BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

Kwanciyar ta tagyara tana kallon sa, ahankali kuma tafurta “Allah na tuba Allah ka cire min zargi araina”.
Aikin yake yi amma maganar Saleema ke kai kawo cikin ransa, duk da yaji sanyi ta wani gefe nasa amma kuma yasan cewa mafarkin sa bazai taɓa zama gaske ba
A haƙiƙanin gaskiya zuciyar sa ta kamu da ƙaunar Halwa tun ranan farko da yaganta, amma taya zai iya mallakan ta bayan ita ɗin ƴar uwa ce ga matar sa?
Har Saleema tayi barci yana nan zaune yana latsa Lapton ɗin sa duk da kuwa tunani ne cinkushe aran sa wanda yahana sa jindaɗin aikin
Daga ƙarshe ma tashi yayi yashige toilet yaɗauro alwala, fitowa yayi yazauna a bakin gadon yana kallon Saleema dake maƙale da Husna, sosai yake mamakin yanda take ƙaunar yarinyan
Ya jima a zaune awajen yana kallon su, amma azahiri tunani ne aransa wanda har yasoma haddasa masa ciwon kai
Kwanciya yayi yaci gaba da tunanin, yafi mintuna 20 kafin yamiƙe yatashi yasoma jero nafilfilu ganin hakan shine kaɗai mafita a gare shi, domin ko kaɗan ayau ɗin baya jin barci zai iya ɗaukar sa.
.
*Plz Share and Vote*
_More Comments more typing._
[11/13/2020, 11:10 AM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Three*
________????Washe gari ƙarfe 07:30am. *BRR. IBRAHIM KHALIL* yagama Shirin sa na zuwa office
Yau yayi shiga na Red colour suit, sai na cikin kuma whiter ne, necktie ɗin sa da Belt ɗin wandon sa baƙi ne, yayi kyau sosai sai tashin ƙamshi yake yi, sosai kwarjinin sa da cikan halittansa suka sake fitowa ainun
Be tsaya yayi breakfast ba duk da kuwa Saleema tuni tatashi tayi masa, haka yafice sabida yana sauri
Aiki sosai yake dashi a office, gashi kuma zasu je wani waje shi da Brr. Tahir
Sai wajen 12:00pm. Yagama sannan suka tafi.
Ƙarfe :2:30pm. Suka gama yanufi gidan su
Yana yin horn me gadi yazo yabuɗe masa, shiga yayi da motar ciki yayi parcking yafito yarufe murfin motan yashiga gidan
Mom na zaune a parlour tana cin Fruits tana kallon tashan African t.v ana wa’azi tajiyo sallaman sa
Fara’a tasaki tana amsa masa sallaman kafin taɗau Remote tarage t.v n
Ahankali yatako cike da gajiya yazauna gefen ta sannan yagaishe ta
Murmushi tayi tana shafa kansa ta’amsa masa tana tambayan Saleema
Sai da yayi releasing akan kujeran kafin yabata amsa da “lafiyan ta ƙalau Mom”.
“Masha Allah haka ake so”.
Sai da tagutsira ???? Bananan hannun ta kafin takalle sa tace “ko asawo maka abinci?”.
Gyaɗa kansa kawai yayi yana jan numfashi
Mom har ta buɗe baki da ninyan kiran ƴar aikin ta sai ga Nazeefa ta fito daga ɗakin ta riƙe da plate a hannun ta
“Yauwa Nazeefa sawo ma Yayan ki abinci”.
Nazeefa da idanun ta ke kan Khalil ta’amsa mata da “Toh”. Sannan tagaishe da Khalil ɗin
Idanun sa shima akanta ya’amsa mata
Kichen ɗin tanufa zuciyarta cike da ƙaunar sa, sosai yau ɗin yasake mata kyau fiye da ko yaushe, domin ta ɗan jima rabon da tagan shi, ko da yazo gidan ita tana makaranta a lokacin
Fitowa tayi riƙe da plate da spoon aciki, taƙariso ta’ajiye masa kan Centre table bayan ta ɗan matso masa dashi, zuwa tayi tazauna can kujeran dake Facing nashi taduƙar da kanta tana satar kallon sa
Shi kuwa abincin sa yaɗauka yana ci yana sauraron hiran Mom da take yi masa akan Yayan nasa Sameer
Ko kaɗan bata gajiya da kallon sa, da ace zata kwana tana kallon sa to baza ta taɓa gajiya ba, a kullum ƙaunar sa sake wanzuwa yake yi a zuciyar ta, ta rasa yanda zatayi tacire sa aranta, bata da damuwa a ko yaushe sai nasa, burin ta kullum tasami hanyar da zata mallake sa duk da tana ganin abu ne me wahala ta same sa, amma baza ta cire rai ba da ikon Allah sai Allah ya mallaka mata shi, koda kuwa zata kasance matar sa ta huɗu ne to zata zauna dashi in dai zai aure ta..
“Nazeefa lafiyan ki ƙalau kuwa tunanin me kike yi?”
Maganar Mom yadawo da ita hayyacin ta, dasauri taɗago kanta tana kallon su
Mom ce kaɗai idanun ta ke kanta, yayinda shi kuma yake cin abincin sa hankalin sa kwance
Cikin daburce wa tace “Mom ban ji bane”.
“Yayan ki ne ke magana”.
Nazeefa sauke idanun ta kansa tayi tace “Yaya me kace?”
Sai alokacin yaɗago fararen idanun sa yana kallon ta, hararan ta yayi yace “ban sani ba”.
Bata san sanda tayi murmushi ba sabida yanda yayi maganar har hararan sai kace wani mace
Mom ma sai da tamurmusa don itama taga sanda yayi hararan, cikin murmushin tace “ayi mata afuwa mana Auta wannan harara haka?”.
Ajiye abincin yayi yana kallon Nazeefan da tasauke nata idanun ƙasa yace “meyasa baki taɓa zuwa gidana ba?”
Hannun ta tamatse waje ɗaya cike da fargaba taɗago kanta tana kallon sa tace “Yaya makaranta ne yahana Ni zuwa”.
Hararan yasake aika mata dashi cikin ɗaure fuska yace “makarantan ne zai hana ki zuwa gidana?”
Mom tace “ai nima nayi godo da ita taje amma taƙi zuwa wlh, Ni bansan meke damun Nazeefa ba yanzu, ko ranan Saturday ɗin nan sai da nasake yin mata magana”.
Nazeefa sad da kanta ƙasa tayi kamar zatayi kuka, ko kaɗan bata son zuwa gidan Yayan nata ba don komi ba sai don kishi, baza ta iya juran ganin sa da wata ba idan har ba ita ba
“Je ki shirya kizo mu tafi, ki haɗo da kayan makarantan ki don kwana zakiyi, idan kin wuce makaranta kya dawo nan”.
Tashi tayi batare da tace uffan ba tanufi ɗakin ta, tana shiga tacire riga da skert ɗin jikin ta tasaka dogowar riga baƙi da yasha stone masu ƙyalƙyali, sosai take son dogoyen riguna shiyasa ma Mom Ko da ɗinki zata bada ayi mata, dogayen riguna take saka wa ayi mata, tunda ko anyi mata sauran ɗinkunan bata saka wa sai taga dama
Ɗan ƙaramin jaka taɗauka tasaka kayan makarantan ta sannan taɗau school bag ɗin ta tafito
Ko kaɗan bata murna da zuwa gidan Yayan nata, sai dai sauƙin ta ɗaya zata riƙa ganin sa yanzu
Tana fitowa Khalil miƙe wa yayi sukai sallama da Mom sannan yayi gaba Nazeefa tabiyo bayan sa bayan itama tayi ma Mom ɗin sallaman.
*_____________________*
A mota babu me magana cikin su, tun sanda yatambaye ta karatun ta be sake magana ba, hankalin sa na ga titi har suka iso gidan
Bayan yayi horn me gadi yabuɗe masa yasaka motan ciki, yana parcking suka fito atare, yana gaba tana bin sa a baya sai bin gidan take yi da kallo, komi an sauya ba kamar sanda tataɓa zuwa ba
Suna shiga babu kowa sai Husna dake wasa a ƙasa
Wajen ta Khalil yawuce yaɗauke ta yana saɓa ta sama yana mata wasa
Sai Nazeefa tasaki baki kawai tana kallon su
Sai shine da yajuyo yaganta har yanzu a tsaye yace “tsayuwar me kike yi kuma?”
Sai alokacin tadawo duniyar tunanin ta tasamu wuri tazauna
Shi kuma yawuce ɗakin Saleema da Husna a saɓe a wuyan sa
Yana tura ƙofan da sallama yahange ta zaune kan stool tana shafa Lipstick a bakin ta, tayi shiga cikin riga da skert na ɗan kanti, farar riga me gajeren hannu sai jan skert me ɗan faɗi tare da tsagi ta baya, kayan sun yi mata kyau gashi kuma sun ɗauki white skin ɗin ta, kanta da ɗan siririn ɗan kwali da taɗaura be gama rufe mata tsakiyar kai ba