BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

Motar sa yashiga yanufo gida tunda dama a kulawan likitoci take, yanke shawara yayi yasoma wucewa gidan su Saleeman yafaɗa ma iyayen ta don haka yakarya kan mota yanufi gidan.

_…… …….. ……. ……. ……_

Fitowar Halwa a wanka doguwar riga kawai tazira taɗaura ɗankwalin rigan tafito parlour

Tana zama Larai tafito cikin ɗakin ta goye da Husna abaya zataje kichen

“Au Ashe kin fito? Na shigo ɗakin ai duba ko Saleema ce tazo amma bangan ta ba”.

Halwa kallon ta tayi da yanayin damuwa a face ɗin ta tace “eh na fito amma ba Saleeman bace tazo drever ne yakawo ta”.

“Allah yasa dai lafiya ko?” Larai tafaɗa itama a yanayin wasi-wasi

Domin sun san babu yanda za’a yi akawo ta gidan idan har ba Saleeman bace tazo

“Wlh nima bansani ba, na kira dai wayan ta amma shiru ba’a ɗaga ba hankalina duk ya tashi, nayi tunanin kiran Ummi kuma kar yazo fahimtar mu ce hakan”.

Larai tace “eh gwara kam kar ki kirata saboda bamu da tabbacin ko matsala ne, amma dai kici gaba da gwada kiran wataƙil adace”.

Gyaɗa kanta kawai Halwa tayi taci gaba da kiran wayan kamar yanda Larai ɗin tace

Ita kuma Larai kichen tanufa don ɗaura girkin dare

Tashi Halwa tayi tanufi kan dainning tazauna, sosai take jin yunwa kamar hanjin ta zai tsinke, yau bata ci komi a school ba haka taje tadawo

Zama tayi tazuba abincin da yakasance Macoroni ne me manja, tana cin abincin tana sake kiran layin Saleema, ko kaɗan ta gaza haƙura, zuwa yanzu hankalin ta yayi ƙololuwar tashi, tabbas tasan akwai matsala

Abincin ma sai yakoma baya mata daɗi, turewa tayi dai-dai da lokacin da taji ana buɗe Gate ɗin gidan

Dasauri tamiƙe tanufi hanyan fita don tasan bazai wuce Ummi bane ko Abba, hankalin ta ne ya gaza kwanciya shiyasa tanufi wajen don tarban su duk da kuwa bata san me zatace musu ba

Tana fita tahangi motan da bana gidan ba, bata san cewa Khalil bane aciki tunda bata ganin shi, kuma ba wai tasan motan gidan shi bane bata tsayawa kallo bare ta tantance, tasan dai yana da motoci aƙalla sun kai biyar agidan

Shi kuwa tun sanda tafito idanun sa yasauka akan ta, har yayi parcking yafito yarufe motan

Zuciyar ta ne tabuga sakamakon ganin sa, duk da dama idan har zata ganshi hakan ke faruwa da ita amma kuma da fargaban ko wani abu ne yasamu Saleema, tana nan tsaye tana kallon sa yayinda zuciyarta ke ci gaba da dukan uku-uku, gaba ɗaya ta dunƙule hannun ta waje ɗaya saboda rawan da suke yi, daƙyar ta’aro jarumta da ya’iso wajen tagaishe sa

Amsa mata yayi yana ci gaba da kallon ta kamar zai cinye ta, tsananin ƙaunar ta ne ke ɗawainiya dashi, ya jima rabon da yaganta sai yaji wani sanyi aransa tare da wucewar wani abu da yatsaya masa a maƙoshi kwana da kwanaki

Matsa masa a hanya tayi batace komi ba

Shi kuma sai yashiga kafin tabiyo bayan sa

A kan ɗaya daga cikin kujerun yasamu wuri yazauna

Ita kuma taje taɗauko masa ruwa duk da kuwa batasan ko yana buƙata ba

Ajiyewa tayi a gaban sa saman Centre table tajuya da ninyan wuce wa duk da kuwa tana son tambayar sa Saleema, gashi kuma yanda idanun sa yake faman yawo ajikin ta yayi bala’in takura ta

Har ta soma tafiya taji sassanyan muryan sa yayi mata magana

“Ina Ummi?”

Juyowa tayi sai dai wannan karon baza ta iya kallon sa ba tasad da kanta ƙasa tace “bata dawo ba”.

Shiru yayi kamar bazai yi magana ba

Ita kuma hankalin ta yagaza kwanciya, bata san sanda tajeho masa tambayan

“Meke damun ƴar uwata?” Tayi maganar idanun ta na kansa

Kai tsaye Khalil yasanar mata inda take

Hankalin Halwa atashe kamar zatayi kuka tace “don Allah zan bika mu tafi”.

Gyaɗa mata kai kawai yayi yamiƙe yanufi hanyan fita

Dasauri taɗau wayan ta tacire ɗankwalin ta tayafa tabi bayan sa, lokacin har ya shige motan ya tayar yana jiran ta

Cikin sassarfa taƙarisa tabuɗe gaban tashiga yaja motan yafice bayan da me gadi yabuɗe masa Gate ɗin

Duk da Khalil yana son zuwa gida amma bazai ƙi biya mata buƙatar ta ba, wannan dalilin ne yasaka yayi tunanin kai ta kafin yakoma gidan

Koda yakaita be daɗe ba yace mata zai tafi

Bata tanka shi ba har yafice, sannan ne tasoma kiran layin Ummi, bugu biyu taɗauka anan Halwa tasoma sanar mata Saleema ce babu lafiya tana Hospital

Hankalin Ummi ya tashi nan da nan takaryo motan ta don har takusa isa gida, tana zuwa tatarar da Saleeman barci take yi Halwa ta tasa ta gaba sai kallon ta take yi

Fita tayi tanufi Office ɗin Doctor ɗin ta, anan take jin bayanin matsalan Saleeman, idan hankalin Ummi yayi dubu to ya gama tashi, sosai taruɗe da jin abinda ke faruwa

Koda tafito lungu tasamu tafashe da kuka na tsananin tausayin ƴar nata, babu abinda bakin ta ke furtawa sai salati, tabbas Saleema tana cikin jarabawa

Da fari ciwon zuciya sannan kuma ciwon hanta, yanzu kuma ga ciwo a mahaifar ta wanda ke barazanar da zata rasa haihuwa har abada

Tasha kuka sosai kafin tashare hawaye tagyara fuskarta, sannan taciro wayan ta a jaka takira Abba tasanar masa

Shima babu jimawa yataho

Gaba ɗaya sun yi zugun a ɗakin sun saka ta gaba sai kallon ta suke yi

Sai gab da magriba tafarka lokacin shima Khalil ya dawo, sosai take jin jiki don ko magana bata yi

A lokacin ne Abba ya lallaɓa Ummi suka tafi gida da Halwa tunda an sake mata alluran barci ta koma

Babu jimawa itama Mom tazo tare da Nazeefa, sun jima har wajen ƙarfe 11:00pm kafin suka tafi

Khalil shi yace zai kwana da ita don haka babu musu Abba yataho yabarta.

[11/24/2020, 2:36 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Six*

________???? Wasa-wasa sai da Saleema tayi kwana biyar cur kafin tasoma samun sauƙi, sai kuma daga baya ciwo yazo mata rigigim, blending take tayi nan likitoci suka rufu akan ta

Halwa kuka Ummi kuka sun rigada sun cire rai ma Saleema zata iya rayuwa

Khalil shi kansa ya rasa inda zai saka kansa, tsananin tausayin matar sa gaba ɗaya ya cika sa, sosai yadamu da halin da take ciki

A ranan duk wani me tausayi dole yatausaya mata, ashe wai duk ɓari zatayi shine yaja mata hakan, sai da aka ƙara mata jini leda biyu sabida yanda tazubar da jinin ta wajen ɓari

Kwanan ta biyu kafin tafarfaɗo, sosai Saleema tayi jinya gaba ɗaya ta rame tayi baƙi sabida jinin da ake ƙara mata, kullum zuwa gaishe ta ake yi

Ita Halwa ma gaba ɗaya dena zuwa school tayi sai da tasoma samun sauƙi sannan ne Ummi tatakura mata tafara zuwa

Idan kuma tadawo nan take fara wuto wa sai dare takoma gida

Haka shima Khalil yake yi, duk da aiki yayi masa yawa amma kullum yana kan zuwa

Satin ta ɗaya aka sallame ta duk da ba wani warkewa tayi ba amma haka takoma gida tana jinya, Khalil shi ke kula da ita ko kaɗan baya gajiya, tausayin ta tsantsa ne a ransa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button