BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

Ɗago kai tayi takalle sa, ganin sun haɗa ido tayi saurin maida kanta ƙasa tana jin gabanta na sake matsanancin bugawa

“Ina so ne kawai”. Tafaɗa a matuƙar sanyin murya

Shiru yayi be yi magana ba, illa kallon ta kawai da yake yi cike da ƙauna, wannan kusancin nasu ya saka sa matuƙar nishaɗi da wani irin farin ciki ainun

Miƙe wa tayi ta ɗan saci kallon sa kafin tace “na gode yaya Khalil, Allah yasaka”.

Murmusawa kaɗai yayi be ce komi ba

Har ta juya kuma sai yace “ina Saleema?”

“Bata jindaɗin jikin ta shine takwanta”.

“Subhanallah..” yafaɗa yana miƙe wa

“Muje in duba ta”.

Ɗakin suka nufa

Suna shiga sukai wajen gadon, zama Khalil yayi yana kallon fuskarta

Har ta samu barci, gaba ɗaya jikin ta a rufe yake ruf sai fuskarta dake waje, a yanda take fitar da numfashi da ƙarfi zaka san jikin ta be mata daɗi, gashi fuskarta ya jiƙe sharkaf da zuba, gaban goshin ta sai tsatstsafo da gumi yake yi

Hannun sa yaɗaura a saman gashinta kasancewar ɗankwalin ta ya zame, shafa gashin kawai yake yi yana kallon ta cike da tausayi

Haka zalika Halwa dake tsaye itama kallon Saleeman take yi cikin tsananin tausayin ta

Babu wanda ke magana cikin su kowa da tunanin dake ransa, tsawon wasu mintuna kafin Khalil yamiƙe yafice a ɗakin

Yana fita Halwa takoma inda yatashi tazauna, tasaka hannun ta itama kamar yanda yayi tana shafa mata gashin

Bata tashi a wajen ba sai da taji kiran sallan Asar, kafin tashiga Toilet taɗauro alwala tafito, sallah tayi tacire Hijabin tana zama kan sofa, sai tabuga tagumi kawai tana kallon Saleema, sai dai abaɗini tunani kawai take yi

Daga ƙarshe tashi tayi tafito parlour, sai tayi hanyan kichen tana tafiya a hankali, tana shiga sai tatsaya tana tunanin abinda zata yi

Ta ɗan jima a tsaye kafin ta’isa wajen kanta tasoma kiciniyar ɗaura musu girkin dare, duk da dama girkin ranan Khalil ne yayi musu Take-away, ita taje yin test a makaranta, Saleema kuma rashin jindaɗin jikin ta yasaka bata girka ba, da Khalil ɗin yadawo sai be ma tambayi ba’asi ba yakoma yasiyo musu

Motsin da taji a bayan ta ne yasaka tajuya dasauri

Khalil ne tsaye ya harɗe hannayen sa akan ƙirjin sa ya zuba mata kyawawan idanun sa masu tsananin kaifi da burge wa, fuskarsa kuma yalwace da murmushi

Duƙar da kanta tayi tana jin matsanancin kunya ya kamata kasancewar ta bata da Hijab a jikinta, duk da riga da sani ne na atamfa a jikin ta, amma kuma duk da haka cikin ta yafito sosai ga kuma ƙiba da yasaka ta tayi

“Me zaki yi?” Yatambaye ta yana kallon ta yana ji kamar yahaɗiye ta sabida tsananin ƙaunar ta da yake ji a ransa

Halwa taba shi amsa batare da ta ɗago kai ta kalle sa ba

“Dama zan yi mana girki ne”.

Khalil yace “a’a ki bar shi kawai, idan na fita anjima zan siyo kar ki wahal da kanki uhmm?”.

Kaɗa masa kai tayi kamar ƙadangaruwa, bata sake ɗago kai ba sai da taji tafiyar sa kafin taɗaga kanta a lokaci ɗaya kuma tana sauke ajiyan zuciya me ƙarfi har da dafe ƙirji

Bata san meyasa take zama wata daban ba a gaban sa, sai takoma kamar ba ita Halwan da tasani ba

Murmushi tayi a fili tace “wlh na sauya sosai kamar ba Ni ba”.

Sai kuma tasaki dariya tana juyawa tanufi wajen Freezer bayan ta ɗau ɗanyen naman da taɗauko tamayar cikin Freezern, sai kuma tatsaya tana tunanin abinda zata girka taci, sosai take jin kwaɗayi tana son ta ɗan saka wani abun da zai mata text a baki

“Ko dai inyi ɗan wake ne?” Tafaɗa tana juya ido alamun tunani

Sai kuma tagirgiza kanta

“A’a bari in yi dai kalallaɓa, yeessss shi zan yi”. Taƙarike maganar da dariyan farin ciki a fuskarta

Kasancewar suna da komi sabida haka cikin ƙanƙanin lokaci tayi tagama sannan taɗauki Plate ɗin da tazuba tanufi hanyar fita, har ta kai bakin ƙofa sai tadawo taɗau Robbern yaji tafice

A Parlour tazauna taɗaura plate ɗin saman cinyan ta, tana ci tana kallon ta cike da nishaɗi da jindaɗin kalallaɓan

Bata san sanda Khalil yazo wajen ba sai tsinkayan muryan sa tayi

“Ashe dai hanci na be jiyo min ƙarya ba”.

Dasauri taɗago kanta a tsorace tana kallon sa

Hakan yasa yayi dariya yana zama yace “sorry na tsorata ki ko? Menene wannan kuma?”

Yaƙarike maganar yana kallon cikin Plate ɗin

Tana murmushi taba shi amsa da “kalallaɓa ne, bismillan mu”.

Taɗago Plate ɗin tana ajiye wa a tsakiyar su

“Ai kuwa zan ci, wannan abun tun daga ɗakin karatuna na jiyo ƙamshin sa”. Yayi maganar yana dariya

Sai kuma yasaka hannu yagutsira yakai bakin sa

Duk tana kallon sa tana murmusawa

Taunawa yasoma yi a hankali yana ɗan yamutsa fuska, sai kuma yasoma gyaɗa kansa yana wani lumshe idanu

“Waiii wannan abun daɗi yake dashi, me kika ce ma sunan sa?”

Dariya tayi tace “kalallaɓa”.

“Uhmm kalallaɓa yayi daɗi fa, Ni ban taɓa cin abun da yakai wannan daɗi ba, so texting”.

Murmushi tayi me fid da haƙora tace “ko dai santi kake yi?”

Saurin girgiza mata kai yayi yana taunan wanda yasaka a baki, a kuma time ɗin yake bata amsa da “a’a dagaske nake miki”.

Halwa dariya kawai take mishi, shi kuma sai zuba santi yake yi cike da barkwanci

Be cire hannun sa ba sai da suka cinye gaba ɗaya

Halwa ƙoƙarin miƙe wa tayi zata maida Plate ɗin kichen

Yayi saurin cewa “no koma ki zauna bari in Kai”.

Ya’amshi plate ɗin yakai kichen tare da wanke hannun sa yafito

“Gaskiya yayi daɗi, kinga daɗin sa ya saka na cinye miki ban rage miki ba, Allah yasa dai ya ishe ki?” Yayi maganar bayan ya dawo wajen ya zauna

Murmushi Halwa tayi tace “sai yanzu kenan zaka tuna bayan ka gama cinye min? To ya zan yi haka nan zan haƙura ai tunda ba wani”.

Shafo kansa yayi yana dariya yace “sorry na manta ne wlh”.

“Babu komi ai”. Tafaɗa cike da nishaɗi

“Wai yaushe ne zaku soma Exams ɗin nan ne, naga time na ƙure wa?”

Halwa tace “jibi ne insha Allahu”.

Zai sake magana wayan sa yasoma ƙara, ciro wa yayi cikin aljihun wandon sa yana kallon screan ɗin wayan, be ɗaga ba sai yamaida kallon sa gare ta yana faɗin

“Bari inje Tahir na jira na, idan Saleema tatashi jikin babu daɗi Please ki kira ni kinji? Bazan daɗe ba ma zan dawo”.

“To sai ka dawo Allah yatsare”.

“Ameen na gode”. Yafaɗa alokacin da yake miƙe wa yayi hanyan fita yana ɗaura wayan a kunne sa bayan yayi peacking call ɗin

Bin bayan sa tayi da kallo har yafice

“Yana da matuƙar kirki”.

Tayi maganar a fili tana murmusawa tare da kwanciya kan kujeran, lumshe idanun ta tayi cike da tsantsan farin ciki tare da tunanin Khalil ɗin

Yau dai baza ta iya hana kanta tunanin sa ba, don haka tabaje zuciyarta tana tariyo duk wani abu da yataɓa shiga tsakanin su, har da ma wanda be faru ba sai da zuciyar nata takawo mata tunanin tare da ƙawata mata abun ta yanda zai saka ta nishaɗi.

_kun san dai zuciya ????????????????__

[12/3/2020, 5:34 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button