BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

Ɗaukan Aamir yayi yana bata amsa da “A ƙoshe nake ai, bari mu fita waje”.
Tunda yafice kuma sai sukai ta hira da Saleema.
*****
Lokacin da suka dawo tare da Sameer suka shigo gidan
Khalil nan yace “Saleema tatashi su tafi”.
Hakima sai tsiya take mishi wai yanzu suka zo har zasu tafi baza su kai musu dare ba
Shi kuwa be ce komi ba
Saleeman ce take ta dariya tana faɗin “zasu biya ɗauko Halwa ne”.
Sannan ne fa Hakima tayi shiru da bakin ta
Har waje suka rako su suka hau mota suka bar gidan
A lokacin ne Khalil yaƙyalla idanu yaga saƙon da Mom tabashi yaba Saleeman, shaf ya manta shiyasa yabar shi cikin motan, don haka ya ɗauka yamiƙa mata yana faɗin
“Gashi in ji Mom ɗazu na manta ban Baki ba”.
Amsa tayi tana kallon ledan, sai kuma tabuɗe jaka tasaka tana cewa
“Allah Sarki Mom ɗina, Allah yasaka da alheri, zan kira ta in mata godiya”.
Shi dai be ce komi ba illa murza sitiyarin da yake yi, ahaka har suka shiga cikin makarantan
Saleema takira ta awaya tasanar da ita inda sukai parcking motan
Don haka babu ɓata lokaci Halwa tafito cikin holl ɗin da suka gama karatu ta tunkari inda zata same su, tana sanye da niƙab da tasaka yanzu da zata fito har ta’isa wajen motan tayi Nocking
Da farko da suka kalle ta basu gane ta ba, sai kuma Saleema tasaka dariya tana zuge glass ɗin tace
“Kaii sis Wai dama kina saka niƙab ne idan zaki zo?”
Murmushi Halwa tayi wanda basu san ma tana yi ba, idanun ta tasauke akan Khalil da shima yazuba mata nashi, tayi saurin lumshe wa tana buɗe su sannan tabuɗe bayan tashiga tana faɗin
“Saboda ƴan saka idanu ne shiyasa nake saka wa, sannu Yaya”.
Taƙarishe maganar tana rufo ƙofan
Jan motan yayi yana amsa mata da “yauwa, ya makarantan?”
“Alhmadulillah”. Tace ataƙaice
Saleema tace “gaskiya ne Sister kuma yayi miki kyau fa wlh”.
Cire niƙab ɗin Halwa tayi tana saka wa ajaka tace “ko Ƴar uwa?”
“Eh mana ki tambayi Yaya Khalil”.
Kallon gefen sa Halwa tayi sai suka haɗa idanu ta mirror, tayi saurin ɗauke kanta batare da tace uffan ba
Shi kam be ɗauke idanun sa akan ta ba, kallon fuskarta kawai yake yi, a ransa kuma sosai yaji daɗin ganin ta da niƙab ɗin
Saleema ce kaɗai take ta faman surutun ta Halwa na bata amsa a taƙaice
Har yanzu bata iya sakin jiki a gaban sa, sabida yanda take ji a game dashi duk da kuwa sun ɗan saba ba kamar da ba.
[12/2/2020, 3:13 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Twelve*
________???? Koda suka isa gida Halwa wanka tasoma yi tasauya kaya zuwa riga da skert na kanti me ruwan bula, sannan tafito tasami Saleema a kichen tana ɗaura musu abincin dare
Fita tayi tanufi kan dainning taɗibo abinci tasake dawowa cikin kichen ɗin tazauna akan Kujeran Robber dake ajiye gaban Freezer, Saleema na girki tana taya ta hira.
Khalil kuwa ɗakin sa yawuce kai tsaye, cire kayan jikin sa yayi yasauya da farar jallabiya da gajeren wando sannan yafito parlour, Kallo yakunna yaɗau Remote yana sauya Channels, ya saka wannan yasaka wancan har sanda Halwa tagama cin abincin tafito don taƙara wani
Tana fitowa suka haɗa ido dashi, ɗauke kai tayi tanufi kan dainning, tana cikin zuba abincin tatsinkayi muryan sa yana cewa
“Maman Husna kawo min ruwa”.
Lumshe idanun ta tayi tana sauraron bugun zuciyarta dake fita dasauri-sauri, ware idanun tayi kansa wanda shima yazuba mata nashi idanun, dasauri taɗauke kanta tana nufan Fridge tabuɗe taciro masa sannan tahaɗo da cup tanufo sa, akan Centre table ta’ajiye masa tajuya da ninyan tafiya, batayi aune ba sabida yanda duk natsuwar ta yabar jikin ta sai ji tayi tay karo da Centre table ɗin ta tafi yarab ta faɗa kansa, sai gata ɗare-ɗare a jikin sa
Kunya tsoro duk su suka taru mata lokaci ɗaya wanda hakan yasaka takasa tashi bare taɗago kai takalle sa, in banda gudun da zuciyarta ya ƙara kamar yafaso ƙirjin ta
Shi kuwa abin ma dariya yaba sa, haka kawai yatsinci kansa cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, sai kawai yazuba mata idanu yana murmushi me sauti
Lokacin ne kuma tasamu ƙwarin jikin da har ta’iya yunƙurin tashi, har a time ɗin bata iya kallon sa ba illa miƙe wa da tayi tana shirin barin wajen
“Maman Husna halan baki gani ne kike son ki karya Ni?” Yafaɗa still yana murmushi
Ɗago kai tayi takalle shi, sai kuma taɗauke kai tana murmushi bata iya cewa komi ba tanufi hanyan kichen dasauri
Tana shiga Saleema ta ɗan kallo ta kafin tamaida kanta taci gaba da aikin ta
Zama Halwa tayi tana sauke ajiyan zuciya har da dafe ƙirjin ta tare da lumshe idanu
“Me yafaru ne Sister wannan murmushi haka?” Tatsinkayi muryan Saleema tana faɗin hakan
Dasauri tabuɗe idanun ta suka haɗa ido da Saleema wacce tajuyo gaba ɗaya a yanzu tana kallon ta
“Babu komi”. Halwa taba ta amsa cike da sanyin muryan ta
Sai kuma tamiƙe tana nufo ta
“Da me zan taya ki?”
Saleema tace “ai na gama, sai dai ki kwashe min zuwa dainning”.
“Ok”.
Tare suka fito kichen ɗin har a lokacin kuma Khalil na zaune a Parlour yana kallon sa
Kallo ɗaya Halwa tayi masa taɗauke kai ganin sun haɗa idanu
Kan dainning ɗin suka kai suka jera, sannan Saleema tanufi parlour’n tazauna gefen sa
Halwa kuma sai tayi ɗakin ta dasauri
“Sis Ina Zaki kuma?”.
Halwa da har ta buɗe ƙofan zata shiga tatsinkayi muryan Saleeman, sai tajuyo tana kallon ta tace “kawai zan ɗan kwanta ne kafin a kira sallah”.
“Kwanciya kuma yanzu? Ki dawo ki zauna anan zuwa anjima kya shiga ki kwanta”.
Gaba ɗaya kallon sa suka yi wanda kamar ba shine yayi maganan ba, don hankalin sa na kan t.v yana sake sauya Channel
Takowa tayi tadawo tazauna can gefen su
Su biyu kaɗai suke hiran su yayinda Halwa tamaida hankalin ta kan t.v amma tana sauraron su, idan Saleema tasako ta kuma tana bata amsa, har sanda aka kira sallah Khalil yatashi yashige ɗakin sa
Su ma tashin suka yi don gabatar da farali.
****** ******** *******
Tunda Zainab tayanke shawaran fid da miji ko ta samu sauƙin nacin Nura hakan kuwa tayi, akwai wani saurayi Aliyu da suke makaranta tare, anguwan su ɗaya dashi sai dai ba layin su ɗaya ba, to shi yana degree ɗin sa ne a school ɗin, suna yawan haɗuwa a makarantan shiyasaka suke ɗan gaisawa har idan Zainab tana da assignment ko wani abinda bata gane ba kai tsaye wajen sa take zuwa, tunda dama sun san juna sosai a anguwan su magana ce kaɗai be haɗa su
Wannan dalilin ne yasaka shaƙuwa yasoma shiga tsakanin su, har dai Aliyu yazurma son ta lokaci ɗaya, ahankali-ahankali dai bayan shaƙuwar su ta sake nisa sai yasanar mata da sirrin zuciyar sa
Zainab bata wani ja aji ba ta amince don dama itama tana son sa aranta, komi nasa yayi mata, bare kuma dama neman saurayi take yi tayi aure ta huta.