yanzu suna zaune gida ɗaya, har hira suna yi tare
Saleema bata barin ta tayi komi duk ita take yi yanzu duk da Halwan tana taimaka mata tunda cikin ba me laulayi sosai bane kamar yanda tayi na Husna me wahala
Ummi ita da kanta tasanar da Abba Saleema na da ciki, sosai yayi farin ciki musamman jin cikin ya wuce wata ɗaya hakan na nufin an samu nasara kenan.
*****
Yau ma tana da lectures ƙarfe 11:00am.
Bayan ta shirya cikin blue and white colour ɗin atamfa ɗinkin riga da skert, tayi Rolling Farin gyale akanta, sai tasaka flet shoes shima fari da kalan baƙi a ƙasan, ta ɗau jakar ta kenan tana ƙoƙarin ratayawa
Saleema tashigo ɗakin riƙe da Plate a hannun ta, tana sanye cikin atamfa ja da kalan ruwan Powder ajiki, ɗinkin riga da zani sai taɗaura zanin ta gefe, ɗankwalin kuma taɗaura sa normal
Zuwa tayi kusa da ita tajanye jakan tana faɗin “ina zaki je baki ci abinci ba?”
Murmushi Halwa tayi tana kallon ta tace “wlh sister bana jin yunwa ne”.
Hannun ta tajanyo suka zauna gefen gado tace “ai baki isa ba babu inda zaki je sai kinci wannan, shiyasa ma nashiga na dafa miki taliyan nan me ɗan romo-romo sabida yayi miki daɗi, kin gani ma har da yaji nazuba miki da yawa zai miki daɗi ai”.
Sai kawai Halwa tasoma dariya
Itama kuma Saleeman dariyan tasoma duk da batasan me take ma dariyan ba, kafin taɗibo taliyan a cokali takai bakin ta tana faɗin
“Haaa bakin ki”.
Hakan yaƙara saka Halwa tsananin dariya har tana tuntsura wa kan gadon
Wannan karon baki Saleema tasaki tana kallon ta
Kusan shuɗewar one minute kafin tace “wai menene kike ma dariya haka?”
Tashi zaune Halwa tayi tana ci gaba da dariyan nata kafin tace “Allah dariya kike bani Sister kin maishe Ni tamkar yarinya”.
Murmusawa Saleema tayi tace “to ba dole ba kina ɗauke da cikin babynmu, nifa wlh ma kewar Husna nake yi dole zan saka Yaya Barrister yaje yaroƙi Ummi tabani ita”.
“Me kike ci na baka na zuba tunda ga sabon baby zai fito? kibar wancan me ƙwallon kan”.
Hararan ta Saleema tayi tace “Ummina ce me ƙwallon kai ko?”
Sai Halwa tayi saurin girgiza kanta tana fiddo ido waje tace “wlh suɓutar baki ne”.
Sai da Saleema ta dara sabida yanda tayi maganar a tsorace
“To shikenan naji amma kar ki sake, yanzu kici abincin kar kiyi latti”.
Amsan Plate ɗin tayi tana faɗin “wlh bana jin yunwa my sister don ke kawai zan ci”.
“To na gode yi maza kici sai kisha ruwa”. Saleeman tafaɗa tana tsare ta da idanu
Murmushi Halwa tayi lokacin da takai spoon ɗin bakin ta, ahankali tay taci ba don ranta na so ba don dai kawai ta faranta ran Saleeman, suna yi suna hira har tagama sannan Saleema taɗauko mata ruwa taba ta tasha suka fito
Har wajen mota sai da taraka ta taga fitan su kafin tadawo cikin gidan.
****** ****** ****** *****
Ƙarfe 01:45pm. Khalil yabar office yanufi gidan su, yau a waje yayi parcking ɗin motan nasa tunda baya son yadaɗe, kwana biyu rabon sa da zuwa gidan shiyasa yau yayanke shawaran zuwa daga nan kuma yasanar ma Mom ƙaruwar da suka samu Saleema na da juna biyu
Koda yayi sallama cikin parlour’n Mom ɗin ce kaɗai zaune, ta ɗan kishingiɗa kanta saman kujera tana ta faman kallo
Sallaman sa shi yatada ita tana amsa mishi kafin tace “my son idanun ka kenan ko?”
Shafa kansa yayi yana nufo ta
Shi kansa yasan be kyauta ba, musamman yanzu da ba samun lokaci yake yi ba ko waya ba suyi a kwanakin