BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

Abba ya haɗa mata duk wani kayan ɗaki da Yakamata ayi mata, shiyasa da aka kai kayan gidan sai su Sameer suka kwashe kayan Khalil ɗin dake ɗakin sa suka zuba nata, sai suka bar masa abubuwan da zai iya buƙata, amma gadon sa dasu sip ɗin sa duk an sauya dana Halwa
Ummi bata yi ƙyashin gyara Halwa ba duk da kuwa lokaci yazo a ƙure kuma gashi tana cikin jego, but duk wani abinda yakamata tayi mata
Halwa dai bata iya mata musu duk abinda tasaka ta tana yi, ko kaɗan bata damuwa da kanta wai ko tana son sa ko bata son sa, ita kawai Saleema ce a ranta, me zai faru idan har tasan cewa ta aurar mata miji? Hakan na ɗaga mata hankali matuƙa har tashiga ɗaki tayi ta kuka, tana jin cewa bata kyauta ba kuma sannan ita butulu ce, ta ɗau alwashi da dama aranta wanda babu wanda yasan hakan sai ita kanta.
Fannin su Mom sun haɗo akwati guda biyar maƙare da kaya, komi sai son barka, duk da a ƙurarren lokaci aka yi komi amma kasancewar da kuɗi komi ya tafi yanda suke so.
Ranan Friday Dad da kansa yakai ma Khalil kayan da zai saka, sun matsa sai da aka sallame shi a ranan saboda jikin da sauƙi sosai domin har riga yake iya saka wa
Khalil yayi mamaki sosai yanda aka bashi sabbin kaya yasaka, sannan kuma har yau yana fargaban Dad da be mishi maganar jaririn sa ba kamar yadda Sameer yafaɗa masa zasu haɗu ne, saka kayan yayi su Sameer ɗin sai tsokanar sa suke yi
Su ma a lokacin suna cikin ɗakin sun sha sabbin kaya iri ɗaya har Dad, sai dai shi nashi har da malin-malin, abun ya ɗaure ma Khalil kai amma be yi magana ba bare yatambaye su
Haka suka fito suka kwashe komi nasu suka hau mota sukai gida
A ƙofar gidan mutane ne sosai ƴan ɗaurin aure duk da ba wani gayya sukai ba, su ma su Dad basu shiga ciki ba sai suka fito suka nufi masallacin ƙofar gidan
Khalil na biye dasu yana ta mamaki, musamman da yaga wasu daga cikin abokan aikin sa, sai kuma yanda ake bashi hannu ana gaisawa dashi suna kiran sa Ango, sai abun yasake ɗaure masa kai, kallon Brr. Tahir dake kusa dashi yayi yace
“Wai meke faruwa ne?”
Dariya Brr. Tahir yayi yace “su Daddy aure zasu yi maka shine abinda ke faruwa”.
“Auree”. Khalil yafaɗa da tsananin mamaki wanda lokaci ɗaya gaban sa yay mugun faɗuwa
Aure kuma? Shi ɗin ne za’a yi ma aure? Mamaki al’ajabi da suka cika sa shine yakasa sake yin magana bare kuma yasake tambayan wani abun
Suna shiga Masallaci bayan sun zazzauna yana ji yana gani aka ɗaura masa aure tunda abun yafi ƙarfin tunanin sa, har fa alokacin mamaki yake yi wanda ya kasa yarda cewa maganar Brr. Tahir gaskiya ne
Amma jin sunan wacce tazame masa mata a yau ɗin sai lokaci ɗaya yayarda da cewa tabbas shine akayi ma aure, shirun da Dad yayi masa yana nufin zai aura masa Halwa ne
Baza ka taɓa sanin wani hali Khalil yashiga ba domin gaba ɗaya jin sa da ganin sa tare da tunanin sa sun tsaya cakk, be san ya aka ƙare a wajen ba, shi dai yasan Brr. Tahir ya riƙo sa sun fito taron jama’a sannan sun shiga cikin gida, ɗakin su dake gidan a nan yanufa dashi, tunda ya’ajiye sa saman gado yazame yakwanta yarufe idanun sa be sake motsawa ba
Shi kansa Brr. Tahir ya shiga damuwa ganin yanda Khalil ɗin yakoma, gashi mutane suna ta shigowa suna masa magana amma tamkar gunki haka yakoma musu, baya magana baya kuma jin su.
*****
Fannin Amarya ma hakan take, baza ka taɓa gane wani irin hali take ciki ba, ko kaɗan bata murna da wannan ranan, ita dai kawai tana yin duk abinda aka saka ta ne, har dare ba ta iya cewa uffan sai dai tabi mutane da idanu
Kuma duk a yau ɗin ne akayi sunan jaririn da yaci suna Ahmad, zai ci gaba da zama wajen Ummi ne har sanda Saleema zata samu lafiya.
Brr. Tahir ne aka wakilta wanda zai ɗauko Halwa yakai ta gida ita kaɗai, don haka lokacin da yazo har an saka ta sake yin wanka ta shirya cikin Swiss less milk colour, duk da kasancewar ta baƙa kayan yayi mata kyau sosai, bare kuma yanzu da tasake haske sosai skin ɗin ta yasake fresh
Ummi ita da kanta taraka ta har mota tabuɗe mata tashiga
Halwa bata yi kuka ba iyakan dai tunda taɓoye kanta a gyalen ta bata sake motsa wa ba
Brr. Tahir yana ta tsokanar ta yana jan ta da hira amma shiru tayi masa tana sauraron sa, har sanda suka kai yaraka ta har ciki sannan yanuna mata ɗakin Khalil a matsayin nan ne ɗakin ta, shiga tayi shi kuma yafice a gidan gaba ɗaya
Ɗakin tabuɗe tashiga a hankali, daddaɗan ƙamshin turaren sa ne yay mata maraba cikin hanci, sai taja gauran numfashi tana sake buɗe ƙofofin hancin nata don sake shaƙa, sosai take jindaɗin ƙamshin shiyasa koda yaushe burin ta kawai tashaƙa a hanicin ta, sauke gyalen daga kanta tayi tana ƙare ma ɗakin kallo, bata taɓa shigowa ba sai a yau ɗin
Sai da tadaɗe a tsaye anan tana kallon ɗakin kafin tataka tanufi gaban gadon tahaye takwanta
Allah babu yanda baya tsara lamarin sa, Wai yau ita ce aka kawo gidan nan a matsayin matar gidan, tabbas yau tana cikin wani yanayin da babu me gane wa sai ita kaɗai
*****
Khalil kuwa yana can gida su Dad sun saka sa gaba suna mishi nasiha, duk da basu san menene a ransa ba amma sun gane baya cikin nutsuwan sa ko kaɗan, sosai yake tattare da damuwa, kuma sun san cewa dole ne zai shiga wani yanayi tunda tamkar auren dole sukai mishi a ganin su
Bayan sun gama mishi nasiha yafito Drever yatuƙo sa zuwa gida batare da yayi tunanin wai yasiyo abubuwan da ake tarban Amarya ba.
Halwa na kwance taji ƙarar buɗe gate da rufe wa, bayan wajen minti 5 kuma taji an buɗo ƙofan ɗakin an shigo, a yanzu tarigada ta ƙudundune kanta cikin gyalen sai dai tana kallon inuwar sa har sanda yasoma takowa yanufo wajen gadon
Tun sanda yashigo idanun sa suka faɗa kanta, don haka yanufi wajen gadon yatsaya ƙerere yana faman kallon ta, ya saka hannun sa ɗaya cikin aljihun wandon sa
Gaban Halwa sosai yake faɗuwa jin sa a bakin gadon, rufe idanuwan ta ruf tayi tana sauraron bugun zuciyar ta da kuma abinda zai biyo baya
Leɓen bakin sa na ƙasa yacije da ƙarfi yana sakin huci, sai yajuya yanufi Toilet, wanka yayi yafito har lokacin Halwa bata motsa ba duk da kuwa tasan baya wajen
Wajen Sip yanufa yabuɗe, yamutsa fuskar sa yayi ganin babu komi a wajen, sai yanzu ma yasake ƙare ma ɗakin kallo yatabbatar an sauya masa kayan ɗaki
Be ce komi ba yasake buɗe ɗaya side ɗin anan ne yaga kayan nasa, jallabiya yazaƙulo tare da gajeren wando yakoma cikin Toilet yasaka, sai da yagama yafito yanufi ƙofa yafice, ɗakin Saleema yashiga yakwanta saman gadon ta
Rufe idanuwan sa yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, bazai ce baya farin ciki ba a yau, sai dai abinda yasani a game da ita shine ya jagula masa duk wani buri na ransa, taya zai iya zama da mazinaciya a matsayin matar sa? Har yau yana matuƙar ƙaunar ta aransa domin kuwa ji yake yi tamkar ana ƙara masa wutan ƙaunar ta, sai dai duk sanda yatuna Halwa tayi rayuwan ƙasƙanci har da rabon ɗiya hakan na mugun ɓata masa rai, kuma ba komi yajanyo hakan ba sai tsananin kishin ta da yake yi, duk sanda yaganta sai zuciyar sa tariƙa raya masa rayuwan da tayi da ƙattin banza, shi a ganin sa tunda har ta iya haifar yarinya tabbas ita ɗin ba ƙaramar tantiriyar karuwa bace, maybe yanzu ta tuba ne shine tadawo gidan su Saleema tazauna