BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

“Dalla rufe min baki, kiyi sauri ki idar kizo ki wuce”.
Zainab bata sake cewa komi ba taci gaba da alwalan ta, sosai take mamakin Mahaifiyar ta akan yanda tasauya lokaci ɗaya akan Nura, duk da tasan Nura yana banka mata kuɗi da kaya amma kuma bata taɓa tunanin zata sauya har haka ba
Tana idar wa tashiga ɗaki tasaka Hijab tasoma sallah, ta ɗau lokaci tana yin Sallah taƙi tasallame sai da Umma tazo tasake mata magana sai faman masifa take mata
Dole Zainab ba don taso ba tamiƙe tafito tafice
Tana fita kuwa taganshi tsaye gaban motar sa, ta rasa wani irin mayen mutum ne wannan
Nura tunda tafito kallon ta kawai yake yi yana murmushi, ko kaɗan be ji haushin daɗewan da yayi a wajen ba tunda Umma tace mishi yajira zata fito, kuma yasan dole zata fito ɗin
Wani mugun kallo Zainab tabuga masa tana jan tsaki taɗau hanya taci gaba da tafiyan ta batare da taƙarisa inda yake ba
Yana kallon ta har taƙule ma ganin shi
Ita kuwa tana shan kwana tasheƙa aguje bata tsaya ko ina ba sai gidan Yayarta Zaituna
Suna zaune ita da kishiyarta suna ƙullin Gishiri sai ganin ta sukayi ta faɗo gidan
“Subhanallah..lafiya Zainab?” Atare suka tambaye ta yayinda Zaituna taƙara da faɗin
“Wa yabiyo ki ne kika shigo haka kamar an jeho ki?”
Zainab da tariƙe gwiwowin ta tayi ruku’u tana numfarfashi ta ma kasa magana
Kishiyar me suna Murjana tace “ikon Allah wai lafiya ko dai gudun fanfalaƙi kika yi ne?”
Bata ce komi ba tanufi wajen randan ruwan su tana sake jan numfashi, ɗiban ruwan tayi tasha kafin tadawo taja kujera ɗan tsuƙuno tazauna agaban su, duk sun tsare ta da idanu suna ganin ikon Allah kuma suna jiran suji abinda yakoro ta gidan da gudu
Sai da taƙara gyara zaman ta tana kallon su tace “wlh daga gida nake..”
Tsaki Zaituna taja tana hararan ta tace “amma kinji kunya wlh, ƙatuwa dake shine kika sheƙo hanya da gudu ga mutane ko kunya ko?”
“To Aunty ki tsaya mana kiji me yakoro Ni, wlh Umma ce tatakura min akan maganar Nuran nan shiyasa na’ari na kare nayo nan”.
Dariya Murjana tayi tace “kai wlh Zainab baki da dama, to Ni wai meye laifin Nuran nan kullum kina wahalar dashi? Magana dai taƙi ci taƙi cinye wa”.
Taɓe baki Zaituna tayi tace “kema dai kya faɗa, bata da hankali Zainab ko kaɗan, wai inace duk kina wannan abun ne don Halwa?”
“Aunty baza ki gane ba wlh, nifa gaba ɗaya tun sanda yasoma nema na natsane shi, wlh koda ba batun Halwa aciki Ni bazan iya auren sa ba, kullum idan yazo min da nacin nan nasa kullum sake jin tsanar sa nake yi araina”. Zainab tayi maganar cike da baƙin ciki
“Aiki ya ganki”. Zaituna tafaɗa tana ci gaba da ƙullin ta
Murjana tace “kiyi ma kanki faɗa don Allah, ko wace mace tana burin tasamu masoyi me ƙaunarta amma ke kin samu kina wasa da damar ki, wlh Nura yana son ki tunda kikaga yana jure wulaƙancin nan naki, Zainab babu batun yaudara anan ki karɓe shi hannu bibbiyu tun kafin lokaci yaƙure miki, dama ce tazo miki har gida, idan kuma kikace zaki tsaya tunanin wata to zaki rasa wannan damar taki, ki duba magana ta”.
Numfashi Zainab taja, baza su taɓa gane abinda take nufi ba, ita tayi alƙawarin wlh sai dai gawan ta za’a kai gidan Nura amma baza ta taɓa auren sa ba, koda kuwa Halwa ce tazo da kanta tace ta’aure shi, amma a yanzu tarigada ta ƙudurta ma kanta dole ne tasamu saurayi tayi aure ko Allah zai sa yabarta, ada dai bata da burin aure yanzu amma tunda taga abun yazo da haka tasan komi zai iya faruwa
Yanzu ma baza ta koma gidan ba sai dare, sai dai idan ta koma Umma tahaɗiye ta
Hannu tasaka tasoma tayasu ƙulla gishirin batare da tasake cewa komi ba
Su kuma tuni sun sauya zancen ma sun ci gaba da hiran su da suke yi.
.
*__________________________*
*BAYAN WASU WATANNI*
A halin yanzu Saleema tasake samun ciki a karo na biyu, kamar dai wancan haka tasha baƙar wahala watan shi ɗaya yafice bayan da tazubar da jini sosai kamar baza ta rayu ba
A wannan lokacin ne kuma tasan matsalan ta, tayi kuka kamar baza ta dena ba, har sai da iyayen nata sukai dana sanin faɗa mata sabida gudun tashin ciwon zuciyarta
Ita kanta Halwa ta taya ta kukan kuma ta tausaya mata sosai
Sai da tayi jinya na tsawon sati biyu a asibiti kafin a sallame ta
Tun daga ranan kuma Khalil yasoma bata maganin hana ɗaukan ciki batare da sanin ta ba, ita a ganin ta duk cikin drugs ɗin da aka bata ne a asibiti tunda wani lokacin shi ke bata magungunan, kuma bata taɓa saka wa aranta zai iya cutar da ita ba bare tayi tunanin wani abu, sosai yake matuƙar tausaya mata baya son tasake shan wahala kamar yanda tasha a baya, duk da yana son yara amma hakan shine mafitan da zai iya taimaka mata idan har yana tausayin ta
A sannu a sannu rayuwa taci gaba da tafiya, tun Saleema na damuwa da matsalan da take fama dashi tunda itama tana ƙaunar yara har dai tacire komi a ran ta, ta buƙaci a dawo mata da Husna taci gaba da riƙe ta amma firr Ummi taƙi tunda har yanzu jiya iyau take, yau lafiya gobe ciwo, kuma Ummi tayi tayi takawo mata ƴar aiki but Saleema ta baɗe ma idanun ta toka akan baza’a kawo mata ƴar aiki ba, ita ta saka a ranta duk ƴar aiki tana ƙwace Mijin matar gida ne, shiyasa take jin tsoron a kawo mata ƴar aiki watarana taƙwace mata miji, anan Ummi tace “to tunda baza ta yarda akawo mata me taimaka mata ba dole tahaƙura da rainon Husna har sai taji sauƙi”, ba da son ranta ba haka tahaƙura
Khalil na iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya taimaka mata ainun, a haka zaman su yaci gaba har zuwa wani lokaci, kuma har a lokacin soyayyar Halwa na nan cikin zuciyar sa sai dai ya binne abun aransa tunda babu yanda zai yi
Ita kanta Halwan abun da take ji akan sa ne har yanzu takasa sakin jiki dashi bare su saba, ko magana zata iya ƙirga iya adadin da yataɓa shiga tsakanin su, sau tari idan tayi tunanin komawa gidan Saleema don ta tayata zama sai ta fasa, bata son ko kaɗan abinda zai sa su haɗa hanya, duk da har yanzu batasan menene musabbabin abinda yasa take jin haka daga gare shi ba, amma ita a ganin ta nesa dashi shine kwanciyar hankalin ta
Har yanzu kuma bata taɓa tunanin yin saurayi ba duk da kuwa ansha biyo ta, amma a ranan farko take taka ma mutum burki
Ummi kanta sai da tazaunar da ita akan tadena koran samari auren nata shine abunda yadace da ita, amma ita Halwa abinda take hangowa tabon da ɗa namiji yayi mata a rayuwa, ta tabbata ko wanene zai so ta idan har yasan da Husna wacce tahaife ta bata hanyar aure ba to zai tafi yabarta, bata son taba ma namiji yardan ta a karo na biyu, tunda wanda yafi kowa sanin ta a duniya kuma yafi kowa sanin me zata iya aikata wa ya juya mata baya akan hakan, tayi imani ko waye ma hakan zai mata, shiyasa maganin kar ayi kar a fara, ta yarda zata ci gaba da rayuwan ta ahaka har ƙarshen numfashin ta, idan har ba Nura bane yadawo gare ta to bata jin zata iya auruwa
A yanzu haka ta shiga aji na biyu, babu abinda tasaka a gaba sai karatu, ko ƙawaye taƙi yarda tayi har yanzu, sai dai mutunci kawai da take yi da wasu daga cikin ƴan ajin su
Har yanzu har gobe tana tunawa da ƙawarta Zainab, sau tari tana tunanin zuwa koda gidan su ne, amma kuma hakan na nufin kamar ta tona ma kanta asiri ne duk ranan da takoma wajen waɗanda suka santa, kuma hakan na nufin zubar da mutuncin su Baba kamar yanda suka guda tun farko, wannan dalilin yake saka wa tafasa zuwa.