BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

Husna ce tashigo ɗakin kasancewar ƙofan a buɗe yake, gaba ɗaya jikin ta da kayan ta ta ɓata shi da garin Flower, har ta a fuskarta zuwa gashin kanta dake ɗaure da Ribom duk Flower ne

Tunda tashigo Halwa take bin ta da kallo batare da ta motsa daga inda take ba

Ita kuma Direct wajen Halwan tanufo tana yarfe hannayen ta tana faɗin

“Mammaaa..”

Tana washe baki da ƙananun haƙoran ta guda shida da tamallaka

Gaban Halwan ta’isa tana miƙa mata hannu alamun ta ɗauke ta

Ita kuma ta zuba mata idanu wanda a baɗini tunani take yi don hankalin ta baya wajen Husnan

Ganin dai ba ɗaukan ta zata yi ba sai tajuya tafice tana sake kiran

“Mammaaa..”

Fitowar ta yayi dai-dai da fitowar Larai daga ɗaki tana kallon ta tazaro idanu tare da nufo ta tana cewa

“Ke.. ke.. ke haka kikai ma jikin ki wannan ɓarnan? Kai Husna ba kya ji yanzu ji be yanda kika ɓata jikin ki, da alamu dai kin zubar min da flowern nan?”

Ɓangale baki Husna tayi tana ƙyalƙyale mata da dariya

Ɗaukan ta Larai tayi tace “mu je in sauya miki kayan tunda kin ɓata”.

Ɗan ƙaramin hannun nata taɗaura saman fuskar Larai ta damalmala mata da flowern da yaɓata mata hannu

Ita kuma Larai sai tacafko hannun tasaka a baki tana dariya

Still Husna ƙyalƙyace wa tayi da dariya tana janye hannayen ta

“Ƙaniyar ki, yarinya sai rashin jin tsiya, ke ko muje in sauya miki kayan inga kuma kin sake ɓata wa”.

Daga haka tashige cikin ɗakin ta da Husnan a hannu tana mangare mata ƙeya.

Halwa na zaune a inda take har yanzu tasoma jiyo hayaniyan Abba da Ummi, abinda bata taɓa ji ba tun zuwan ta gidan, hakan yasa sosai tayi mamaki tayi shiru tana kasa kunne don jin abinda ke faruwa

Izuwa yanzu muryan Abba ake jiyo wa sosai yana ɗaga murya, duk da kuwa ba ta fahimtan abinda yake cewa amma tasan faɗa yake ma Ummi

Bata motsa a wajen ba sai da taji hayaniyan ya lafa sannan tamiƙe tafito, lokacin tahangi Abba har ya buɗe ƙofa ya fice

Ɗakin Ummin tanufa don jin abinda ke faruwa, duk da kuwa wani sashi na zuciyarta na kawo mata musabbabin faɗan, be wuce sanin gaskiyan samuwar jaririn nan ba.

[12/13/2020, 3:37 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

_wannan shafin naku ne wattapad fans kusha sha’anin ku, Nagode da soyayyar ku gare ni❤️_

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Nineteen*

________???? Nocking tayi tare da sallama, bata shiga ba sai da Ummi taba ta izni bayan ta amsa sallaman nata

Tura ƙofan tayi tashige tana kallon Ummin dake zaune gefen gado, kallo ɗaya tayi mata tahango tarin damuwa a fuskarta, wanda kowa yakalle ta ya san tayi kuka

“Lafiya Halwa?” Ummi tayi maganar tana sakar mata murmushi

Kanta tasauke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace “dama naji kamar hayaniya ne shine nazo duba ko lafiya”.

Still Murmushi Ummi tasaki tace “lafiya lau Halwa babu damuwa, yanzu ina yaron yake ne?”

“Yana ɗaki yana barci”.

“To kema Yakamata kije ki kwanta ki huta sabida kin san abinda likita yafaɗa kenan”.

Murmushi Halwa tayi kafin tagyaɗa mata kai tajuya tafice, ɗakin takoma tayi kamar yanda Ummin tace don dama barci sosai take ji, ga jikin ta duk babu daɗi.

       *****

    Fitan Abba babu inda yazarce sai asibiti, kasancewar sun yi waya da Dad ya tambaye sa inda yake zai zo su tattauna wani matsala

Dad ɗin sai da yace masa shi yabari yazo yasame shi har gida, but Abban yaƙi hakan

Lokacin da ya’isa waya yaɗauka yakira Dad yafito suka shiga mota suka zauna, sun daɗe sosai suna tattaunawa kafin Dad yafito ranshi duk a ɓace, duk da kuwa cewa sai da suka tsayar da mafita akan zancen kafin yafito, amma ɓacin ran da yake ji akan maganar ya gaza gushewa

Cikin Hospital ɗin yakoma

Shi kuma Abba yaja motar sa yatafi.

       Yana shiga ɗakin Mom da Sameer dake zaune suna taɓa hira suka kallo sa, ganin yanda fuskar sa yake a matuƙar ɗaure sai abun yabasu mamaki

“Lafiya dai Alhaji meke faruwa?” Mom tatambaye sa har alokacin tana kallon sa

Numfashi yaja kafin yasauke idanun sa kan Khalil, kamar yana jin sa cikin ɓacin rai yace “zaka tashi dan ƙaniyar ka zaka gaya min abinda yasaka ka aikata ma ƴar mutane hakan”.

Ƙirjin Mom ne yabuga da ƙarfi, cikin ruɗu tace “Alhaji kana nufin shine yay ma Halwa ciki?”

Girgiza kan sa yayi cikin takaici yazauna yana faɗin “yo ai ban ga banbancin abunda suka yi mata ba da cikin, wai ƙwanyin haihuwar su shi da matar sa aka saka mata don ta haifa musu ɗa”.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Cewar Mom cike da tsananin al’ajabi

Sameer kam kasa magana yayi sai mayar da idanun sa kan Khalil ɗin da yayi yana kallon sa, be san cewa ɗan uwan nasa har yanzu be da wayau ba sai yau

“Menene hakan kenan?” Wai yanzu kana nufin ɗan su ne Halwa ta rainan musu?”

Dad yace “wlh raina yayi mugun ɓaci da Alh. Mustapha yafaɗa min, amma dole zan ɗau mataki bari yafarka zai gane be da wayau”.

Daga haka yamiƙe yafice yabar su nan shiru suna mamakin wannan abinda Khalil ya aikata, abun ma yay musu girma da yawa don haka basu sake yin magana ba har sanda Atine me aikin Mom tazo, sai Sameer yatashi yay ma Mom sallama yatafi akan sai gobe zai dawo sabida yau yana da dutyn dare.

         ******

Washe gari da yamma Khalil yafarka

Mom CE lokacin ita kaɗai a wajen sa, doctor takira yaduba sa sai da yatabbatar babu matsala sannan yatafi

Tea tahaɗa masa me kauri kamar yanda doctor ɗin yabuƙaci aba shi wani abun yaci, sai da tagama haɗa wa kafin tamiƙo masa Cup ɗin tace

“Ga shi ka daure kasha ko zaka ji daɗin jikin ka”.

Numfashi yaja kafin yasoma yunƙurin dai-dai ta zaman sa, yana yi yana cije baki

Hakan yasa Mom ɗin ajiye Cup ɗin hannun ta, tamiƙe tataimaka masa yazauna tare da jingina da pilow

A hankali cikin sanyin murya na maras lafiya yace “zan wanke baki”.

Vowel ta ɗauko sannan taɗauko ruwan gora ta buɗe ta kafa masa a baki

Yakurɓa yakuskure bakin sa yazuba cikin Vowel ɗin

Sannan ta’ajiye tamiƙo masa Cup ɗin ya’amsa yafara sha

Yana sha yana rufe idanun sa har ya ɗan sha rabi tukun yamiƙa mata Cup ɗin, a karo na biyu tun tashin sa yasake magana

“Mom Ina Saleema?”

Ita kawai tafaɗo masa a rai saboda yasan dole zata shiga wani hali da abinda yafaru dashi

Amsar da taba shi shiyasaka shi ɗaura idanun sa akan ta, be iya yin magana ba illa kallon ta kawai da yake yi

Har maganar haihuwar Halwa sai da tayi masa duk da kuwa bata nuna masa tasan ainihin zancen ba

Ɗan waro idanu yayi still yana kallon ta zuciyar sa na bugawa da tsananin ƙarfi

Ganin kallon da yake mata ba ƙaƙƙauta wa tace “lafiya ko akwai wani abu ne?”

Lumshe idanun sa yayi yana kwantar da kansa, be sake yin magana ba duk da kuwa Mom ɗin tana ta yin masa hira

Har sanda su Hakima da Nazeefa da suka zo a tare be sa ya buɗe idanun sa ba, iyakan gaisuwar su ya’amsa yasake juya bayan sa tare da ci gaba da tunanin sa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button