BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

Hakima na ta tsokanar sa but be ma san tana yi ba.

      Har dare suna nan zaune, sai da Sameer yazo sannan suka tarkata har da Mom drever yakai su gida, Sameer ne zai kwana dashi a yanda suka tsara tunda ya tashi

Tun fitan su Sameer ɗin yake tsaye bakin ƙofa yana yin waya, sai da yagama kafin yazo yazauna yana kallon Khalil da idanun sa suke rufe kamar yanda yake tun ɗazu

“Khalil wai su wanene kake zargi akan wannan abun da akai maka?”

Sai a lokacin yabuɗe idanun sa yana kallon Sameer ɗin, sai kuma ya yamutsa face ɗin sa sabida zugin da yake ji a ciwon sa, kamar bazai yi magana ba har Sameer ya buɗe baki da ninyan sake yin masa magana sai kuma yace

“Bana zargin kowa”.

Jinjina kai Sameer yayi yace “su ma har yanzu ƴan sanda sun kasa samun wani ƙwaƙƙwaran shaida wanda zai sa agane me hannu ciki, wannan aikin naka yana da maƙiya da yawa matuƙa hakan yasa baza mu iya gane wanda yake da hannu ba, sai dai Allah yaƙara tsare wa, but insha Allahu ko ma wanene sai asirin sa ya tonu”.

Khalil dai yana jin sa be tanka ba, har sanda yasauya maganar da faɗin

“Ni ban taɓa tunanin baka da hankali ba sai yanzu Khalil, wani wauta ne zai saka kayi wannan gangancin, kana tunanin wannan shine maslaha da zaku cutar da ƴar mutane? Haramun ne hakan a musulunci but har da kai aka haɗa baki wajen aikata wa, ka bani mamaki wlh”.

A yanzu Khalil ya maida idanun sa kan Sameer ɗin yana kallon sa, sai dai be iya yin magana ba

 “Yanzu kowa yasan cewa Halwa ta haifa mana ɗa?” Yatambayi kansa batare da yasan afili yayi maganar ba

Hannu Sameer yasaka yadungure masa kai yace “baza ka san kowa ya sani ba sai ka haɗu da Dad, wlh zaka sha mamakin sa domin yayi fushi sosai, meyasaka zaka biye ma yarinya don kawai bata haihuwa ku cutar da Halwa..”

“Ni fa ba Ni ne na bada shawaran hakan ba, itama ɗin ai har da yardan ta tunda ba mu mukai mata tilas ba”. Khalil yakatse sa da faɗin hakan yana turo baki

“To tunda har da yardan ta kai kuma babban banza ko sai ka amince?”

Marairaice fuska Khalil yayi kamar zai yi kuka yace “Bro wlh tausayin Saleema yasaka na amince da wannan shawaran da Ummi takawo, kuma wlh ban tashi dana sani ba sai daga baya, Ni kaina na so azubar da cikin sai dai kuma hakan ba me yiwuwa bane tunda Matata ta ƙwallafa ran ta akai”.

Sameer yace “kana nufin kenan da Ummi cikin zancen?”

“Eh”. Yaba shi amsa yana sake langaɓe kai

Taɓe baki Sameer yayi yace “zaka sani ne babu ruwana Ni dai”.

Ɓata fuska Khalil yayi be sake yin magana ba, sai kuma yasaki ajiyan zuciya jin Sameer ɗin shima be ce komi ba yakalle sa yace “Brother taimaka min zan yi sallah”.

Tashi Sameer ɗin yayi yazare masa ƙarin ruwan da aka saka masa sannan yataimaka masa yamiƙe tsaye

“Kayi a hankali kar ka zuba ma wajen ruwa”. Sameer yafaɗa yana koma wa yazauna

Be ce komi ba yataka a hankali yashige toilet ɗin, be wani jima ba yafito

A lokacin Sameer ɗin yamiƙe yashimfiɗa masa sallaya yasoma gabatar da sallan da ake bin sa bayan ya tambaye sa kwanakin da yayi a kwance

Sai da yagama sannan yakoma kan gadon yakwanta bayan Sameer ya mayar masa da ruwan, rufe idanun sa yayi yana sauke tagwayen ajiyan zuciya, be sake motsawa ba har sanda barci yaɗauke sa cikin ƙanƙanin lokaci.

    **** ***** ***** *****

*BAYAN KWANA BIYU*

Alhmadulillah jikin Khalil yana ta samun sauƙi, har a lokacin ana ta binciken waɗanda sukay mishi hakan but ba’a samo su ba

Gwamna da kansa yasaka ayi bincike sosai don gano su, duk da kuwa har yanzu an kasa samo shaida ko guda ɗaya, Asibitin babu CCTV ???? cameras Wanda zai sa ayi saurin gano su, amma duk da haka an zuba jami’an tsaro a Hospital ɗin don tsaron Khalil ɗin, suna da tabbaci waɗanda sukai yunkurin wannan aikin suna da ninyan kashe sa ne zasu iya dawowa at any time.

    Fannin Saleema dai babu abinda yaci gaba tana nan a yanda take, su Ummi sai dai su zo ganin ta tunda har yanzu ba’a barin kowa yashiga inda take kwance, ta Glasses kamar yanda suka saba suke ganin ta sannan su koma gida, idan nace muku hankalin iyayen ta yana kwance nayi ƙarya, sosai suke cikin damuwa da halin da ɗiyar su take ciki, ita ba matacciya ba ita kuma ba rayayyiya ba.

Kamar yanda Dad yabuƙaci ganin su a yau saboda tattauna matsalan su Khalil ɗin gaba ɗaya, yau ne suka taru a gidan Dad ɗin, har da Halwa aka zo da ita sai aka bar yaron wajen Larai

Bayan sun hallara gaba ɗaya, Ummi Abba Halwa Dad da Mom sannan sai Sameer aka buɗe taro da addu’a

Dad ne yasoma magana da faɗin “Asma’u abinda kuka aikata hakan be mana daɗi ba, ko kaɗan bamu ji daɗin hakan ba domin wannan ba koyarwa ne ta addinin musulunci ba, shiyasa muka zauna don samun mafita kamar yanda muka yanke hukunci Ni da Alh. Mustapha, wannan yarinya dai an cuce ta matuƙa saboda da agaban iyayen ta take hakan zai jawo mana matsala, sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba tunda wannan yarigada ya faru”.

Sai ya ɗan ja numfashi kafin yaci gaba

“Sai dai ku gafarce Ni sabida hukuncin dana yanke daga baya, na cewar Ibrahim ɗin zai auri ita Halwan sai su zauna gaba ɗaya domin hakan shine yafi dace wa”.

Gyaɗa kai kawai Abba yake yi kafin yace “wannan shine daidai domin nima da tunanin hakan a raina, ai ko ba’a haɗa su aure ba babu yanda za’a yi Khalil yazauna da Saleema ita kaɗai dole zai ƙara aure, tunda ba zai zauna haka nan babu yara ba”.

Ummi kanta bata ji haushin wannan abun ba, sabida tasan dole ne Khalil yasake aure nan gaba, to abun farin cikin su ne tunda Halwa ce zata zama kishiyar ƴar su, ta tabbata baza ta taɓa cuta mata ba

Itama Mom ta nuna goyon bayan ta tare da farin cikin ta sosai duk da har a yanzu bata san ainihin wacece Halwa ba, but shi Dad ya sani tunda sai da Abba yafaɗa masa komi da wannan maganar tafito

Halwa kuwa tunda aka soma maganar kanta na ƙasa, ta shiga matsananciyar faɗuwar gaba jin cewa za’a haɗa ta aure da Khalil, sai dai bata iya nuna musu wani hali take ciki ba duk da kuwa cewa taji sanyi aranta ganin Iyayen Saleema basu nuna rashin amincewar su ba, har aka gama tattaunawan bata ɗago kai ba kuma su ma basu tambaye ta jin ra’ayin ta ba, shiyasa itama bata furta komi ba

Da zasu tafi Ummi ce tayi mata maganar tatashi, don haka tamiƙe suka fito sukai gida.

.

_To pa Kuna ganin hakan babu matsala?_

[12/13/2020, 6:17 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Twenty*

________???? An tsai da ranan auren nan da kwana huɗu masu zuwa ranan juma’a kenan

Kuma duk wannan abun da ake yi babu sanin Khalil, Dad ne yace kar a faɗa masa a bari sai ranan ɗaurin aure

Don haka Sameer da Brr. Tahir ne suke ta shirye-shiryen bikin, wanda yadace su gayyata sun gayyace shi duk da ba wai taron biki za’a yi sosai ba, kuma duk wani gyara na gidan sa su ne kan gaba akai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button