BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

Aliyu na zuwa wajen ta, a school kuma koda yaushe suna tare hakan yaƙara ƙarfafa soyayyar su da shaƙuwar su, kuma a gidan su babu wanda be san Aliyu ba

Umma ko kaɗan hakan be mata daɗi ba tunda Aliyu ko ƙwaƙƙwaran sana’a bashi dashi, iyakan dai karatun sa yasaka agaba sai kuma ɗan jiran shago da yake yi, sosai ran Umma yasake ɓaci musamman da tasan ko shi wanene don haka tasoma rura ma Zainab wuta dole tarabu dashi takoma ma Nura tunda shi yana da sana’ar sa

Zainab ita kuma ta nuna mata sam ita Aliyu take ƙauna, hakan yajawo har sai da Umma tayi mata tsinannen duka

Ba ƙaramin ɓaci ran Abba yayi ba, a ranan shima sai da yayi kamar zai duke Umma akan abinda tayi, wannan dalilin ne yasaka yanemi Aliyu yabashi damar yaturo idan har zai iya auren Zainab

Duk da Aliyu be da wani abun yi sosai wanda ke kawo masa kuɗi, sai dai yana da ƴan uwa waɗanda ciki ɗaya suka fito su ne kuma suke taimaka masa a fannin karatun sa sabida suna da hali sosai, jiran shagon da yake yi yana yi ne kawai don rage zaman banza

Koda Abba yayi masa zancen yaturo hakan ya faranta masa, kai tsaye sai yanufi gidan Babban Yayan su yasanar masa, dayike su ma suna son yayi aure sai Yayan nasa yace “yatafi zai neme sa idan suka yi shawara da Umman su”.

A cikin sati ɗaya har an nema wa Aliyu auren Zainab kuma Abba ya basu ita, sai aka saka ranan nan da wata uku bayan ta gama final exams ɗin ta da sati biyu, dama ƴan uwan sa zasu yi masa komi na bikin don haka basu wani damu ba koda aka saka ranan babu yawa.

Fannin Nura kuwa yayi baƙin cikin hakan sosai, ya tabbata ya rasa Zainab bazai taɓa samun ta ba tunda yasan bata son sa, amma kuma har yanzu yaƙi ba ma zuciyar sa haƙuri be dena zuwa wajen ta ba. Sai mu ce Allah yakyauta maka.

.

_kuyi haƙuri da wannan babu yawa._

_sai kun ji Ni a next page._

_kar ku manta plz Vote and share ????_

[12/2/2020, 3:31 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Thirteen*

________???? *AFTER THREE MONTHS*

“Wai jikin ne Sister?” Halwa tafaɗa lokacin da take zama gefen gadon

Numfashi Saleema taja tana sake jan bargon da tarufe jikin ta dashi a lokaci ɗaya tana bata amsa

“Wlh kuwa sis, gaba ɗaya bana jin daɗi yau, dama tunda naga a kwana biyun nan jikina ya soma kumbura na san akwai matsala”.

Cike da tausayin ta Halwa tace “eyya ko dai in Kira Ya Khalil mu je asibiti, don bana son wlh ciwon ki yatashi da tsananin nan”.

Ɗan guntun murmushi Saleema tasaki tana kallon ta cike da nuna jarumta tace “kar ki damu babu abinda zai faru, bari dai insha magani na sai in kwanta in ɗan samu barci insha Allahu zan ji daɗi domin barcin nake buƙata a yanzu”.

“Tom bari in ɗauko miki Maganin”.

Dasauri tamiƙe tazagaya side ɗin gadon tabuɗe drower taɗauko mata, tanufi Fridge tahaɗo mata da ruwa sannan tadawo tazauna

“Tashi kisha”. Tayi maganar tana ajiye goran ruwan da maganin ajikin ta

Sai da tataimaka mata tatashi zaune kafin tabuɗe mata maganin taba ta tasha ta’ajiye ruwan a ƙasa

“Ki ɗan tsaya yanarke tukun sai ki kwanta”.

Murmushi Saleema tayi tace “to Nagode sis, Ina jin daɗin kula dani da kike yi Allah yabiya ki da mafifin cin alkhairin sa..”

“Ya isa don Allah duk abinda zan miki be kai kwatankwacin taimakon da kikai min ba, kar ki damu sister insha Allahu Allah zai yaye miki duk wani damuwar ki, Allah maji roƙon bawan sa ne kuma yana jin mu”.

Cikin jindaɗin maganar ta Saleema tace “Sister to ki je ki ƙarisa assignment ɗin naki mana ko kin gama ne?”

Gajeren tsaki Halwa taja tana shafa gefen fuskarta tace “wlh na kasa ƴar uwa, duk wani searching da zan yi ban samu abinda nake so ba, na dai ƙoƙarta nayi biyu a cikin biyar ɗin, kuma gashi Lecturer ɗin nan yace mana shine Test ɗin mu na rasa ya zan yi”.

Saleema tace “to ki kai ma Yaya Barrister mana zai taimaka miki, tun farko ma na manta wlh da shi kika kai ma wa”.

Halwa dai batace komi ba illa jinjina zancen da take yi aranta, ba wai kai mishin bane bata so kusancin su ne ko kaɗan bata so..

“Kin yi shiru Sister?” Saleema takatse mata tunanin ta

“To”. Kaɗai ta’amsa mata dashi kafin tamiƙe tanufi kan kujera taɗau Hijabin ta tana ƙoƙarin saka wa

“Wlh Sister ban taɓa ganin wanda ciki yake masa kyau ba kamar ke, Ni har na fi ganin kyan wannan cikin akan wancan, kinga yanda kika yi kuwa?” Cewar Saleema tana dariya ahankali

Itama Halwan dariyan tayi tana ƙarisa saka Hijabin sannan taɗau Peppers ɗin ta tana kallon Saleeman

“Ke dai Sister kin fiye saka idanu, ina wani kyau anan kina ganin yanda yaƙara min muni ya mayar dani sai kace wata uwa”.

Dariya suka yi gaba ɗaya kafin Halwa tafice

Ita kuma Saleema tagyara kwanciyar ta.

Tana fita tatarda Khalil ɗin zaune saman sofa yana latsa wayan sa

Ƙarisawa tayi ahankali tayi masa sallama

Hakan yasa yaɗago kai yana kallon ta at the same time yana amsa mata sallaman tare da ɗaura murmushi a fuskar sa

“Maman Husna”. Yafaɗa idanun sa akan ta

Murmushi tayi tana Sad da kanta ƙasa don bata son ko kaɗan suna haɗa idanu, sai taji kamar wasu abubuwa suna fita ta cikin nasa idanun su shiga cikin nata

“Dama yaya Khalil nazo ne kayi min wannan assignment ɗin”.

Gyara zaman sa yayi yana ajiye wayan yace “mu gani”.

Miƙa masa tayi

Ya’amsa yana duba wa, ya ɗau tsawon mintuna biyu yana duba wa kafin yaɗago kansa yana kallon ta yace “ina Bairo ɗin?”.

Miƙa masa tayi dasauri

Ya’amsa yaci gaba da dubawa kafin yasoma rubutun

Ita kuma tana tsaye tana kallon sa

“Baki gaji ba? ki zauna mana”.

Tatsinkayi muryan sa yana faɗin hakan batare da ya ɗago ya kalle ta ba

Babu musu tazauna kan hannun kujeran

Tsawon mintuna goma yaɗauka yana mata kafin yagama yakalle ta yana cewa “matso in yi miki bayani yanda zaki fahimta koda nan gaba”.

Hakan kuwa yayi mata daɗi don babu ita akai karatun shiyasa duk bata wani fahimta ba

Zama tayi kan kujeran sosai, shima kuma yamatso ta yanda zata iya ganin rubutun sannan yasoma mata bayani

Sosai tatsayar da hankalin ta waje ɗaya tafahimce sa duk da kuwa yanda take ji sabida kusancin su da yayi yawa

Sai da yagama sannan yaɗago kai yana kallon ta da murmushi yace “yauwa to na gama saura biya ko?”

Itama kallon sa tayi tana fid do idanu waje tace “ba kyauta kayi min ba?”

“Laa ba kyauta nayi miki ba, ki duba ai nayi ƙoƙari Yakamata ace kin biya Ni” yayi maganar yana shafa suman kanshi yana dariya ƙasa-ƙasa

“To nawa ne sai in biya ka?”.

“Duk yanda kika ba da babu matsala, amma meyasaka kike son karantan Low?”

Kanta tasauke ƙasa, batasan me zata ce masa ba illa jujjuya Bairo ɗin hannun ta da take yi

“Kinyi shiru”. Yace mata a hankali idanun sa ƙyam akanta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button