BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

Haka rayuwa taci gaba da shuɗewa gashi yanzu har an shafe watanni uku da ciwon da Saleema tayi, yanzu komi ya koma normal sai dai ciwon da ba’a rasa ba wanda take fama dashi koda yaushe.
*________________________________*
Ƙarfe 03:20pm. Su Zainab da friends ɗin ta suka fito lectures
Tafiya suke yi suna hira ɗaya daga cikin su tana basu labarin gwaraman da akayi a anguwan su, sai dariya suke yi sabida yanda me basu labarin ta dage tana nuna yanda matar take ɗaukan mijin ta tana tiƙa sa da ƙasa
Daga bayan su can ɗan nesa kaɗan Halwa ce ke tafiya tana latsa wayan ta, tun daga inda take tana jiyo dariyan su sai dai hankalin ta baya kansu sai faman neman layin Drever take yi
Yau yayi late be zo ya ɗauke ta ba shiyasa take sake kiran sa taji inda yake, yana ɗagawa yace mata “gashi nan yanzu zai shigo school ɗin”
Tsayawa tayi a wajen har sanda tahango shi ya shigo cikin makarantan, sai tanufi wajen shi tana ɗaga masa hannu, shima ɗin ya ganta don haka yatsaya tahau yaja yayi reverse suka nufi bakin Gate
Lokacin su Zainab har sun kusa fita motan tazo tawuce su, har alokacin sai faman dariya suke yi, ahaka suka fita cikin school ɗin cike da nishaɗi
Suna fita sauran friends ɗin ta duk suka dare biyu daga ciki sukai musu sallama suka ci gaba da tafiya sabida babu nisa da gidajen su, ɗaya ce tahau keke napep tatafi aka bar Zainab ita kaɗai tunda ba hanya ɗaya zasu bi ba
Tana nan tsaye wajen sai ga wata dalleliyan mota ta faka a gaban ta, tunda takalli motan sau ɗaya takau da kanta tana kicin-kicin da fuska
Fitowa yayi daga cikin motan yana kallon fuskarta, ɗan taku uku yayi ya’iso gaban ta, murmushi yasaki yace
“Plz Zainab don Allah kihau in Kai ki gida, yau rana ɗaya dai kiyi min wannan alfarman”.
Tsaki Zainab taja batare da ta kalle sa ba, ji take yi idan har tatanka masa zuciyarta zata iya bugawa sabida tsaban jin haushin sa, don haka batace komi ba tajuya taci gaba da tafiyan ta
Nura kallon ta kawai yake yi har sanda taɗan yi nisa sannan yanufi motan sa yashiga yabi bayan ta
Kullum ranan duniya sai yazo domin ta amma bata taɓa masa kallon arziƙi ba, kuma shi be taɓa gajiya ba sabida yanda yake jin ta cikin ransa, duk wulaƙancin da zata yi mishi zai iya jurewa idan har zai same ta, yana matuƙar ƙaunar ta fiye da tunanin mutum
Yana biye da ita abaya har sukai nisa, gashi ta kasa samun keke napep duk rana sai faman gasa ta yake yi
Shi kuwa gab da ita yazo suka jera yana mata magiya ta cikin motan amma firr Zainab taƙi kallon sa bare tatanka masa
Gajiya tayi kawai tasamu acaɓa tahaye tunda babu napep ɗin
Nura yana kallon ta har tahau suka tafi yabi bayan su, duk inda me machine ɗin yabi nan shima yake bi har suka kawo ƙofar gidan su Zainab ɗin tasauka tamiƙa ma me machine ɗin kuɗin sa tajuya tashige gida batare da ta amshi canjin ta ba, don baƙin cikin ganin Nura ƙofar gidan su ya hana ta ma tsayawa
Ajiyan zuciya Nura yasauke yana bin ƙofar gidan da kallo, ya jima acikin motan.. shi be tafi ba shi kuma be fito ba, sai da yashafe mintuna 20 zaune anan kafin yafito yana rufe motan
Kalle-kalle yai tayi sai daga baya yahangi yaro yakira sa yace masa yashiga ciki yakira masa Zainab
Da gudu yaron yashige gidan
…… ……. ……. …..
Zainab tun shigan ta da tayi sallama taji babu umma sai tashiga ɗaki kawai ta’ajiye jakar ta tare da gyalen ta tafito tashiga kichen taɗauko abincin ta
Zama tayi anan farandan ɗakin su taci abincin tagama, miƙe wa tayi takai coolarn wajen wanke-wanke taɗibi ruwa a buta tashiga Toilet.
Tana cikin Toilet ɗin tajiyo sallaman yaro, bata amsa ba har sanda tafito tabi yaron da kallo, bata raba ɗayan biyu Nura ne ya’aiko shi
Ai kuwa bata gama tunanin zucin ta ba yaron yace
“Wai ana kiran Zainab a waje”.
Ajiye Butan hannun ta tayi tazauna kan dutse a bakin Toilet ɗin, sannan takalli yaron tace
“Je kace masa baza ta zo ba”.
Babu musu kuwa yaron yajuya yatafi don isar da saƙon ta
Sosai baƙin ciki ke ɗawainiya da Zainab, ta rasa wani irin maye ne wannan mutumin, ko kaɗan ita bata ƙaunar sa a ranta bata jin kuma zata iya son sa ko anan gaba, sa’ar ta ɗaya Umma bata nan amma da dole sai ta saka ta fita
Shiyasa take roƙon Allah aranta Allah yasa yatafi kafin Umma tadawo
Ta soma alwala kenan yaron yasake dawowa yace
“Wai yace don Allah tazo zai bata saƙo ne”.
“Dan ubanka wuce anan gidan”. Zainab tafaɗa cikin tsawa tana zazzare ma yaron idanu
Da gudu kuwa yasheƙa yafice har da waigen ta
Baƙin ciki da ƙunci ne suka taru mata iya wuya, ta rasa me za tayi ma Nura don huce takaici
Ƙyalla idon ta tayi tahangi taɓarya, dasauri tatashi tanufi wajen taɓaryan taɗauka tayi hanyan fita a fusace
Yau dole ne sai ta kawo ƙarshen zuwa wajen ta da yake yi.
.
_hahaha Fans kar ku damu ba daku zata rotsa ma kai ba, Nura kawai tanufa banda ku._
_Kuyi haƙuri da wannan babu yawa, aiyuka sun yi min yawa shiyasa nayi muku ɗan kaɗan._
_kar ku manta da Comments ɗin ku shi ke ƙara min ƙwarin gwiwa._
_Ina jiran Comments ɗin ku shin ayi maganin Nura ko ya? Nasan da yawa haushin sa kuke ji bayan kuma be muku komi ba bawan Allah._????
[11/24/2020, 2:50 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Seven*
________????Tana shiga zaure sukaci karo da Umma dole taja tatsaya tana ƙifƙifta ido
Umma da tafiddo ido waje tana kallon Zainab ɗin da taɓaryan dake hannun ta tace “na shiga uku ni Jummai me zan gani haka Zainab? Ashe dama baki da mutunci dan ubanki? Yanzu abun naki har ya kai kifita da taɓarya kije wajen Nura? To me kike shirin aikatawa kenan?”
Turo baki Zainab tayi tana sosa kai, sai kuma tajuya dasauri tayi ciki tana jefar da taɓaryan
“To dan ƙwal uwar ki zo ki wuce kije wajen shi”. Cewar Umma tana bin bayan ta itama tashiga cikin gidan
“Wlh Umma babu inda zani, nifa nace miki bana ƙaunar sa bana son sa bana son sa, Ni bazan iya son sa ba wlh”.
Umma kama haɓa tayi tana kallon Zainab ɗin dake masifa kamar batasan da wa take yi ba
“Zainab Ni Sa’an wasan ki ne ina faɗa kina faɗa? Wlh sai kin fita ko in saɓa miki kamanni, shashashan yarinya mara hankali..”
Kuka Zainab tafashe dashi
Sai umma kawai takama haɓa tana kallon ta
Cikin kukan take cewa “wlh Umma bana ƙaunar sa, koda kuwa be so Halwa ba Ni bana son sa, har cikin raina nake faɗa miki bazan iya auren sa ba wlh”.
Sai taja majina tanufi wajen butan ta tazuƙuna tasoma alwala
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un yanzu Zainab har kin isa in saka ki abu kice baza kiyi ba? Baza ki tashi ki wuce ba yana jiran ki?”
Cikin tsananin ɓacin rai Zainab tace “Umma zan yi sallah ne lokaci na ƙurewa, kuma kinsan illan rashin yin sallan Asar da wuri, yana ɗaya daga cikin sallolin da ake so mutum yakula…”