BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Fourteen*
________????Sai da akayi kiran sallan magriba sannan tamiƙe tanufi ɗakin Saleema
Har a lokacin barci take yi bata farka ba, don haka tawuce kai tsaye cikin Toilet taɗauro alwala, hijab tasaka tayi sallah
Lokacin da tasallame Saleema tatashi
Jin motsin ta yasa Halwa juyawa tana kallon ta, sai kuma tamiƙe dasauri tanufe ta tare da faɗin
“Sannu Sister ya jikin?”
Ahankali ta’amsa mata da “alhmadulillah” tana yunƙurin tashi
Taimaka mata tayi tatashi zaune kafin tasake tambayan ta
“yanzu ina ke miki ciwo?”
Murmusawa tayi tana kallon ta tace “babu, sai dai kawai ƙarfin jiki ne bana ji”.
“Sannu gashi jikin ki duk zafi”. Halwa tafaɗa cike da tausayin ta bayan ta ɗaura hannun ta saman wuyan ta tana tattaɓa wa
Saleema tace “taimaka min in tashi zan yi sallah”.
Taimaka mata Halwan tayi tamiƙe sannan tariƙe ta takai ta har Toilet ɗin tafito, sai da tadaidaici ta gama abinda zata yi takuma komawa tariƙo ta suka fito, akan dadduma ta’ajiye ta taɗauko mata Hijabin ta
Sai da tafara sallan kafin tazauna gefen gado tana kallon ta
A zaune tayi sallan har ta idar
A Lokacin ne Khalil yashigo ɗakin da sallama
Halwa ce ta’amsa masa yayinda Saleema tabi shi da idanu
Takowa yayi zuwa wajen Saleeman yaduƙa agaban ta yace “Ya jikin naki?”
“Da sauƙi”.
Hannun sa yasaka yana taɓa jikin ta yaji zafi sosai, sai yamaida idanun sa kanta yace “but ga jikin ki da zafi anya baza muje asibiti ba?”
Duƙar da kanta kaɗai tayi batare da ta bashi amsa ba, domin ko kaɗan bata son yin magana sabida kanta sara mata yake yi
Hannun sa yamaida kan haɓan ta yaɗago kanta yana ƙura mata idanu, yayinda itama tazuba nata idanun cikin nashi tana kallon sa cike da rauni
Halwa dake zaune tana faman kallon su, sai tamiƙe dasauri tayi hanyan Toilet, sai kuma tadawo tayi wuri-wuri tarasa ina zata bi kawai sai tafice a ɗakin
Shi Khalil be ma lura da fitan ta ba illa ɗago Saleema da yayi tamiƙe tsaye, yajanyo ta jikin sa suka nufi kan gado suka zauna, hannun ta ɗaya yariƙe yana murza wa yayinda ita kuma takwantar da kanta saman kafaɗan sa ta saƙalo ɗaya hannun zuwa bayan sa tana lumshe idanun ta
Sun jima a haka babu me magana, sai kuma yasaki hannun nata yana ɗago kanta yace
“Bari in ɗauko ruwa da towel in rage miki wannan zafin jikin ko zaki ji daɗi”.
Bata yi magana ba har yamiƙe yashige toilet, ita kuma sai takwanta tana sake rufe idanun ta.
Fitan Halwa ɗakin ta tashige takwanta saman gado tana tarufe idanun ta tare da sauraron bugun zuciyar ta, sai kuma tasoma juye-juye ta kasa zama waje ɗaya don dai kawai tahana kanta tunani da kuma abinda take ji cikin zuciyarta
Tsaki taja tana miƙe wa zaune, sai kuma tamiƙe tafito parlour, anan tatarda ledojin da Khalil yashigo dasu, ɗauka tayi taduba sai taga abinci ne ciki hakan yasa ta kwashe tanufi dasu kan dainning
Kichen tanufa taɗauko coolars tasake abincin, sannan tasake farfesun kayan ciki shima a cikin coolar tarufe su yanda bazai yi sanyi ba, sai da tagyara wajen tayi setting komi abinda zasu buƙata kafin takoma ɗakin ta, sallan isha’i tayi tazauna nan tana lazimi batare da ta fita ba, sai da taji motsin su a Parlour kafin tatashi tafito itama
Saleema ce kaɗai zaune, ta sauya kaya zuwa kayan barci me taushi riga da wando farare
Wajen ta tanufa tazauna tana cewa “sannu Sister ya jiki?”
Murmushi Saleema tayi tace “alhmadulillah, dama ke nake shirin kira muci abinci kuma kin ƙule ɗaki”.
Dariya kaɗai Halwa tayi batace komi ba tamiƙe
Itama Saleeman miƙewa tayi suka nufi dainning, bayan sun zauna Halwa take cewa
“Ina yaya Khalil ɗin ko ya fita ne?”
“A’a yana ɗakin sa, yace be jin yunwa yana da aiki ya shiga yi”.
Gyaɗa kanta tayi tana zuba musu abincin
A haka sukai ta ci suna ɗan taɓa hira har lokaci yaja suna nan zaune a wajen
Daga ƙarshe Halwa tamiƙe ta tattara kayan takai kichen tafito tana kallon Saleema da har yanzu tana nan zaune bata motsa ba
“Sister Ni zan shiga ɗaki ina son Nima in Yi bitan karatu”.
Miƙe wa Saleema tayi tanufo ta tana faɗin “to muje nima in taya ki karatun”.
Halwa dariya tayi tace “kai sis ke dai ki wuce wajen mijin ki kar yaji ki shiru, ko baki san dare yayi bane?”
Itama dariyan tayi tace “na fiki sani ai, Ni dai muje in tayaki bana jin barci wlh, yanzu idan naje shima ya ƙufe akan aiki sai in ta zama Ni kaɗai”.
Shiga ɗakin suka yi suka zauna, Halwa ta jawo handout ɗin ta tana karatun Saleema na kwance tana jinta, kaɗan-kaɗan kuma suna taɓa hira
Sai wajen 10:00pm. Kafin Saleema tamiƙe tayi mata sallama tafice
Itama tashi tayi tarufe ƙofan sannan tasauya kayan ta zuwa na barci takwanta, bata ɗau lokaci ba barcin ya ɗauke ta tunda shine cike fal a idanun ta.
**** ***** ***** ****** *****
*WASHE GARI*
Washe gari ta kasance Sunday ranan da ake ɗaura auren Zainab
Babu laifi gidan an cika maƙil don dama suna da ƴan uwa da yawa, yayyin Zainab su uku duk ka mata ko wacce ta zo da iyalan ta, Haka zalika shima babban Yayan su dake zaune a Yola da nashi iyalan shima ya zo
Umma dai babu yanda zata yi ne amma kowa yaganta ya san akwai abinda ke damun ta, don ko gayyan mutane sai Zaituna ne ta’aika ma mutane, kuma ita taraba ma mutanen anguwa Chwingum duk dai don Umma taƙi yi.
Ƙarfe 11:30am. Aka shaida ɗaurin auren Zainab da Aliyu
A ranan kuma ƴan uwanta suka je ganin ɗakin ta suka ga abinda Yakamata su saka sannan suka wuce kasuwa, labulayen ɗaki da ƙarafen da za’a buga duk suka siyo, da sauran abubuwan buƙata, sannan suka koma gidan suka kafa
Lokacin ne kuma aka ɗauko kayan ɗakin ta da Abba yayi mata, don haka suka tsaya suka shirya mata komi inda yadace, ɗakin Amarya yafito fes gunun sha’awa
Sabon gini ne da yayyin Aliyu suka haɗa kuɗi sukai masa tunda dama yana da filin sa a cikin gidan su, daga Umman sa sai shi sai kuma autar su agidan.
Sasan sa daban akayi masa, sai da aka kewaye da gini, ɗakuna ne ciki biyu sai ƙaramin parlour a tsakiya, sannan ko wani ɗakin akwai Toilet a ciki, idan kafito a bakin ƙofan ɗakin shine kichen ɗin ta yake, har da kantan kichen sai da akayi mata inda zata riƙa ajiye-ajiye
Sai kuma babban Bayi dake sasan Umma
Komi yayi dai-dai gunun sha’awa Amarya kawai yake jira ɗakin
Da dare aka kawo ta gidan ta inda kowa yatafi yabar ta ita da Angon ta, sai muce Allah yasanya alkhairi *ZAINAB* ya nuna mana na ƴan baya lafiya.
_sai mun zo cin dubulan da cin-cin, kar agaji damu_????
[12/4/2020, 5:52 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
_Wannan shafin naki ne *NANA ALIYU* ki more kiji daɗin ki ke kaɗai bance wani yataya ki ba, na gode da ƙaunar ki gare ni._