BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 41 to 50

.

*____________________________*

Baku tambaye Ni labarin Haris ba?

Tunda baku tambaya ba nima bari in ƙyale KU, byeeee???????????? sai ajiman ku ko in CE sai gobe.????????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️

_kar ku manta don Allah ????????ku danna Vote sannan kuyi comments don jin ra’ayoyin ku, na gode._

[11/24/2020, 3:14 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Eight*

________????Haris ɗan wani babban attajiri ne ɗan siyasa, yanzu haka yana riƙe da kujeran Minister, shi ɗaya ne ɗa wajen iyayen sa duk da iyayen Familyn su ɗaya ne kuma babban Family ne dasu

Ya taso cikin gata sosai, babu abinda yarasa a rayuwan sa, wannan dalilin ne yasa yake taka duk wanda yaso yakuma hukunta duk wanda yake ƙi, sabida yana da ɗaurin gindin mahaifin sa don ko kaɗan baya ganin laifin sa

Haris yana da son mata da yawa sannan kuma yana da farin jinin ƴan matan, su da kansu ƴan matan suke kawo kansu wajen sa don yayi amfani dasu yabiya su kuɗi, duk da sau da dama suna kawo kukan su akan ya taimaka ya aure su amma shi a ganin sa babu macen da ta’isa yaso ta, shi dai kawai ya san mata a wajen sa su biya masa buƙata ne yajefar dasu don basu da wani Amfani

Ana cikin haka kwatsam yazo giftawa ta hanyar makarantar su Halwa yakusa bige ta, tun a lokacin da yaganta yakamu da tsananin kaunar ta har yana jin koda zai yi aure to babu shakka ita zai aura, duk da alokacin mafi rinjaye na zuciyarsa sha’awar ta ce, amma kuma ita kaɗai ce yake iya mata kallon wacce zata iya kasancewa matar sa anan gaba

Sai dai abinda be sani ba Halwa ta mutu a ƙaunar Nura a lokacin, duk da alokacin yaso yanuna mata kuɗi da gadara, amma da yaga yarinyan tana da taurin kai babu yanda zai yi yasame ta sai yakoma yana bin ta talalama

Sai kuma tsautsayi yagifta a ranan da Halwa tamare shi, wannan dalilin ne yaɗau alwashin sai yayi mata abinda baza ta taɓa mantawa dashi ba, domin kuwa tunda yake babu wanda yataɓa taɓa masa lafiyan jiki

A lokacin babu abinda be sani akanta ba, har soyayyar da suke yi da Nura ya san komi sabida yana da yaran da suke bibiyan masa ita

Abu na farko da yasoma yi shine neman Nura, har gida aka kawo masa Nura kuma yafaɗa masa buƙatarsa, a lokacin Nura be amince ba sai da yaji kuɗi Miliyan uku da yayi masa alkawarin zai basa in dai zai sadaukar masa da budurcin Halwa, shi a ganin sa idan har yakawar da sha’awar Halwa aransa to tabbas duk wani soyayya da yake mata zai gushe, wannan dalilin ne yasaka yanemi aikata mata fyaɗe bayan ya nemi taimako wajen Nura

Shi kuma Nura babu musu ya amince, a ganin sa idan har yasadaukar da budurcin Halwa akan wannan zunzurutun kuɗin be faɗi ba, kuma hakan yana ganin dama ce tazo mishi da zai yi kuɗi batare da yasha wahala ba, sannan yarigada ya saka ma ransa shi zai auri Halwa ɗin yarufa mata asiri tunda SHINE SILA, kuma shine zai ɗau alhakin duk abinda zai same ta don yarage girman laifin sa

Take nan ya amince sannan suka shirya yanda za’a yi har Halwa tazo hannun Haris, kamar yanda kuka gani abaya

Duk wannan abinda yafaru da Halwa da haɗin bakin Nura, sannan kuma lokacin da yaji maganar ciki hankalin sa yayi mugun tashi duk da alokacin yana tunanin bazai iya auren macen da yasan ba ta tare da mutuncin ta ba, anan ne dabara yazo masa har yanuna shi be san da maganar Fyaɗen da akayi mata ba don kawai ya yakice ta ajikin sa

Haris kuma tun sanda yayi mummunan aika-aikan nan yakoma Abuja kasancewar acan yake aiki, yana kula ma mahaifin sa da ƙaramar Companin sa da yabuɗe na Shinkafa, amma me tunda yakoma sai yazamana bashi da sukunin zuciya, ƙaunar Halwa tayi masa bakeke a rai ta hana sa saƙat, be taɓa tunanin sonta ya kai haka ba sai da yayi nisa da ita, ya so yadanne yajure ko zai manta da ita amma hakan ba me yiwuwa bane

Dole yadawo gida don ganin ta ko yaji sanyi a ransa, lokacin watan sa biyu acan kuma a lokacin tuni Halwa tayi wajen two weeks da barin gida

Dawowar sa da jin abinda yafaru wajen Nura hankalin sa yayi ƙololuwar tashi, yayi baƙin cikin koran ta da sukayi da cikin sa ajikin ta, ya sake shiga damuwa matuƙa, haka ya bazama neman ta ko Allah zai sa adace, domin ya rigada ya ɗau alwashin muddin yaganta zai aure ta kuma su raine abunda zata haifa, yana matuƙar son ta bazai iya rabuwa da ita ba, har Gombe can dangin mahaifin ta sai da yaje amma akace bata zo ba, su ma alokacin suka ji abinda yafaru, sai dai basu wani damu ba tunda Mama ta faɗa musu cikin Shege tayi suka koro ta nan ashe bata zo ba, su aganin su hakan ma da tayi yadace tunda ko tazo su ma ɗin korata zasu yi don baza su iya riƙe ta da abun kunya ba

Rayuwa ta sauya ma Haris matuƙa ya shiga damuwa sosai akan rasa Halwa wanda har sai da yakwanta ciwo, kullum bashi da buri idan ba yahaɗu da ita ba, a haka iyayen sa suka tilasta masa auren ɗaya daga cikin dangin su, domin su a ganin su idan har yasamu mata hakan zai dawo masa da nutsuwar sa, duk da dai basu san musabbabin abinda yafaru ba amma sun san cewa akan mace yashiga wannan halin, tunda be da abin faɗa sai sunan ta

Be musa musu da auren ba tunda shima hankalin sa baya jikin sa, ahaka akayi auren Amarya Zubaida tatare a gidan auren ta, da daɗi babu daɗi haka tazauna dashi tunda dama ita tana matuƙar ƙaunar sa, haka rayuwa taci gaba da tafiya har komi yalafa ma Haris duk da har yanzu ƙaunar Halwa na ransa sai dai yanzu ya cire duk wani damuwa aran sa ya dawo daidai yaci gaba da aikin sa, sai dai yaƙi komawa Abuja acewar sa anan Katsina Yakamata yazauna yayi aikin sa koda Allah zai haɗa sa da Halwa, baya son ko kaɗan yayi nisa da garin duk da be san cewa tana nan ko bata nan ba

Haka shekara ɗaya da watanni yashuɗe Zubaida bata taɓa koda ɓari ba, gashi burin iyayen sa su samu jikoki masu yawa tunda shi kaɗai Allah yabasu, hakan sosai yaɗaga musu hankali har shi Haris ɗin don shima yana son ganin yaran sa, don haka suka soma ziyartan asibiti amma sakamako ya nuna lafiyan su ƙalau lokaci ne be yi ba

Ana cikin haka Mahaifiyar Haris tasake ce masa yayi aure domin ita bata yarda matsalan ba daga wajen Zubaida yake ba, shi kuma Haris ko kaɗan baya ƙaunar tara mata da yawa don haka yabijire mata duk da kuwa ba wai yana son Zubaida bane amma suna zaune lafiya sosai sabida kyautata masa da take yi

An kai ruwa rana kafin Haris yayarda aka yi masa aure, don iyayen nasa duk sun goyi bayan ƙara auren nasa tunda suna son suga jikokin su nan kusa, duk da kuwa shekara biyu kenan da auren

Haris ya rigada ya sa aransa duk sanda yahaɗu da Halwa idan har zata aure sa to tabbas sai ya rabu da duk matan nasa tunda shi a tsarin sa mace daya yake so, sosai yaji daɗin cikin da tatafi dashi, kuma hakan yasa ya gane cewa shi ɗin yana haihuwa Allah ne be kawo ba, bashi da buri a yanzu illa yaga abinda tahaifa masa, ƙaunar ɗan nasa da be taɓa gani ba tuni ya shiga ransa sosai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button