BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

Murmushi Saleeman tayi duk da hawayen basu dena zuba a idanun nata ba
Ummi tashafa kanta cikin jindaɗi da ganin ƴartan ahalin lafiya, sai takalli Halwa tace “muje kiyi sallama da Baƙuwar tamu zata tafi”.
“To Ummi”. Halwa ta’amsa mata tana tashi tsaye
Dasauri itama Saleeman tamiƙe tana jeho ma Halwan tambaya akan wacece? Don tuni Ummi tayi gaba ta fice
Ataƙaice Halwa taba ta amsa da faɗin “wacce tadawo dani ne”.
Abba da Dad ne zaune a parlour’n suna sake sallama da Mami, kafin kuma su ɗunguma gaba ɗaya da Ummi dasu Saleeman suka je raka ta zuwa wajen motan ta, anan suka sake sallama yayinda Ummi take sake mata godiya tare da faɗa mata insha Allahu zasu har gida su sake mata godiya
Itama Halwa godiyar tasake mata tare da bata saƙon gaisuwa zuwa wajen su Safina
Har sai da tabar gidan sannan suka yo cikin gidan, Ummi tasoma yin gaba tabar su nan
Har zasu shige su ma suka jiyo ƙaran buɗe Gate, a tunanin su ko Mami ɗin ne sai duk suka waiga, saɓanin haka sai suka ga motan Khalil na shigowa ciki
Ahankali Halwa tajanye idanun ta daga kallon motan tabuɗe ƙofan tashige
Saleema da bata san da shigewar ta ba tajuyo da murna zata yi mata magana sai kuma taga wayan babu ita, murmushi tayi tagyara tsayuwar ta tana jiran isowar sa.
A ciki kuwa Halwa na shiga tanemi ƙasa tazauna tana gaishe dasu Abba duk kunya ya cika ta, su kuwa kamar babu wani matsala suka amsa mata cike da fara’a
Har ta tashi zata tafi Ummi tace mata takoma tazauna
Babu musu tabi umarnin ta
A lokacin ne su ma su Khalil suka shigo
Kusa da ita Saleema tazauna tana riƙo hannun ta gam, duk yanda ka kalli fuskarta zaka san tana cikin tsantsan farin ciki wanda hakan ba ƙaramin faranta ran iyayen nata suka yi ba, dawowar Halwa ɗin ya yaye mata duk wani ciwo da take fama dashi, tamkar ba ita ce take a mawuyacin hali ba ɗazu, har sai da aka yi mata alluran barci hankalin su yakwanta
Shima Khalil a ƙasa yazauna sabida girmama iyayen nasu, idanun sa ƙyam akan Halwa wacce kanta ke ƙasa ta kasa ɗagowa, sosai zuciyarsa tayi masa sanyi da jin labarin dawowarta wajen Dad..
Maganar Abba shi yadawo dashi hankalin sa har yaɗauke kansa daga kallon ta yana sauke ajiyan zuciya, a kwana biyun nan da babu ita har ya faɗa sosai sabida zullumi da tunanin rasa ta har abada, sai gashi kuma ta dawo wanda be taɓa tunanin hakan ba..
Faɗa sosai Abba yayi mata akan abinda tayi, daga ƙarshe kuma yayi mata nasiha me ratsa zuciya inda shima Dad yaɗaura da nasa, sannan yaƙare da faɗin
“Ina ga kamar yanda Hajiya tabamu shawara hakan yakamata muyi, Ibrahim ya sauwaƙe mata kar a sake samun matsala irin hakan, in yaso sai mu haɗa su ita da Sameer”.
A razane Khalil yaɗago kansa yana ware idanun sa kan Dad zuciyarsa na matsanancin bugawa..
[1/5, 3:14 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER twenty Seven*
________????Kuka Saleema tasaka tana roƙon Dad akan kar araba auren
Murmushi Dad yayi yana girgiza kai cike da mamakin irin wannan soyayyar nasu
“Don girman Allah kar araba auren nan Dady, wlh idan aka raba nima bazan zauna dashi ba dole sai ya sake Ni”.
Babu wanda maganar Saleema be basa dariya ba har Khalil kuwa dake a cikin matsanancin ruɗu, a yanda tayi maganar cikin taɓara da sangarta wanda kuma ita iya gaskiyar ta take faɗa tana ci gaba da kukan ta
“Ya isa to ƴata baza’a raba ba, nima wasa nake yi wlh”. Cewar Dad yana zuba murmushi
Cak kuwa taɗauke kukan nata jin abinda Dad ɗin yace
Yayinda Khalil yasauke ɓoyayyen ajiyan zuciya yana sauke kansa ƙasa zuciyarsa cike da tsananin ƙaunar Saleema, lumshe idanun sa yayi batare da ya sake jiyo zantukan da ake yi ba, domin tuni ya faɗa duniyar tunani, sai da Dad yaɗan zungure sa da ƙafa kafin yadawo hayyacin sa yana ɗago idanun sa masu tsananin haske da kyawu yazuba masa
“Tunanin me kake yi ana ta magana kana jin mutane?”
Ɗan wur-wurga idanu yayi ganin Dad ɗin ne da Abba kaɗai a cikin parlour’n, sauke kansa ƙasa yayi yana sosa ƙeya be ce komi ba
Murmushi Abba yayi yace “To Khalil sai kayi haƙuri da duk abinda zaka gani na zamantakewar ku, dama zaman tare zo mu zauna ne zo mu saɓa ne, bare in an haɗa da sha’anin mata, duk abinda zaka ganin kayi ta haƙuri kamar yanda kasaba, Allah yayi muku albarka gaba ɗaya”.
“Amin Abba”. Khalil yafaɗa idanun sa a ƙasa
Tashi Dad yayi yana faɗin “to Ni dai bari in soma gaba ko?”
“ai jira Ni sai mu koma tare nima ba zama zanyi ba”. Cewar Abba shima yana miƙewa
Lokacin su ma su Saleema suka fito sai sukai waje gaba ɗayan su, inda Ummi tayi musu rakiya har waje
Dad da Abba sun hau motar su daban-daban suka bar gidan, kafin shima Khalil yahau nasa yana jiran ƙarisowar su Saleema dake gefe suna magana da Ummi, Saleeman ce tatsaya tana ma Ummi magiya akan gobe a haɗo mata kan ƴaƴan ta adawo mata dasu, yayinda Halwa ke tsaye tana sauraron su tana murmushi
Abun da yasa ma yanzu batace zata tafi dasu ba saboda ita Husna tana school tunda ta fara zuwa, shi kuma Ahmad yana wajen Larai ta tafi dashi gidan su
Sai da Ummi tayarda zata kawo su gobe kafin tasamu sukuni wajen Saleeman, motan suka ƙarisa suka shiga yaja yay bakin Gate yafice bayan an buɗe masa Gate ɗin
Yana dai-dai ta motan nasa akan titi yasauke idanun sa kan mirror yana kallon Halwa dake baya zaune
Itama dai-dai lokacin ta ɗago kai tana amsa wa Saleema maganar da tayi mata suka haɗa ido
Yanda yakafe ta da ido ne yasa tajanye nata tana lumshe su tare da kau da kai gefe, bata sake gigin ɗago kai ba har suka kai gida.
*****
Kusan ƙarfe 05:30pm. Saleema tafito haraban gidan, Sale takira taba shi aike sannan takoma ciki, dayake lokacin Khalil ya fita sabida wani waje da zai je yau ɗin, dama yaso yawuce ne lokacin da yatashi Office sai kuma Dad yakira sa akan dawowar Halwa, hakan ne yasa be je ba sai yanzu da yamma
Ita kuwa Halwa tunda suka dawo sallah kaɗai tayi ko abinci bata nema ba takwanta barci, har yanzu kuwa barcin take yi batare da ta tashi ba
Saleema tayi mitan tashin ta don taci Indomien da ta girka musu amma ina tamkar wacce mayen ƙarfe ke ja sabida barci ko motsi taƙi yi
Yanzu ma da tashigo ɗakin nata kai tsaye gaban Sip ɗin kayan ta tanufa tabuɗe tasoma ciro mata kayan ta, sai da taciro su tsab sannnan tazuba cikin Trolly taja zuwa ɗakin Khalil, buɗe sip tayi tasoma jera mata har tagama sannan tasake fice wa
Nocking door ɗin da akayi yasaka tazarce kai tsaye bakin ƙofan, tana buɗe wa Sale ne tsaye da Ledoji guda biyu da ta’aike sa saƙo
Amsa tayi tayi masa godiya tare da rufe ƙofan tajuya ciki, ɗakin ta takai ta’ajiye inda baza’a gani ba sannan tafito takoma ɗakin Halwa