BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

Haneefa cikin son nuna mata abunda take nufi tace “ƙawata ki gane mana hakan shine kaɗai mafita kuma hanyan da zaki samu zuciyar sa…”

Ɗaga mata hannu Nazeefa tayi tace “ya isa bana son ji, Kar ki sake min irin wannan maganan”.

Tana faɗan haka tamiƙe tawuce tabar Haneefa nan zaune baki sake tana bin bayan ta da kallo.

Tun daga ranan kuma sai Nazeefa tadena sake ma Haneefa fuska, ko tazo school ɗin babu ruwan ta da ita, ita a ganin ta Haneefa ba ƙawar kirki bace da har zata bata wannan shawaran, duka-duka ma nawa suke da har zata bata shawaran zuwa wajen Boka?

Ita ma dai Haneefan tasha jinin jikin ta, tun daga ranan itama taja baya da ita, idan ba gaisuwa ba babu abinda ke haɗa su, a ganin ta taimakon Nazeefa zata yi, amma tunda ta nuna bata so to itama ta bar maganan, duk ranan da komi yarincaɓe mata tazo taneme ta ita kuma anan ne zata taimaka mata.

.

*Facebook: Muh’d Lawal Nafisat*

*Wattpad: UmmuDahirah*

*WhatsApp number:07065334256*

_plz karku manta da share, Vote, Comments. Nagode._

[11/22/2020, 1:20 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Five*

________????Rayuwan Khalil da Saleema rayuwa ce da suke yin ta cikin jindaɗin juna da nuna ƙauna da kulawa, zuwa yanzu komi yana tafiyan musu dai-dai

Gefe ɗaya kuma ciwon Saleema na zuwa mata jefi-jefi, duk da tana shan magani amma wataran haka zata tashi da tsananin ciwo har asibiti Khalil yake kai ta, sai kuma daga baya ciwon nata yalafa

Yanzun ma kwana biyu kenan bata jindaɗi sai dai ba sosai ba tana yin duk aiyukan ta tare da taimakon Khalil, idan yana gida shi yake taimaka mata da rainon Husna, girki kuma hanata yayi sai dai yayi musu Take-away, idan tatashi kuma da ƙwarin jiki sai tayi musu girkin

…….. …….. ……. ……..

Yau tun safe da Khalil yatafi aiki bayan ta gama gyaran gidan tayi ma Husna wanka itama tayi, sun shirya cikin farar atamfa me zanen ja da ruwan goro, ɗinkin riga da skert akayi mata sai akayi ma Husna doguwar riga dai-dai ita, duk kwalliyan da akayi iri ɗaya akai musu a rigan

Fitowa Parlour tayi da Husna a hannun ta ta’ajiye ta saman carpet, ita kuma tahaye kan 3sitter takwanta, yau sosai jikin ta yamatsa mata ga sanyi da take ji sosai duk da kuwa ta kashe AC da Fan ɗin parlour’n

A hankali ciwon yaci gaba da cin ta, hakan yasa tamiƙe takoma ɗaki tahaye kan gado taƙudundune da bargo, nan da nan tasoma rawan ɗari.

Wajen awanni biyu da shigan ta Khalil yadawo gidan, da sallama yashigo cikin parlour’n, da Husna yasoma cin karo tayi wasan ta har ta gaji tasoma ƙananun kukan ta daga ƙarshe barci yaɗauke ta a dungure a wajen ta kofa kanta kamar wacce take sujjada

Dasauri yaƙariso yana ajiye briafcase ɗin sa yasaka zara-zaran hannayen sa yaɗauke ta, sannan ne yaga ashe barci take yi, murmushi yayi yana kallon fuskarta da tataɓe baki duk hawaye ya gama bushe mata a fuskar

Gaban sa ne yafaɗi sakamakon ganin yanda kamannin ta da Halwa yasake fitowa ainun, basu da maraba a yanzu ɗin

Shiru yayi yana ƙure ta da kyawawan idanun sa, ya ɗau tsawon mintuna 3 kafin yamiƙe yanufi ɗakin Saleema da ita a hannun sa, yana shiga yahangi Saleeman kan gado nannaɗe cikin bargo

Dasauri yanufi bakin gadon dan yasan babu lafiya, ajiye Husna yayi can ƙarshen gadon kafin yamatso kusa da Saleeman yana zama ya yaye bargon yana kiran sunan ta

Zafin da yabuge sa ne yayi saurin sake yaye bargon yana tallabo kanta, nan yaga fuskarta sharkaf da hawaye idanun ta kuma sun kaɗa sunyi jawur gunun tausayi, gaba ɗaya jikin ta rawa yake yi ga shegen zafi kamar tafashashshen ruwa, shi kanshi dauriya yayi wajen riƙe ta

Cikin tsananin firgici yace “subhanallah.. Saleema meke damun ki? Tun yaushe kika fara ciwon?”

Bakin ta rawa yake yi ta ma kasa magana in banda hawaye da ke zuba kan kuncin ta yana gangara ta gefe yasauka hannun sa

Dasauri yakwantar da ita yana miƙe wa cikin sauri, wayan sa yaɗauka yakira doctorn ta, sai dai baya shiga hakan yasaka ya’ajiye wayan yafita da sauri

Sai kuma yasake dawowa yaɗauki Husna yakaima drever akan yakaita gida sannan yadawo yatallabi Saleema yasaka mata Hijab suka fito

A back seat yakwantar da ita yashiga yaja motan yafice cikin gidan da mugun gudu.

*___________________________*

   Drever na zuwa gidan su Saleema Gateman yamiƙa ma Husna sannan yatafi

Nocking gate man yayi a bakin Parlour

Halwa na tsaye gaban Fridge tana shan ruwa, dawowar ta kenan dama daga makaranta tasoma nufan Fridge ɗin, ajiye ruwan tayi tanufi ƙofan tabuɗe, kallon Gate man tayi tare da Husna dake hannun sa

“Dama drever ne yakawo ta inji Mijin Hajiya Saleema”. Cewar Gate man ɗin yana kallon Halwa

Mamaki ne Yakamata amma sai batace komi ba ta’amshe ta tarufe ƙofan takoma cikin parlour’n, ajiye ta anan ƙasan carpet tayi tanufi kan kujera inda jakar ta yake tazaro wayan ta tasoma kiran numban Saleema, sosai hankalin ta yaba ta babu lafiya ne don tasan babu ta yanda za’a yi Saleema tayarda adawo da Husna, ƙirjin ta sai fat fat fat yake yi gashi Ummi tana Hospital kuma tace mata zata biya anguwa, so dawowarta ma ba yanzu ba

Ringing wayan take yi but not answer, zuwa lokacin Halwa ta kasa zama sai Safa da marwa take yi tana sake danƙara mata kira, tsaki taja tana ɗaukan jakan ta tanufi ɗakin Saleema wanda yazama nata a yanzu

Ta dawo makarantan yau agajiye Allah-Allah take yi tadawo tayi wanka ko zata rage gajiyan, ga mugun yunwa dake addabar ta, amma a yanzu bata jin zata iya cin wani abu idan har batasan halin da take ciki ba, kayanta tacire tashiga wanka.

Larai ce tafito daga ɗakin ta tahangi Husna tana kuka, dasauri taƙarisa wajen ta taɗauke ta tasoma jijjiga ta tana tambayan ta “ina Mamarta? Wa yakawo ta?” Sai kace tana jin ta

Ɗakin Halwan tanufa tunda a tunanin ta Saleeman ce tazo gidan, amma koda tashiga babu kowa sai ƙarar ruwa da taji, hakan yasa tafita takoma ɗakin ta da Husnan.

*________________________________*

Lokacin da Khalil yakai Saleema asibiti Ummi tabar asibitin

Emargancy ward aka nufa da ita, hankalin Khalil duk ya tashi haka yake ta Safa da marwa, gashi be zo da wayan sa ba bare yakira gidan su yasanar musu

Wajen 1hour aka ɗauka ana duba ta kafin likitan yafito yabuƙaci ganin Khalil, kan dai matsalan ciwon ta ne sai kuma shigan ciki na sati Uku, gashi kuma sun gano da matsala sosai a mahaifar ta zai yi wuya ta’iya ɗaukan ciki har yagirma a jikin ta, sai dai sun ɗaura ta akan magani don aga yanda hali zai yi

Hankalin Khalil sosai yasake tashi da jin bayanin doctor, sai dai komi ya fawwala ma Allah hakan shine cikan imani

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button