BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50
Nazeefa tace “a’a bazan iya cin komi ba, zan tafi Aunty sai kuma wataran in na sake dawowa ki gaida yaya”.
Saleema kallon ta kawai take yi cike da mamakin ta, sai kuma dai batace komi ba ta’amsa mata sannan tabata saƙon gaisuwa wajen Mom
Tana kallo Nazeefan har tafice sannan taci gaba da aikin ta
Drever yaɗauki Nazeefa yanufi da ita school ɗin su.
[11/16/2020, 6:56 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Four*
________???? *TWO MONTHS AGO*
A cikin wannan watannin abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da soma zuwan Halwa makaranta, tayi farin ciki matuƙa
Da farko Saleema ce ma Abba tayi yakaita Abroad tayi karatun, har Abba ya amince amma Halwa ita tace sam bata son tayi nesa dasu dole aka barta anan Katsinan
Tunda tasoma zuwa school ɗin babu ruwan ta da kowa harkan gaban ta kawai take yi, kuma sosai take gane karatun tunda shi tasaka a gaba
Duk da kuwa mutane da dama suna sonn ƙulla alaƙa da ita amma taƙi yarda musamman ma maza da yawancin su suke nuna suna son ta, wannan dalilin ne ma yasa take saka niƙap, da zaran drever ya kawo ta zata ɗau niƙap ɗin ta tasaka, idan kuma yazo ɗaukar ta sai ta shiga motan sai tacire
Har yanzu ta kasa manta tabon ɗa namiji cikin rayuwan ta, ta kasa manta abinda Haris yayi mata, sannan takasa manta abinda Nura yayi mata duk da kuwa har yanzu zuciyarta na mishi uzuri
Ko kaɗan ta tsani namiji yanuna yana son ta sabida tarigada ta cire soyayya cikin ranta
Zuwan ta gidan Saleema sau biyu shima daƙyar taje don aranta ko kaɗan bata son sake haɗuwa da Mijin nata da yatsaya mata arai yaƙi gushe wa, sau tari tana tunanin sa sai taji gabanta ya faɗi kuma tarasa me yasa, sai dai tana ƙoƙarin yakice sa aranta musamman ganin ta dena tuna sa gaba ɗaya, sosai take mamakin haɗuwa da cikan halitta irin Mijin Saleema, sai yanzu tagane abinda Saleeman tahango atare dashi har tamutu a ƙaunar sa haka, domin samun irin sa sai wanda yake da babban daraja wanda kuma yakai
Zuwan da tayi gidan duk sun haɗu amma gaisuwa kaɗai ke haɗa su, shima daga nan ko kallo baya sake yin mata har kuwa tatafi
Don shima a nashi fannin sosai yake son cire ta aran sa musamman yanzu da yasan matsayin ta a wurin shi, yana auren ƴar uwan ta, ko kaɗai baya son abunda zai kawo saɓani a tsakanin zaman sa da matar sa tunda yana jindaɗin zama da ita ainun
Amma abinda akace zuciya na so babu me iya raba ta da shi, bare shi da ya jima a ƙaunarta tun lokacin da be san ita ɗin wacece ba, a kuma kallo ɗaya da yayi mata, sau da dama yana mamakin irin Wannan soyayyan, har zama yake yi yayi ta tambayan kansa “wai dama ana soyayya irin haka daga kallon farko da akayi wa mutum koda kuwa baka san ko shi waye ba? Koda kuwa bakasan zaku sake haɗuwa ba?” A yanda take zuwa masa a mafarkin sa ne yake basa mamaki, kullum idan har be yi mafarkin ta ba to zai yi tunanin ta, idan har zata zo mishi kuma a mafarkin tana me kuka ne tana neman taimakon sa, ya kasa gane irin wannan mafarkin musamman yanzu da yaganta cikin gatan ta.
*______________________*
A fannin Nazeefa ma tana nan tana ta fama da son maso wani, ta ari damuwa duk ta yafa ma kanta, yanzu abun har yakai ko karatun ta bata maida hankali a kanshi
Mom tayi mitan sauyawan ta har ta gaji amma taƙi faɗa mata abinda yake damun ta
Wannan halin da take ciki kullum idan taje makaranta bata kula kowa ko ajin ma sai taga daman shiga, da zaran taje zata wuce bayan makarantan inda ɗalibai ƴan Pramary suke wasa taɓoye anan tazauna tayi ta tunanin ta
Ƙawarta Haneefa ita take damun ta kullum tafaɗa mata damuwarta, ta kai ta kawo ma har faɗa sukayi akan ƙin faɗa mata da tayi, daga ƙarshe dai Haneefa da taga fushin bazai kai ta ko ina ba sai tadawo tana rarrashin ta don tasanar mata damuwarta, daƙyar dai Nazeefa tabuɗe baki aranan tasanar mata tana yi tana kuka kamar ana yankan naman jikin ta, har wani rawa jikin nata yake yi sabida tsaban yau komi ya kai mata maƙura
Haneefa na zaune gefen ta tana bin ta da idanu cike da tsananin mamakin ta, bata hana ta yin kukan ba har sanda tayi ma’ishi tafitar da duk ƙuncin dake cikin ranta, sannan ne tadafa kafaɗan ta da hannu ɗaya tace
“Ban taɓa tunanin akan ɗa namiji bane kika shiga duk wannan damuwar Nazeefa, sabida ɗa namiji kika dena shiga aji kika dena mayar da hankalin ki kan karatun ki duk a sabida ɗa namiji? nayi mamaki wlh ƙawata duk kyawun ki kizauna kina ma ɗa namiji kuka”.
Shiru Haneefa tayi tana jan numfashi tare da tsare Nazeefan da idanu
Ita kuma Nazeefa alokacin ne taɗago kanta tana kallon ta da rinannun idanuwan ta tace “baza ki gane a halin da nake ciki bane Haneefa, zuciyata tariga da ta mutu a ƙaunar sa, nayi duk iya abinda zanyi don in cire sa araina amma na kasa, wlh ji nake yi kamar in mutu saboda yanda nake ji a kansa, bana jin zan iya auren wanin sa idan bashi ba, bazan taɓa zama da kowa ba sai shi, tun bansan meye so ba zuciya ta takamu da mahaukacin ƙaunar sa har sanda nagane, gashi yanzu yayi min ratan da samun sa babban wani aiki ne agare Ni”.
Dariya ma abun yaba ma Haneefa, sai tasaki baki tana yi
Hararan ta kawai Nazeefa tayi tana ɗauke kai cike da haushi
Tsai da dariyan Haneefa tayi tace “ƙawata kenan kin faɗa da yawa, Ni kuwa zan so ganin wannan Jarumin me babban matsayi a wurin ki, amma fa idan har kina son samun sa to ba wani babban aiki bane a wurin ki ƙawata sai dai idan kece baza ki bi hanyan da yadace ba, Allah na tuba don yana da mata sai kice yayi miki nisa?”
Kallon ta kawai Nazeefa take yi kamar idanun ta zasu faɗo ƙasa har sanda tadire aya kafin taɗaura da nata
“Wace hanya ce tadace da zanbi don samun sa? Kina ganin har akwai sauran hanyan da zanbi Ya Khalil yakalle Ni a matsayin Masoyiya?”
“Ƙwarai kuwa, me zai hana ki faɗa ma Mahaifiyarsa tunda ita tabuƙaci haka, na tabbata wlh zata share miki hawayen ki tunda tana ƙaunar ki”.
Shiru kawai Nazeefa tayi don tasan baza ta taɓa iya faɗa mata ba, to taya shi Khalil ɗin zai kalli maganar? Abinda take tunawa kenan, ba wai faɗan bane.. matsalan ta na ga Uban gayyar”.
Maganar Haneefan ne takatse mata tunanin ta, taɗago tana kallon ta cike da wani irin kallo me wuyan fassara, bakin ta har rawa yake yi wajen cewa
“Baki da hankali ne wannan wani irin shawaran banza ce? No bazan taɓa iya aikata hakan ba, idan kuwa nayi masa haka tabbas na zama butulu, tabbas idan na aikata hakan mutane zasu zage Ni sannan zasu la’ance ni tunda ban riƙe maraicina ba..”
Sai kuma tagirgiza kanta cikin kuka tace “bazan taɓa iya aikata masa haka ba, wlh gwara in mutu da in je wajen boka in cutar da wanda yataimaka min”.