BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

“Kina nan tsaye har na dawo?”
Kanta tasauke ƙasa batare da tace uffan ba
Hannun ta yariƙe yajanyo ta jikin sa yasake cewa “wai menene lafiyan ki ƙalau kuwa?”
Murmusawa tayi kafin tagyaɗa masa kai batare da ta furta komi ba, sai kuma tajanye jikin ta tana shirin juyawa tatafi yasake riƙe hannun ta yamaido ta jikin sa
“Ki faɗa min meke damun ki? ko dai..”
Sai yayi shiru be ƙarisa ba illa zuba mata idanu da yayi
Idanun ta tasanya a cikin nasa sai dai baza ta iya juran kallon cikin idanun ba, sai takawar da kai tana cewa “mu je in taimaka maka”.
Matse baki yayi kafin yanufi gaban mirror yazauna, tasoma tsane masa jikin sa da towel ɗin da yaɗaura a kafaɗa
Shiru yayi kawai yana kallon ta ta cikin mirror, har tagama masa komi sannan tadube sa tace
“Wani kaya zan ɗauko maka?”
“Ko wanne”. Yaba ta amsa a taƙaice
Juyawa tayi tanufi gaban sip ɗin sa tabuɗe tazaɓo masa riga da wando Three qweater, takawo masa har gaban sa sannan tajuya tafice.
Bayan ya gama shiryawa yafito yatarda ita zaune tana kallo
Tana ganin shi tamiƙe tanufo sa tana murmushi
“Kayi kyau”.
“Thank you Matata”. Yayi maganar yana maida mata martanin murmushin
Dainning suka nufa tayi saving ɗin sa, yasoma ci tana zaune gefen sa, tana so tayi masa hira sai dai yanda fuskar sa har yanzu babu walwala kamar yanda tasaba gani shiyasa tayi shiru abunta
Har yagama sannan suka koma Parlour
Tunda yazauna yaɗau wayan sa yana ta latse-latse wanda a zahiri ba wai komi yake yi ba, ya Bama kansa damar yin tunani ne batare da Saleema ta gane hakan ba, daga ƙarshe ma sai yatashi yashige ɗakin sa bayan ya sanar mata zai je yaduba wani aiki ne
Ita kuma sai tagyara takwanta saman Three sitter da suke zaune taci gaba da kallon ta
Har barci ya soma ɗiban ta Khalil yafito yatashe ta akan taje tayi sallah an kira, shi kuma yafice masallaci.
Lokacin da yafito masjid ɗin yahangi drever na ƙoƙarin shigar da mota cikin gidan, yana isowa yashiga gidan dai-dai itama Halwa ta fito cikin mota, ganin sa sai tatsaya jiran sa
Shi kuwa sai yaɗauke kai tamkar be ganta ba tare da ɗaure fuska tamau, ta gaban ta yazo yawuce be kalle ta ba, sai tayi saurin cewa
“Barka Yaya Khalil”.
Tafiyan sa yaci gaba da yi batare da ya amsa ba, yanufi Garden ɗin gidan
Halwa jiki a sanyaye tabi bayan sa da kallo yayinda tanufi cikin gidan, bata bar kallon sa ba har sai da takusa cin ƙasa sabida tuntuɓen da tayi, sannan ne tadawo da nutsuwar ta jikin ta tabuɗe ƙofa tashige.
.
_plz kuyi comments da share sannan ku danna Vote._
[12/5/2020, 3:34 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Sixteen*
________???? Ɗakin Saleema tashiga nan taganta tana nannaɗe dadduma alamun ta idar da Sallah
“Oyoyo Maman Baby”. Saleeman tafaɗa tana kallon ta fuskar ta cike da fara’a
Murmushi Halwa tayi taƙariso tazauna kan sofa tana faɗin “washh na gaji da yawa”.
Ajiye dadduman tayi tazo tazauna kusa da ita
“Lallai kam ki ce zan yi tausa yau kar Baby yayi fushi damu”.
Dariya Halwa tayi
“To ya jarabawan yayi sauƙi dai ko?”
Halwa tace ” alhmadulillah komi normal ƴar uwa”.
Saleema tace “masha Allah haka nake son ji, ya Baby be dai takura miki ba ko?”.
Miƙe wa Halwa tayi tana bata amsa “to ga dai shi nan duk yabi ya ishe ni ya hana Ni saƙat yau”.
Saleema marairaice fuska tayi tace “eyya sister Baki bashi abinci bane, i know kin bar shi da yunwa, muje yanzu ki bashi kar yasoma kuka”.
“Ai kya bari nayi sallah ko?” Halwa tace tana dariya
Kafin tanufi hanyan ƙofa
Saleema ma miƙe wa tayi tabi bayan ta, suka fito tare Saleema tana faɗin
“Kiyi sauri sister Plz”.
Halwa bata ce mata komi ba illa dariya da take mata tashige ɗakin ta, ajiye jakan ta tayi tacire Hijabin ta tashiga Toilet, alwala taɗauro tafito tashimfiɗa sallaya tamaida Hijabin ta tayi sallah, tana idar wa tazare Hijab ɗin tafita parlour
Lokacin Khalil ya shigo suna zaune shi da Saleema kan Two sitter, yayinda shi kuma yake latsa wayan sa
Ƙariso wa wajen tayi tana shirin zama Saleema tayi saurin cewa
“Sister je ki ɗibo abincin mana”.
Yamutsa fuska Halwa tayi tazauna sannan tace “wlh bana jin yunwa fa, kuma ban ce miki kukan yunwa yake min ba”.
Saleema kallon Khalil tayi tace “kana ji ko Ya Barrister, wlh sis sai ta haifa mana yaro ramamme ko kaɗan bata son bashi abinci”.
Khalil be ɗaga kai ba bare yayi magana ba
Hakan yasa Saleema tasake kallon Halwa dake kallon Khalil tana jiran jin me zai ce, don dama sun saba irin hakan kuma yana saka musu baki, amma yau saɓanin tunanin su be tanka ba
“Sister don Allah kije ki ɗibo abinci, baki ji me Ummi tace miki bane?”
Miƙe wa Halwa tayi tana nufan dainning tace “to bari dai in ɗibo shikenan ko?”
Dariya Saleema tayi tana faɗin “shikenan wlh, sai kuma inga kin cinye”.
Ɗago kai yayi yazuba mata idanu na tsawon soconni kafin yalumshe su yana jin wani baƙin ciki na ƙara shigan sa
Ji yake yi tamkar yaɗauke ta yakaita a cire cikin, kwata-kwata yanzu baya ƙaunar cikin kamar yanda yake jin son sa a baya, tunda a yanzu ɗin zai fito ne ta ƙazantar zina, “shikenan shi kuma yana ji yana gani za’a haifa masa yaro da dattin zina?”
Halwa na dawowa wajen yamiƙe yanufi ɗakin sa batare da yace komi ba
Saleema tabi bayan sa da kallo har yashige ɗakin sa, kafin tasauke ajiyan zuciya tana maida idanun ta kan Halwa wacce a yanzu ta lula duniyar tunani
Sosai taga damuwa akan fuskar sa wanda kuma yahaddasa mata rashin jindaɗi sam, sun rigada sun saba a ɗan kwanakin nan ko batay masa magana ba sai yayi mata, kuma kullum sai ya tambayi lafiyan Babyn sa, shiyasa da taganshi be tanka ta ba hakan be mata daɗi ba
“Sister yau kamar wani abun na damun Barrister ko baki lura da hakan ba?” Saleema takatse mata tunanin ta da faɗar hakan
Idanun ta tamurza tana kallon Saleeman tare da ƙirƙirar murmushi tace “Haka ne sister nima naga sauyi a tare dashi, but ki bashi lokaci zai koma normal tunda kinsan ba halin sa bane, kar ki ce zaki saka damuwa a ranki kinji?”
Murmusawa Saleema tayi tana gyaɗa kanta, sai kuma tace “yauwa Sister na gode har naji daɗi wlh, Allah ya yaye masa damuwar sa”.
“Amin”. Halwa ta’amsa mata tana saka abinci a bakin ta
Daga nan hira suka ci gaba da yi cike da nishaɗi.
****
Tun daga ranan kuma sai yazamana Khalil ya dena kula Halwa, ita kanta tuni ta fahimci hakan, idan har ya amsa gaisuwar ta daga hakan babu maganar dake sake shiga tsakanin su
Wannan dalilin ne yasaka itama ta dena shige masa kamar da, duk da abun na matuƙar damun ta aranta amma kuma ta danganta hakan da sabawar da sukayi ne a kwanakin baya, yanzu kuma ya zo ya dena mata magana.