BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Fifteen*

________???? *TWO DAYS*

Yau agajiye yadawo aiki, bayan yayi parcking motan sa yafito riƙe da briafcase ɗin sa da Suit ɗin sa da yacire, rufe motan yayi yanufi cikin gidan cikin tafiyan sa me burge wa, duk da kuwa a yanzu ɗin salon tafiyan ya sauya yana yi ne kamar me tsoron taka ƙasa, nan kuwa duk cikin gajiya ne

Tura ƙofan yayi kafin yayi sallama wanda a dai-dai laɓɓan sa yatsaya

Babu kowa cikin parlour’n don haka kai tsaye ɗakin sa yanufa, sai da ya’ajiye komi na hannun sa sannan yazauna yasoma zare Combat ɗin ƙafafun sa da Socks, bayan ya gama sai yaɓalle bottles ɗin rigan sa gaba ɗaya singlate ɗin jikin sa ya bayyana, be cire rigan ba sai yagishingiɗa akan pilow yana lumshe idanun sa

Tsawon mintuna biyar yaɗauka kafin yamiƙe yanufi parlour riƙe da wayan sa a hannu yana latsa wa

Har alokacin babu kowa a parlour’n don haka kansa tsaye yanufi kan dainning, har ya zauna kuma sai yamiƙe yanufi ɗakin Saleema

Ƙofar a buɗe yake ba’a rufe duka ba, har ya saka hannu zai sake tura wa yashige sai yaji maganar Halwa wanda yasaka dole ya ɗan dakata yana sauraron su

“Ki dena ma maganar Haris a yanzu, yanzu na rigada na cire wannan burin a raina, Ni ce Mahaifiyar Husna kuma na baki ita har abada wlh, kin san kuma be da iko da ita tunda dai ba aure aka ɗaura mana dashi ba, musulunci ya yarda idan an haifi yarinya ba da aure ba uwa ke da alhakin riƙe ta”.

Rungume ta Saleema tayi cike da farin ciki tace “gaskiya na gode ƴar uwata, kin bar burin ki akaina duk sabida ki faranta min bansan da me zan saka miki ba, Allah yabiya ki..”

Katse ta Halwa tayi da faɗin “Ni fa nace miki bana son godiya, idan na baki Husna ba ke ne zaki gode min ba, Ni ce zan gode miki, don haka ki dena min godiya don Allah”.

Sakin ta Saleema tayi tana murmushi tace “ai bazan dena miki godiya ba wlh, kin bani Husna sannan kina shirin haifa min wani ɗan, idan ban miki godiya ba me zan miki?”

Halwa tashi tsaye tayi tana yamutsa fuskarta tace “kinga Ni bani da lokacin wannan yanzu, bari inje inyi wanka in shirya in tai school, tunda yau Pepper ɗaya zan yi insha Allahu zan biya gida nagaishe da Ummi”.

Zaro ido Saleema tayi tace “me zaki je yi bayan kin san tace kar ki so ma ki je? Babu ruwana wlh”.

Dariya Halwa tayi tace “to na fasa”.

“Da dai yafi miki, banda ma kinibibi muna haɗuwa fa a Hospital salon dai ki ja mana tonon silili”.

Ƙofa Halwa tanufa tana ci gaba da dariyan ta

“Dama tonon ki nake yi in ji me Zaki CE”.

Ahankali yaɗaga ƙafafun sa da sukai mishi nauyi yamatsa bakin ƙofan sa yabuɗe yashige

Dai-dai da Halwa ta fito taji ƙarar rufe ƙofan nasa, kallon ƙofan tayi na ɗan seconni kafin taɗauke kan ta tana jan numfashi tare da shaƙan daddaɗan turaren sa da ya mamaye ilahirin wajen

Ɗakin ta tanufa tabuɗe tashige, tana shiga wanka tafaɗa.

          ***

A hankali ya ƙarisa gaban gadon sa jiki a matuƙar sanyaye, zama yayi yana dafe kansa dake barazanar tarwatse wa sakamakon abinda yaji, be ma san a wani yanayi zai fassara kalaman ta ba

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un..” yafaɗa a wani rikitaccen murya da dole kasan cewa yana cikin wani yanayi

A duk abinda yafahimta tana nufin kenan ita ɗin karuwa ce, ta haifi Husna ba ta hanyar aure ba, “Why zuciyar sa zatay masa irin wannan gangancin? Meyasaka zata so wacce bata kama ce sa?”

Hannu yaɗaura setting zuciyar sa yana ji tamkar yaƙwaƙulo zuciyar yawanke yagoge duk wani son ta da yataɓa wanzuwa a cikin ta

Sake runtse idanun sa yayi sai ga wasu siraran hawaye sun soma fitowa suna sauka kan dandamalin kumatun sa, wani irin ƙunci me haɗe da raɗaɗi ne yatsaya masa iya maƙogwaron sa, wanda ji yake yi tamkar yahaɗiye zuciya ya mutu sabida tsaban baƙin kishi da yake ji

Tsakiyar gadon yafaɗa yana ɗaura duk ka hannayen sa saman fuskar sa batare da ya buɗe idanun sa ba, shiru kawai yayi yana sauraron bugun zuciyar sa dake fita a wani irin yanayi me haɗe da firgitar wa ga duk wanda yasaurara

Tsawon lokaci yana a wannan yanayin mara daɗi wanda har sai da hawayen fuskar sa suka bushe batare da ya sake ƙwaƙƙwaran motsi ba

Saleema ce taturo ƙofan tashigo kasancewar Halwa da zata fita taje ta sanar mata Khalil ɗin ya dawo, hakan yasa tafito daga ɗaki tazo gare sa

Har taƙariso bakin gadon be motsa ba be kuma buɗe idanun sa ba, yana nan ayanda yake tamkar be san da wanzuwar ta ba, gadon itama tahau tana ɗaura rabin jikin ta kan nashi tace

“Mijina don Allah kayi haƙuri ashe ka dawo bansani ba, na Barka kai kaɗai”.

Idanuwan sa yabuɗe waɗanda suka sauya kala ainun, yazuba mata su batare da yace komi ba, kuma babu ko alamun walwala a face ɗin sa

Kallon sa itama take yi cike da tsoro don bata taɓa ganin sa a haka ba, cikin rawan baki tasoma jero masa tambayan “Lafiya me yafaru da kai? Meke damun ka?”

Rufe idanun sa yayi yana haɗiye abinda yatsaya masa a maƙoshi tun ɗazu, daƙyar yaɗaga hannun sa ɗaya yajanye ta a jikin sa yamiƙe da hanzari yana shige wa cikin Toilet

Sai kawai tasaki baki tana bin sa da kallo cike da wani irin baƙon yanayi, tunda take ko kaɗan bata taɓa ganin fushin Khalil ba, ko kaɗan baya da saurin fushi, babu abinda zaka taɓa gani a tare dashi da zaka san ransa a ɓace yake, amma yau kallo ɗaya idan kayi masa zaka san tabbas yana cikin wani hali me wuyan fassara

Tana nan zaune duk ranta a jagule, ƙiris take jira tasaka kuka, gaba ɗaya hankalin ta yayi mugun tashi fiye da tunanin me karatu, gaban ta sai bugawa yake yi tamkar zai faso ƙirjin yafito

Har mintuna 20 suka shuɗe be fito ba, sai kawai tasaki kuka jikin ta na wani irin rawa kamar mazari

Ahankali kukan nata yasoma isa kunnen sa, lumshe idanun sa yayi yana buɗe su a lokaci ɗaya, idanu yatsira ma kansa ta cikin mirror batare da ya sake motsa wa ba, sai da yaji kukan nata na fita da ƙarfi sannan yawanke fuskar sa yanufi ƙofa yabuɗe yafito

Dasauri kamar an tsikare ta ta’isa gaban sa, cikin kukan take cewa “don Allah mene yafaru ka ɗaga min hankali, ban taɓa ganin ka a haka ba me yasame ka?”

Idanu kawai yatsira mata cike da ƙaunar ta aransa, sosai taba shi tausayi yanda tanuna damuwar ta akan shi, hannun sa kawai yasaka yajanyo ta jikin sa yarungume ta sosai kamar zai maida ta ciki, gaba ɗaya ya zagayo da hannayen sa ta bayan ta yana faman shafa mata bayan, cikin sanyin murya a hankali yasoma rarrashin ta

“Shiiiiiiii.. Ya isa menene kuma na kuka? Ke abun kuka baya miki kaɗan ne ko kin manta halin da kike ciki ne..?”

Numfashi yaja kafin yaci gaba

“Babu abinda ke damuna kawai na tuna wani abu ne, amma duk kin bi kin ɗaga min hankalin ki”.

Yaƙarike maganar yana ɗago ta daga jikin sa tare da sakar mata lallausan murmushi

Izuwa yanzu ta tsai da kukan nata sai dai kallon sa kawai da take yi tamkar t.v, sosai take hango matsanancin damuwa a fuskar sa da muryan sa wanda shi kansa ya kasa ɓoye hakan

Hancin ta yaja yana faɗin “ki dena saka damuwa haka kinji, bari in Yi wanka ina zuwa”.

Sai yajuya batare da ya jira me zata ce ba yashige toilet ɗin

Tana nan tsaye bata jirga ba har sanda yafito

Shi kansa yayi mamakin ganin ta a wajen sabida daɗewan da yayi cikin Toilet ɗin

Matsowa kusa da ita yayi yana kallon ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button