BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

Kallon Yaron Halwa tayi wanda yake lulluɓe da kayan sanyi hannun Larai ta ƙanƙame shi, numfashi taja kafin ta kawar da kanta tace
“Bazan iya shayar dashi ba, sai dai ki kai ma Saleema shi domin yaron ta ne”.
“Ban gane ba me kike nufi?” Larai tafaɗa a matuƙar ɗaurewar kai, dama tunda tazo take neman wanda zai amsa mata tambayoyin ta da suke cin ta arai bata samu ba, sosai tayi mamaki da aka ce Halwa ta haihu, bare kuma da taga yaron sak irin Khalil, kawai sai taɗaura wa zuciyar ta zargin cewa wannan yaron tabbas na Khalil ne, amma yanzu kuma zancen na son Shan banban..
Bata kai ga sake magana ba taji muryan Ummi tana faɗin
“Larai ki bashi ruwa don Allah ki lallaɓa sa yakoma barci”.
“To Hajiya”. Larai ta’amsa mata cike da ƙullewar kai, sai dai babu yanda zata yi tasake wani tambayan tunda ba’a bata dama ba
Ruwan taba ma yaron sannan taci gaba da lallaɓa sa yana ta ƙananun kukan sa
Halwa kuwa juya bayan ta tayi tarufe idanun ta kamar me barci, amma ina tunani ne fal a ranta na abinda yafaru a yau ɗin, hawaye tasoma zirarar wa tuna yanda taga Khalil ya faɗi ƙasa baya numfashi, take zuciyarta ta wani irin bugawa lokaci ɗaya ta zabura tana ɓarke wa da kuka.
[12/13/2020, 1:09 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Eighteen*
________???? Lokacin Ummi taci gaba da sallan ta, sai Larai ne tayi mata magana
“Halwa wai lafiya kukan me kike yi?”
Shiru Halwa tayi taci gaba da zubar da hawaye tare da haɗiye kukan nata
Larai ajiye yaron tayi lokacin yayi barci sai takoma shimfiɗar ta takwanta, babu jimawa kuwa barci yaɗauke ta, to bata san dai ya aka ƙare ba sai washe gari da suka tashi da safe
Lokacin yaron sai ɓaɓɓaka kuka yake yi amma Ummi na gani bata ce Halwa taba shi Nono ba, sai ma ɗaukar sa da tayi tana rarrashin sa, sannan takalli Larai da tasaki baki tana kallon su
“Yauwa Larai ke nake ta jira, don Allah kije yanzu ki amso min madaran sa wajen Sister A’ishah, naji ta shiru bata kawo min ba gashi kuma yana ta kuka”.
Larai tace “to”.
Sannan tanufi ƙofa tafice
“Itama kuma a lokacin Halwa ta gama cire kayan ta ta ɗaura zani tanufi Toilet don yin wanka
“Halwa kiyi wankan nan da kyau don Allah, yanzu zan zo idan Larai ta dawo sai in taimaka miki”.
Gyaɗa kanta tayi tabuɗe Toilet tashige batare da ta furta komi ba.
Lokacin dasu Abba suka shigo asibitin a time ɗin ne kuma ƴan sanda suka zo, don haka basu shigo ɗakin ba sai da suka gama da Police ɗin, sun zo yin bincike akan harbin Khalil da aka yi
Bayan duk sun yi abinda yadace sai Dad dasu Brr. Tahir suka bi su can Station ɗin kamar yanda suka buƙata
Abba ne kaɗai yashigo ɗakin
Halwa na zaune saman gado tana shan tea, sai Ummi dake zaune kan kujera riƙe da jaririn tana sake bashi madara
Sallaman Abba ne yasaka duk suka ɗago kai suna kallon sa sannan suka amsa
Shigowa yayi ciki yana kallon Ummi fuskar sa da tsananin mamaki
“Ina kwana Abba”. Halwa tafaɗa kanta a ƙasa
“Lafiya lau ƴa ta ya jikin naki?”
“Alhmadulillah”.
“Masha Allah haka ake so Allah yaƙara lafiya”.
A laɓɓa ta amsa masa da “ameen”.
Ummi ma gaishe sa tayi tana goge ma Yaron baki wanda duk ya ɓaci da madara
Abba kallon Yaron yasake yi sannan kuma yamaida idanun sa kan Ummi yace “ya naga kina bashi wannan abun bayan ga mahaifiyar sa? Meyasaka baza’a shayar dashi ba?”
Shiru Ummi tayi bata bashi amsa ba
Yayinda itama Halwa tasake duƙar da kanta ƙasa tana sauraron Abban
“Ɗiya ta me yafaru da baki shayar dashi ba ake basa madara?”
Ummi ce tayi magana
“Abban Saleema akwai abinda nake son faɗa maka dama, amma kuma na bari ne sai mun samu nutsuwa, Halwa baza ta shayar da yaron ba sabida ta ba ma Saleema ne, kuma gashi ita bata da lafiya bare ta shayar dashi”.
Idanuwa Abba yafid do waje yace “ban gane ba me kike nufi?”
Shiru Ummi tayi ta rasa ma me zata ce
Abba kallon ta kawai yake yi na wani lokacin kafin yajuya yafice
Ajiyan zuciya Ummi tasaki
Lokacin ne kuma su Mom suka yi sallama ita da Nazeefa suka shigo
Amsa musu Ummi tayi tana kallon su
“Sannu da zuwa Hajiya”.
Murmushi Mom tayi tana aza idanun ta kan Halwa kafin ta’amsa, sannan suka gaisa a mutunce kafin tatambayi lafiyan me jiki
Ummi tace “alhmadulillah ga ta nan jiki ya wartsake”.
“Allah yaƙara lafiya”.
“Ameen ameen, ya shima Khalil ɗin?” Ummi tatambaya
Numfashi Mom taja kafin ta’amshi Yaron tana cewa “to dasauƙi dai za’a ce, Allah yarufa asiri gaba ɗaya yakuma basu lafiya gaba ɗaya”.
“Ina kwana Momy”. Halwa tafaɗa tana ajiye cup ɗin hannun ta
Da fara’a Mom ta’amsa mata tana ƙara wa da
“Ya jikin naki?”
“Da sauƙi”.
Mom tace “to Allah yasawaƙe yaƙara muku lafiya”.
Nazeefa ma sai a lokacin ta gaishe da Ummi
Itama ta’amsa cikin fara’a tana tambayan ta School ɗin ta
Daga nan shiru ne yagibta a tsakanin su
Nazeefa ita dai idanu kaɗai tazuba ma Halwa tana faman kallon ta, jiya da ita takwana a ranta, musamman yanda aka ce ita ce Maman yaron nan me kama da Khalil, duk da dai bata taɓa ganin ta ba amma a fahimtan ta tasan cewa itace ƴar uwan Saleema wacce take zaune da ita, har yanzu mamaki yaƙi barin ranta yanda aka yi yaron ta yake kama da Khalil, sannan kuma ita ba aure ne da ita ba, kuma har yanzu taƙi yarda da zuciyar ta akan cewa Khalil zai iya aikata mummunan wannan zunubin da ranta ke kitsa mata
Itama Mom yaron kawai tazuba ma idanu tana kallo, ta rigada ta yarda a ranta tabbas yaron Khalil ne wannan, sai dai bata so tayi maganar ne yanzu sai idan hankalin kowa ya kwanta duk da kuwa zuciyar ta a matse take da son sanin gaskiya
Tabbas ba’a shedan ɗan yau, bata taɓa tunanin Khalil zai iya aikata mummunan aiki irin wannan ba, a jiya tayi kuka sosai akan wannan al’amarin, har abun ma yafi tada mata hankali a bisa ciwon Khalil ɗin, yanzu tana ji tana gani an haifa mata jika shege
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Tafaɗa a ranta tana ɗauke idanun ta kan yaron zuciyar ta cike da ƙunci
Numfashi taja kafin tamiƙa ma Ummi yaron tana faɗin
“Bari muje, dama zan koma gida ne sai anjima in dawo”.
Amsar yaron Ummi tayi sannan tace “to Hajiya sai kin dawo”.
Sallama suka yi daga nan suka fice ita da Nazeefa.
*****
Da yamma aka sallami Halwa kasancewar yanzu babu wata matsala dake damun ta, lokacin da zasu tafi Abba ya zo don haka shine yace su haɗo kayan su yakaisu
Halwa ta so taje duba jikin Khalil da Saleema amma babu hali, gashi har a lokacin ba’a basu damar sake ganin Saleeman ba
Lokacin da suka isa gida Halwa tawuce ɗakin ta kai tsaye, tana shiga ta’ajiye Yaron saman gado sannan tazauna tana riƙe kanta dake faman sara mata sakamakon kukan da tasha daga jiya zuwa yau