BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

Fannin Khalil shi kuma duk yayi hakan ne sabida son cire ta aran sa, amma kuma tamkar ƙara masa wutar ƙaunar ta ake yi, ya rasa ya zai yi duk da ko kaɗan baya ƙaunar wani alaƙa yashiga tsakanin su, koda yaushe babu abinda yake tuna wa a ransa illa kalaman ta, hakan na ɓata masa rai matuƙa

A yanzu kuwa tuni ya sake rungume matar sa wanda yasan ita kaɗai ce kawai zai iya zama da ita, tunda wacce zuciyar sa ke so bata kama ce sa ba, soyayya tsantsa yake nuna ma Saleema wanda a yanzu ita kanta tasan da banbanci dana Da, yanzu sosai yake ƙaunar ta ko kaɗan baya son abunda zai ɓata mata rai

Ita dai Halwa ta zama ƴar kallo ne domin ko a gaban ta haka zai zaƙe yanuna mata soyayya ko a jikin sa, don haka wani lokacin in dai akwai shi a wajen ta gummaci tashiga ɗaki tazauna ita kaɗai, da tazauna tana ganin abinda ke ɗaga mata hankali yana saka ta tunani tare da hana ta ishashshen barci

Har yanzu ba wai ta yarda da cewa zuciyar ta na begen sa bane, wanda bata san cewa tuntuni ta afka kogin ƙaunar sa ba, kuma ko kaɗan bata taɓa kawo hakan a ranta ba, tunda babu ta yanda za’a yi ta auri Mijin Saleema wacce ta taimaki rayuwan ta, tabbas idan hakan yafaru da ita ta gummaci ta mutu da ƙaunar sa amma baza ta taɓa ba ma zuciyarta damar wannan tunanin mara amfani ba.

       Haka kwanaki suka shuɗe wanda har Halwa ta gama jarabawan ta an yi musu hutu

Kwanaki sun ci gaba da tafiya haka satikai yayinda aka tasar ma watanni, gashi yanzu har sun koma hutu sun shiga aji na uku

Ta ci gaba da rainon cikin ta yayinda yake ƙara girma, sosai cikin yake da girman mamaki wanda duk wanda yagani sai ya tausaya mata sabida tsaban girman sa, gashi ya saka ta ta kumbura ainun, kuma tun sanda yashiga wata na tara ta dena lafiya, yau ciwo gobe lafiya, tuni ta jingine karatun ta a gefe har sai sanda Allah yasauke ta lafiya

Shi kansa Khalil yanzu ba ƙaramin tausayi take bashi ba, duk da har a yanzu ba wai magana na shiga tsakanin su bane, idan ko kaji magana me tsawo ya haɗa su sai dai akan cikin ne

Tun farko shi ke kai ta awon cikin har yau kuma be fasa ba, wani lokacin su je da Saleema wani lokacin kuma su biyu suke zuwa.

       Yau ma ɗin gaba ɗaya tare suka shirya zasu je asibitin, kasancewar yau ɗin Halwa tatashi jikin babu daɗi sosai, duk da a gobe ne Yakamata su koma Hospital a duba ta amma kuma Khalil ɗin yace su shirya su je yau

Saleema ke riƙe da ita har zuwa wajen motan, tabuɗe mata tashiga daƙyar sannan itama tashiga

Khalil na zaune cikin motan yana kallon su ta cikin mirror, sai da Saleema tarufe motan sannan yasaki ajiyan zuciya yana tada motan yanufi bakin Gate

Me gadi ya wangale masa Gate ɗin yafice da hanzari

Waya Saleema taɗauka takira Ummi

“Ummi ga munan zuwa asibitin”.

“Subhanallah.. me yafaru ne ko haihuwar ne?”

Girgiza kanta Saleema tayi kamar tana kallon ta tace “a’a Ummi jikin ne dai babu daɗi shine zamu je”.

Ummi tace “to gashi kuma yau ban samu zuwa ba naje duba jikin Sultan baya jindaɗi, amma idan kun ƙarisa sai ki nemi Sister A’isha ta duba ku”.

“To Ummi ki gaishe da Aunty, Allah yabashi lafiya”.

Daga haka sallama suka yi tasaka wayan a jaka, sannan takalli Halwa dake jingine da kanta jikin kujera ta rufe ido ruf

“Sannu Sister”. Saleema tafaɗa kamar zatay kuka

 

Buɗe idanun ta tayi tasakar mata murmushi tana gyaɗa mata kai don baza ta iya magana ba sabida yanda take ji.

Koda suka isa cikin asibitin Saleema ce tariƙo ta sukai ciki, yayinda Khalil yabiyo su a baya yazauna a reception yana waya da Brr. Tahir

Sister A’isha tayi musu jagora zuwa wajen Likita, an duba ta babu wani matsala kuma ba haihuwa bane, don akwai sauran kwanaki a yanda suka ce musu, illa magani kawai da suka bata, sai ta ɗan kwanta na tsawon mintuna goma sannan suka sallame ta

Sun fito suka haɗu da Khalil ɗin, shi ya’amshi takardan maganin da suka rubuta mata yabar su nan yaje yasiyo sannan yadawo suka fito

Dai-dai sun kawo haraban Hospital ɗin, wani baƙar Mota dake fake a gaban Gate aka zuge glass ɗin, sai jin harbi suka yi wanda yasauka a kafaɗan Khalil dake gaban su yana tafiya, be tabbatar da abinda ke faruwa dashi ba yasake jin wani a setting inda aka sakar masa wancan, idanuwan sa ne suka juye lokaci ɗaya yasulale ƙasa riƙe da wajen, cikin second ɗaya ya dena motsi gaba ɗayan sa

Wanda faɗin nasa yayi dai-dai da kurma ihun da Saleema da Halwa suka yi suka bi shi da idanu da suka firfito dasu waje

Wani irin bugawa zuciyar Saleema tayi tay saurin riƙe ƙirjin ta tana kallon sa, bakin ta na rawa takira sunan sa da ƙarfi wanda yayi dai-dai da zubowar jinin bakin ta, sai kuma tasulale ƙasa tafaɗi babu alamun numfashi

Kuka Halwa tafashe dashi, tayunƙura tabi Saleeman ƙasa tana girgiza ta, lokaci ɗaya itama numfashin ta yaɗauke tafaɗi warwas sabida tsananin firgita da tayi

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”.

Gaba ɗaya jama’ar wajen sun hargitse sai salati suke saka wa, masu kuka nayi masu guduwa nayi, ƙalilan mutane ne sukayo kan su Khalil dake yashe a ƙasa babu rai a jikin su.

Baƙar Motar nan wanda a cikin ta aka yo harbin tuni sun arce a tsiyace.

[12/6/2020, 9:59 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Seventeen*

________???? *2 Hours Ago*

Suna zaune gaba ɗayan su a reception sun yi cirko-cirko hankalin su duk a matuƙar tashe, babu abinda suke tsimaye yanzu sai fitowar doctors su san wani hali suke ciki

Ummi da Mom sai faman share hawaye suke yi domin labarin abinda yafaru da yariske su ba ƙaramin girgiza su yayi ba

Fitowar Babban doctorn da ya jagoranci duba Su Khalil yasaka suka nufe sa gaba ɗayan su suna jera masa tambayoyi ko wannen su yana tare da fargaban amsar da doctor ɗin zai bayar

Likitan be ce komi ba illa ce musu da yayi su bi sa Office

A tare Dad da Abba tare da Sameer suka bi bayan sa yayinda su Mom suka kasa haƙura suka take musu baya

Bayan sun shiga sun zazzauna likitan yacire Glasses ɗin sa yana saka Handkerchief yashare zufan goshin sa sannan yadube su ɗaya bayan ɗaya yasoma da faɗin

“To alhmadulillah zamu ce tunda komi ya zo da sauƙi ba kamar yanda muka yi zato ba, duk kan su suna da rai, kuma munyi nasaran cire masa harsashin dake jikin sa insha Allahu nan da kwana biyu zai iya farfaɗo wa, sannan…”

Sai yasaki numfashi yana ci gaba da faɗin

“Ita kuma Saleema gaskiya matsalan ta babba ne, domin sanadiyar hakan zuciyar ta tayi wani irin razana wanda yahaddasa mata matsala ainun, kuma hakan ya saka Zuciyar ta tana barazanar bugawa wanda Allah ne kaɗai yatsare be kai ga bugawan ba, but.. yanzu ta shiga Coma farfaɗowar ta sai ikon Allah..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button