BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

Zama yayi yana kallon ta da tsadadden murmushin sa yace “I’m very sorry Mom kinsan aiki yayi min yawa shiyasa bana samun zuwa wlh, ina yini?”
“Lafiya lau my son ya matar taka?” Mom ɗin ta’amsa masa cikin fara’a
“Lafiya lau Mom tana gaishe ki ma”.
“Ina amsa wa, yanzu Sameer yafita baku haɗu ba?”
Girgiza kansa yayi yana kallon ta, kafin yace “Mom babu lafiya ne?”
“To lafiyan dai za’a ce, Aamir ne yake fama da zazzaɓi, duk da dai Baban nasa ma yace min ya samu sauƙi”.
Cike da damuwa Khalil yace “ayya bansani ba insha Allahu zan je gaishe shi yau ɗin nan”.
“To Allah yabaka iko”.
Sallaman Nazeefa yasaka suka kalli ƙofan suna amsa mata
“Nazeefa an dawo?” Cewar Mom tana kallon ta da murmushi
Itama Nazeefan murmushin take yi cike da farin cikin ganin Khalil tana tahowa ta’amsa mata da “Eh Mom Barka da gida”.
Sannan takalli Khalil ɗin da a yanzu yafito da waya cikin aljihu tace “Yaya ina wuni”.
Sai da yaɗago yakalle ta kafin yace “lafiya ya school?”
“Alhmadulillah Yaya”.
Je ki cire kayan makarantan sai ki zo ki zuba ma Yayan naki abinci, yau babu Atine agidan”.
Kafin takai ga amsawa Khalil yayi saurin faɗin “a’a Mom bana jin zan iya cin komi yanzu”.
Mom ɗin bata tsawaita bincike ba tace “to shikenan”.
Ita kuma Nazeefa sai tayi hanyan ɗakin ta Mom tabi ta da kallo, kafin tajuyo ga Khalil dake latsa waya tace
“Wai ni kam Auta dama akwai maganar da nake so muyi da kai”.
Be amsa mata ba illa ɗago kai da yayi yana bata attention ɗin sa
Nazeefa da har ta shiga ɗaki tana ƙoƙarin rufe ƙofa tajiyo muryan Mom tana faɗin sunan ta, hakan yasa tadakata don jin me zata ce
“Ni kuwa ina maka sha’awar Nazeefa”.
Kallon rashin fahimta Khalil ɗin yayi mata, kafin kuma yace “Mom sha’awa kuma? Kamar ya?”
Murmusawa tayi tace “Ni naga tunda matar ka bata da lafiya kuma kaima kana buƙatan ƴaƴa, ba’a son ranan dacewa ba bare ta haifa maka, me zai hana kaƙara aure? Ga ƙanwar ka Nazeefa tunda ba wani matsala ce da ita ba sai ka aure ta, in yaso sai wani hidindimun dake kan Saleeman su ragu, kaima zaka fi samun nutsuwa ko?”
Tunda tafara maganar yake yamutsa fuska, maganar tazo masa a bazata sosai, cikin rashin jindadin abinda tafaɗa yace
“Momyyy why zaki yi irin wannan tunanin? Ni fa na ɗauki Nazeefa tamkar ƙanwata ce wacce muka fito ciki ɗaya da ita, ban taɓa kallon ta a matsayin da kike magana ba, don Allah ki dena wannan maganar ma kar wani yaji”.
Mom dariya tayi tace “sai kace wani abun kunya? Tunda baka so shikenan, dama sai da nayi ma Daddyn ku magana yace “shima babu ruwan sa idan ka amince to” tunda yanzu ka nuna baka so ai shikenan babu dole a zancen”.
“Kuma Mom komi yanzu ya zama normal tunda yanzu tana ɗauke da ciki har na tsawon Two month”. Yayi maganar yana turo baki
Da fara’an ta tace “haba dai? An dace kenan?”
“Insha Allahu Mom haka muke saka rai tun da gashi ya wuce wata ɗaya”.
“Masha Allah, Allah Sarki wlh yarinyan nan tana bani tausayi matuƙa Allah yaraba lafiya, yanzu tana gidan su ne ko kuwa don kasan dai baza ta zauna ita kaɗai ba?”
Khalil yace “A’a bata koma gida ba, sai dai Halwa tana zaune da ita”.
“To masha Allah haka ake so, har yanzu ita babu labarin komawar ta gidan mijinta ne?”
Khalil ɗan waro ido yayi don be fahimci maganar da take yi ba
Hakan yasa Mom ɗin tasake cewa “ina nufin ita Halwan tunda naji ance sun rabu da mijin ne”.
Ɓata fuska Khalil yayi yana shafa sajen sa yace “Ni bansani ba”.
Yanda yayi maganar ne sai da Mom tasake duban sa, sosai taga ɓacin rai a fuskarsa har a maganan da yayi sai da yanuna
“Mom zan tafi”. Yafaɗa yana miƙewa tsaye
Itama miƙewar tayi tana faɗin “yauwa bari in baka saƙo sai kabata, ina zuwa”.
Wuce wa ɗaki tayi taɗauko tabashi sannan suka sake sallama yafice.
****
Kuka Nazeefa tafashe dashi tana zame wa ƙasa, da rarrafe tanufi cikin ɗakin har zuwa bakin gado tahaɗa kai da gwiwa tasoma rera kuka ahankali, kukan rashin madafa a wannan halin da take ciki, shikenan tasan babu ita babu auren KHALIL tunda be taɓa mata kallon yanda take masa ba, infact ma ya ɗauke ta tamkar wacce suka fito ciki ɗaya ne, hakan yasa tasake fashe wa da kuka tuna abinda yace, sai dai yanzu tasan dole tararrashi zuciyarta tunda baza ta taɓa samun sa ba.
Share this
[ad_2]