BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

Amsa sallaman tayi tana juyowa takalle su
Sosai tayi masa kyau yatako wajen yana kallon ta batare da yace komi ba
Sannu da zuwa tayi masa tana murmusawa
Ya’amsa mata still yana kallon ta kafin yace “kin yi kyau matata”.
Rufe fuskarta da tafin hannayen ta tayi tana ɗan sakin dariya me sauti kafin tace “Nagode Mijina”.
Shima sai yayi dariyan yana sauko Husna yariƙe ta sosai a hannun sa sannan yace “ga ƙanwata nan nazo da ita zata kwana gobe zata tafi”.
Miƙe wa tayi ta’amsa mishi da “Toh”. Tanufi ƙofa, shima yabi bayan ta
Suna fitowa idanun ta yahaɗe dana Nazeefa, har yanzu dai bata san wacece ita agare su ba duk da kuwa tasan ba ƙanwar Khalil ɗin bane, amma ta danganta hakan da ƙila ƴar uwansa ce
Zuwa tayi da fara’an ta tazauna
Ita kuma Nazeefa ganin Khalil shima yazo ya zauna ne tasaki fuskarta itama sannan tagaishe ta
Saleema ta’amsa mata tana murmusawa sannan tatambaye ta Mom? Ita kuma tabata amsa “tana nan lafiya tace agaishe ki”.
“Yaya ko in kawo maka abincin nan ne?” Saleema tayi maganar tana kallon Khalil da yatasa Husna gaba yana faman mata wasa
Girgiza mata kai yayi batare da ya kalle ta ba yace “no sai nayi wanka zuwa anjima zanci”.
Sannan yamiƙe tare da Husnan yanufi ɗakin sa
“Ƙanwata taso muje kici abinci”. Saleema tafaɗa tana kallon Nazeefa da tabi bayan Khalil da kallo
Murmushi taƙirƙiro tana kallon Saleeman tace “a’a Aunty Alhmadulillah sai da naci abinci kafin na taho”.
“Haba dai ko ɗan ruwa ne ai kya sha, bari in kawo miki”.
Tashi tayi tanufi wajen Fridge
Nazeefa taraka ta da kallo, sosai take mamakin yarinyan da tagani don bata da masaniyar zaman ta agidan, har Mom ma itama sai daga baya tasani, sai kuma tataɓe baki aranta tace “to Ni ina ruwana”.
Saleeman tadawo riƙe da
Drinks da taɗauro saman plate ta’ajiye Mata a gaban ta kan Centre table sannan takoma tazauna tana faɗin “bismillah”.
Babu musu Nazeefa taɗauka Robbern Fanta tabuɗe tazuba cikin glass cup ɗin da tahaɗo mata dashi, tana sha suna kallo batare da ɗayan su ya sake magana ba tunda babu sabo ko kaɗan a tsakanin su
Suna nan zaune har Khalil yafito, da alamun yayi wanka ne don ya sauya kayan sa cikin shiga na ƙananan kaya wanda sukai ma jikin sa kyau sosai
Duk kansu kallon sa suke yi cike da tsantsan ƙauna
Shima dai kallon su yayi sai ya’aza idanun sa kan Saleema yaɗan ɗage mata gira ɗaya yace “My dear na wuce masallaci, ga ƴar ki can tana barci”.
Murmushi Saleema tayi tace “to adawo lafiya”.
Gyaɗa kansa yayi yanufi ƙofa yafice
“Ƙanwata muje in Kai ki ɗaki”.
Maganar Saleema yakatse mata tunani, cikin son kawar da abunda yatokare mata maƙoshi tamiƙe da jakanta tabi bayan ta
Ɗakin ta takai ta sannan tafito tanufi ɗakin Khalil, anan ita tayi sallan ta kafin tadawo parlour
Alokacin shima Khalil ya dawo har ya zauna saman dainnig yana latsa wayan sa
Wajen tanufa tasoma saving ɗin sa sannan tajuya zata tafi
“Ke kinci abincin ne?”
Juyowa tayi tana kallon sa sannan tagyaɗa masa kanta tana murmusawa
Be ce komi ba yaɗau spoon ɗin yasoma cin abincin sa
Nazeefa tunda tagama Sallah tazauna nan kan sallayan taƙi tashi, sai ma zuba tagumi da tayi ta’af ka tunani
Bata sake fitowa ba har dare
Koda Saleema tashigo tayi mata maganar tafito Parlour ko zata fi jindaɗi, sai tace “a’a nan yayi mata”.
Juyawa tayi kawai tabarta takoma parlour taci gaba da kallon ta don shi tuni Khalil ya shige ɗakin sa yana faman aiki a Library ɗin sa
Daga karshe da tagaji da zaman sai tanufi kichen tayi musu girki me sauƙi, taliya tadafa da raguwar miyan ta na jiya
Sai da tagama komi taje tajera a dainning table, lokacin har an kira sallan magriba
Ɗakin Khalil ɗin tanufa tashiga ciki, alokacin ya fito daga Toilet bayan ya ɗauro alwala, kallon ta kawai yayi yafice dasauri
Ita kuma tanufi kan gadon inda Husna ke kwance tarigada ta farka tana ƙananun kukan ta, ɗaukan ta tayi tanufi ɗakin ta da ita
Shiga tayi da sallama a bakin ta, kallon Nazeefa dake sallah tayi tawuce cikin Toilet
Kayan Husna tacire tawanke mata kashin da tayi sannan tayi mata wanka tafito taɗaura ta kan gado, sai takoma taɗauro alwala tadawo tagabatar da Sallah
Nazeefa na zaune akan kujera tana faman kallon Husna dake ta mutsil-mutsil cikin towel da aka nannaɗe ta dashi tana son cire wa tasauko
Har Saleema ta’idar da sallan ta tamiƙe tasoma shirya Husnan, ta kula Nazeefa ba me son yin magana bane shiyasa itama taƙyale ta batare da ta kula ta ba, amma abinda yadace tana tambayan ta
Har tagama abinda zatayi tafito Parlour tazauna tana ma Husna wasa tana kallo
Sai bayan isha’i sannan Khalil yadawo gidan
Suna zaune kan dainning shi ya ɗaura Husna ajikin sa yana cin abinci yakalli Saleema da itama take saving nata yace
“Ina Nazeefa ne?”
“Tana ɗaki tana sallah nayi mata magana yanzu zata fito..”
Bata rufe baki ba nazeefan tafito taƙariso wajen tana gaishe da Yayan nata
Amsa wa kawai yayi yaci gaba da cin abincin sa
Itama zama tayi tayi saving kanta tasoma ci, can kuma taɗago kanta tana kallon sa yanda duk yabada hankalin sa kan Husna ko abincin ma baya ci sosai
“Yaya wai wannan yarinyan wacece?” Tayi tambayar tana ci gaba da kallon sa
Daga shi har Saleema suka ɗago kansu suna kallon ta
Sai da yakau da kansa gare ta kafin yace “Ƴata ce”.
Bata sake cewa komi ba taci gaba da cin abincin ta sai dai zuciyarta haushin amsar da yabata take ji
Ita kuwa Saleema murmushi kawai tayi tana kallon Khalil ɗin cike da ƙaunar sa, sannan taci gaba da cin abincin ta
Shi yasoma tashi yanufi ɗaki
Kamar ana tsikarar Nazeefa tana ganin ya shige itama tamiƙe tanufi parlour
Saleema dai bata ce mata komai ba illa kallo ɗaya da tayi mata taɗauke kanta, sai da tagama tattara komi takai kichen sannan tanufi ɗakin ta
Wanka tayi tasanya kayan barci sannan taɗau abubuwan da zata buƙata tare dana Husna tafito tana kallon Nazeefa dake zaune tana kallo
“Ƙanwata koda akwai abinda kike buƙata ne?”
Sai alokacin Nazeefa taganta ma, kallon ta kawai take yi cike da tsananin kishi, tasan tunda tagan ta da shiri ɗakin Khalil zata tafi
“Kenan ko hiran daren ma basuyi sai su shige ɗaki?” Tatambayi kanta tana ci gaba da kallon Saleeman cike da tsantsan haushin ta
Ita kuma Saleema ganin tayi shiru sai tabuɗe ɗakin Khalil kawai tashige abunta aranta tana jinjina wulaƙacin yarinyan, ko ba komi ai ita Matar YaYanta ne bare ma ta girme mata sosai don aƙalla zata bata shekaru uku ƙwarara
Tana ganin ta shige itama tatashi tanufi ɗakin Saleeman zuciyarta kamar zata tarwatse, har wani ɗaci-ɗaci take ji a maƙoshin ta.
Sai Khalil ne daga baya yafito yakashe t.v n yakulle ƙofan Parlourn yakoma ɗaki.
Washe gari ƙarfe 07:20am. Ya riga ya gama shirin sa har breakfast yayi sannan yafita
Lokacin itama Nazeefa tafito da shirin ta na makaranta tana rataye da school Bag ɗin ta tare da jakan da tasaka kayan da tacire, fuskarta duk babu walwala idanunta sunyi luhu-luhu kamar wacce bata samu ishashshen barci ba
Saleema dake kakkaɓe parlour’n taɗago tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta tace “Ƙanwata har kin fito?”
Itama Nazeefan murmushin tayafa ma fuskarta sannan tace “eh Aunty Ina kwana?”
“Lafiya lau kin tashi lafiya? Ya baƙunta?” Saleema tasake yin maganar da fara’a
“Alhmadulillah”.
“Ok ga breakfast ɗin ki kizo kici”.