BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Ummi tafaɗa tana fashe wa da kuka, a tsaye take sai taja da baya tajingina da bango tana kuka kashirɓan jin halin da ɗiyarta mafi soyuwa a gare ta take ciki
Su kansu su Dad hankalin su yayi matuƙar tashi musamman Abba da yacire hulan sa cikin tashin hankali, babu abinda yake yi sai salati, sosai zuciyar sa ta taɓu da halin da yaji ƴar sa a ciki, sai dai ƙarfin hali da ya ara ya yafa ma kansa yayi juriyar hana kansa kuka
Shiru ne yaratsa a tsakanin su gaba ɗaya babu wanda ya’iya buɗe baki a cikin su
Girgiza kansa Doctor yayi cike da tausayin su yace “haƙuri zaku yi haka Allah yaƙaddaro, am.. ita kuma ɗayar Allah ya sauke ta lafiya duk da dai itama sakamakon gigitan da tayi jinin ta ya matuƙar hawa, sai dai muyi fatan samun lafiyan ta”.
Kallon likitan suke yi don basu fahimci me yake nufi ba
“Yanzu ana duba lafiyan Babyn ne kasancewar be yi kuka ba, amma da zaran sun fito zaku ji bayani”.
“Doctor Wai me kake nufi?” Cewar Sameer yana kallon sa da mamaki
Shima dai Doctor ɗin kallon sa yayi a rashin fahimta yace “me kenan kake magana akai Docta?”
“Likita maganar Halwa muke maka kuma mun ji kana maganar haihuwa?” Cewar Abba da yatari numfashin Sameer dake shirin magana
Cikin Ummi ne yayi ƙululu tuna abinda ke shirin faruwa, sam ta manta da cikin Halwa ɗin sai yanzu da ake maganar, gashi ba wancan likitan bane da yayi musu aikin bare yarufa musu asiri
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”.
Rufe baki tayi kukan nata yatsaya cakk tana sauraron abinda doctor ɗin ke faɗi cike da nunkuwan tashin hankalin da take ciki
Hannun sa yahaɗe waje ɗaya yana kallon su yace “too Ni dai ina muku magana ne akan ita ɗayar yarinyan wacce suka zube tare da ɗiyar ku, tana da juna biyu kuma ta haihu ɗa namiji, wannan shine maganar da nake muku”.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un..”
Gaba ɗaya suka faɗa a lokaci ɗaya, yayinda Abba yaƙara da faɗin
“To taya? Ta ina zata haifu bayan bata da juna biyu wannan wani irin abu ne?” Yayi maganar yana kallon Ummi da a yanzu hawayen fuskarta suka ci gaba da kwaranya
Ita kanta bata san me zata iya faɗa a yanzu ɗin ba amma kuma ta san dole ne kowa yasan abinda ke faruwa
“Kun ga yanzu ba wannan maganar zamu tsaya yi ba, mu je mu duba ta mu ganin ma idanun mu wataƙil ba ita ce ba”. Dad yafaɗa yana tashi tsaye
Gaba ɗaya miƙe wa suka yi suka fito, da jagorancin doctor ɗin suka isa ɗakin da aka kwantar da Halwa wanda har a lokacin bata farfaɗo ba sabida alluran barcin da aka yi mata, sai dai kuma a lokacin an dawo da jaririn nata an ajiye sa kusa da gadon ta yana kwance sai wutsil-wutsil da ƙafafu yake yi yana ƙwalala idanuwa, baya kuka sai dai hannu ɗaya da yasaka a bakin sa yana ta gwagwiya
Shigowar su sai gaba ɗaya idanun su yasauka akan yaron wanda a lokaci ɗaya suka nufi gaban gadon, Mom CE tasaka hannu taɗago shi tana kallon sa cike da zallan mamaki wanda duk kan su haka fuskar su yanuna
Yaron bashi da maraba da Khalil sak kamannin sa har skin ɗin sa, duk da kuwa Halwa itama baƙa ce amma skin ɗin iri ɗaya ne dana Khalil komi nashi yaɗauko
Salati da tasbihi suka saki suna sake kallon yaron cike da tsananin zargin da yaɗar su lokaci ɗaya a zuciyoyin su, wanda kuwa gaba ɗaya sun ɗaura zargin ne akan ɗan Khalil ne wannan, babu ta yanda za’a yi ta raini ciki a gidan sa be san da cikin ba har kuwa ya isa haihuwa, hakan yasake tabbatar musu da zargin su gaskiya ne
Kuka Mom tafashe dashi tana kallon Dad tace “Alhaji kana ganin abinda nake gani kuwa? Khalil..”
Sai kuma tayi shiru takasa ƙarisawa sabida kukan da yaci ƙarfin ta
Al’amarin da yaƙara ta azzara zuciyar Dad da Sameer kenan, domin su ma tunanin da suke yi kenan a ran su na cewar wannan yaron Khalil ne
Gaba ɗayan su shiru suka yi kamar an yi ruwa an ɗauke, in banda kukan Mom da ƙaran fanka babu abinda ke tashi a ɗakin, har ta da Doctor tsayawa yayi shima yana kallon su batare da yasan me zai yi ba
Motsin Halwa shi yafargar dasu daga tunanin da ko wannen su yake yi a ransa
Ummi ce tayi saurin matsawa kusa da ita tana ɗaura hannu saman nata tare da kiran sunan ta
Ahankali Halwan tabuɗe idanu tana bin mutanen dake cikin ɗakin da kallo, kana daga bisani kuma tasauke idanun ta kan Ummi da har yanzu take zirarar da hawaye, lumshe idanun ta tayi sai tabuɗe su cike fal da hawaye, cikin wani irin karyewan murya tare da sanyi sosai tace
“Ummi… Ina Saleema? Bata mutu ba ko? Don Allah kar kice min wani abun ne yasame ta?”
Sai kuma tajujjuya kanta tana kallon ƴan ɗakin kafin tace
“Yaya Khalil..”
Shiru tayi tana zirarar da hawaye sosai kamar an kunna famfo
Likitan ne yamatso kusa da ita yana faɗin “ki kwantar da hankalin ki kinji kinga kina cikin wani yanayin da ba’a son jinin ki yasake hawa, duk kan su lafiyan su lau babu abinda yasame su kinji ko?”
Kallon Ummi tayi, sai Ummin tagyaɗa mata kai
“To yakamata ku bata wuri ta huta ba’a son tana hayaniya, sannan sai ku nema mata abinci taci za’a bata magani”.
Likitan yafaɗa kafin yayi musu sallama yafice
Fitowa suka yi gaba ɗayan su suka bar Ummi a ɗakin, daga nan inda aka kwantar da Khalil suka wuce suka ganshi
Yana kwance babu riga an naɗe masa kafaɗa da bandage, tamkar matacce haka yake ko motsi baya yi, numfashi ma sai da taimakon Oxgyen
kuka sosai Mom tafashe dashi har sai da Dad yariƙo ta suka fito shima yana share hawayen sa, duk sun shiga tashin hankali matuƙa baka ma iya bambance wanda yafi shiga wani hali
Saleema kam ma basu samu damar ganin ta ba, domin an hana su ganin ta tunda har a lokacin akwai likitoci akan ta
Basu sake tayar da zancen yaron Halwa ba tunda kowa hankalin sa baya jikin sa duk da kuwa abun na ransu, itama kanta Halwan an sake yin mata alluran barci ta koma sabida har yanzu jinin ta be sauka ba, kuma suna son tasamu hutu sosai tayanda komi zai zama normal
Mutane sun soma tururuwan zuwa inda akai ta zuwa gaishe su, duk wanda yaji halin da suke ciki dole ya tausaya musu, Brr. Tahir ma yazo da matar sa, haka ma su Hakima da Abida drever ya kawo su, Nazeefa ma tazo sai kuka take yi tunda tashiga ganin Khalil, shiyasa Dad yasaka Sameer maida su gida gaba ɗaya, sai aka bar Mom da Ummi tare dasu Dad ɗin a asibiti
Kasancewar dare yayi bayan su Dad ɗin sun gama yin abinda yadace sai suka tafi, aka bar Mom wajen Khalil, ita kuma Ummi da Larai suka zauna wajen Halwa tunda Ita Saleema sun ce basu buƙatar kowa wajen ta, kafin su tafi da daren sai da aka bar su suka ga Saleema ta cikin Glasses, hakan ya ƙara ɗaga ma iyayen ta hankali sosai
Abba kuwa da tashin hankali yakoma gida, a ranan mutane da dama basu runtsa ba yanda suka ga dare haka suka ga rana
Halwa sai tsakar dare ta farka, tunda ta tashi Larai ta haɗa mata tea me kauri tasha, sannnan tace taba ma yaron Nono tunda sai tsala kuka yake yi domin shine ma yatashe ta, amma ina Halwa ko kallon ta bata yi ba bare ta tanka mata
Lokacin Ummi na sallah tana kai kukan ta wajen rabbi domin yaji ƙan ɗiyarta yaba ta lafiya
A karo na ba adadi Larai tace “Halwa ki shayar da yaron nan mana in dai ba so kike yi ya mutu ba, kinsan kuwa tun yaushe ake godo dashi yayi kuka be yi ba sai yanzu? Amma kuma kin ƙi kula sa bayan kuma kin san yunwa ke cin sa”.