BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

Halwan na zaune abakin gado tashin ta kenan tana maida ɗankwali kanta da yakwance time ɗin tana barci
“Kasa kin ta shi?” Cewar Saleema tana murmushi
Fuskarta taya mutsa tamkar dai yanda tasaba sai kuma tasaki murmushi tana gyaɗa mata kai kasancewar hamma ya taho mata, hannu tasaka takare bakin ta tana sake waro idanu kan Saleeman dake gaban mirror tana kwashe kayan kwalliyan ta tana zuba wa cikin wani farin kwando
“Sis me zaki yi dasu ne?” Halwan tatambaye ta da mamaki
Bata ɗago kai ba illa amsa da taba ta
“Zan mayar miki ɗakin ki ne, daga yanzu komi naki zai koma ɗakin Barrister ne tunda can ne ɗakin ki ba nan ba, yanzu ke matar gida ce bare ki zauna a ƙaramin ɗaki”.
Shiru Halwa tayi bata sake cewa komi ba amma zuciyarta na jujjuya maganar nata, sai kuma tamiƙe ahankali tashige Toilet, wanka tasoma yi duk da lokaci ya ƙure mata sannan sai taɗauro alwala tafito
Gaban Sip tatsaya tana ɗan murza idanun ta da sabulu yashiga wajen wanka, guntun tsaki taja kafin tabuɗe Sip ɗin tana kallon ciki da mamaki ganin babu komi, sai kuma tajuyo tana kallon Saleema wanda a yanzu har ta gama kwashe kayan gaban mirror ɗin tana tattara takalman Halwa a cikin wani kwandon
“Sister yanzu har kaya na kika kwashe?”
“Eh mana baki ji me nace miki bane? Ai daga yau kema zaki fara amsa matar *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* na haƙiƙa, domin yau Amarya ce ke”. Duk maganar nan da Saleema tayi tana ci gaba da aikin ta ne batare da ta ɗago ta kalli inda Halwan ke tsaye ta saki baki tana kallon ta ba
Shiru tayi tatsira mata idanu na tsawon lokaci batare da tayi abinda zai fishshe ta ba, sai da tagaji don kanta kafin tanufi ƙofa tafice tayi ɗakin Khalil, tana shiga tasauke ajiyan zuciya ganin babu shi ciki, da sauri ta’isa bakin sip ɗin tabuɗe tazaro doguwar rigan atamfa da tagani asama tare da ɗankwalin shi, Hijab tasake ciro wa tare da under wear tarufe, memakon tasaka a ɗakin sai takuma koma wa can ɗakin inda tabar Saleema har yanzu tana faman aiki, saka kayan tayi tahau kan sallaya tasoma gabatar da sallan Asar da bata yi ba
Lokacin da ta idar tuni Saleema ta gama kwashe mata komi, shigowar ta ɗakin ne Halwa dake zaune kan dadduma har yanzu tabi ta da idanu
Murmushi Saleema tayi tana dafe ƙugun ta da hannu biyu, taƙariso bakin gado tazube tana faɗin “washhh Allahna wlh nasha aiki, kin jini ne tamkar zan rabe gida biyu”.
Babu shiri Halwa tasaka dariya tana sake juyowa yanda zata ganta
“To dama wa yasaki? Aikin da babu lada kawai kin saka kanki”.
Hararan ta Saleema tayi tana tashi zaune tace “ai in ke baki gode min ba Mijin ki zai gode min, kuma ai taimakon ku nayi ko?”
Dariyan dai Halwa tayi bata ce komi ba, murza hannun ta tayi tana tunanin yanda za’a yi tafurta abinda ke bakin ta, sai kuma tasake kallon Saleeman da a yanzu take ta faman jan hannayen ta tana naushin iska tamkar zata yi kuka, hakan sai yasake ba ma Halwa dariya, ai kuwa tasaka mata dariya
Yayinda ita kuma Saleema tasake kwaɓe fuska tana cewa “wlh sister ki dena min dariya dagaske nake yi baki ji yanda jikina ke min ciwo ba”.
Rage dariyan nata tayi tana kallon ta tace “to Sister ai gaskiya nafaɗa miki dama, meyasa zaki yi wannan aikin baki jira Ni na tashi in taya ki ba? Kin san Baki da lafiya amma don Allah kin ɗaura wa kanki abinda yafi ƙarfin ki”.
Saleema tace “to ai ke Amarya ce taya zan bar ki kiyi aiki? Bari ma kiji sai kinyi sati ɗaya curr Sannan zaki soma aiki agidan nan don na rigada na amshe komi”. Taƙarishe maganar cike da fara’a wanda kana kallon ta zaka san maganar da tayin ya saka ta nishaɗi ne sosai
Halwa har ta buɗe baki da ninyan yin magana Saleeman takatse ta da cewa
“Yauwa yanzu kinga saura abinci zan je in dafa mana shi kaɗai yarage min”.
Dasauri Halwa tamiƙe tana faɗin “ki barshi Ni zan yi”.
Hararan ta Saleema tayi tana yin gaba tafice batare da ta tanka mata ba
Itama bin bayan ta tayi har zuwa kichen ɗin, duk magiyan da Halwa tayi ma Saleema akan tabar shi ita zata yi but samm taƙi sauraron ta, dole ta haƙura tahau taya ta tana mita
Abinci me rai da lafiya suka shirya cikin awannin da basu gaza biyu ba, sai da suka gama suka kai dainnig suka jera sannan suka zube saman kujera suna taɓa hira, har sannan Khalil be dawo gidan ba.
Sai gab da magriba yashigo, alwala kawai yaɗaura yasake ficewa zuwa masjid, be dawo ba sai da akayi sallan isha’i kamar yanda yasaba akoda yaushe
Suna zaune a parlour’n yashigo da sallama, atare suka amsa masa tare da mishi sannu
Amsawa yayi idanun sa na kan waya, zama yayi yana ci gaba da latsa wayan sa kamar yanda yashigo yana yi
Saleema ce tatashi takawo masa ruwa ta’ajiye masa, ganin hankalin sa baya kansu sai suka ci gaba da hiran su, yayinda shi kuma yake ta latse-latsen wayan sa, ga duk kan alamu abu me muhimmanci yake yi, daga ƙarshe ma tashi yayi yashige ɗakin sa, be fi mintuna goma ba yafito
Saleema da tayi masa maganar abinci sai be amsa mata ba kasancewar a yanzu ɗin ya saka waya a kunne yana amsa Call, da hannu yayi musu nuni su je su ci, sai suka miƙe suka nufi dainning ɗin suka zauna
Kamar mintuna biyar da zaman nasu shima yaƙariso yana jan kujera gefen Saleema yazauna, yayinda suka saka ta tsakiya kasancewar Halwa na zaune ɗaya side ɗin nata
Khalil ɗin be wani ci abincin sosai ba saboda hankalin sa kacokan yana kan waya, Call yake ta amsa wa, daga ƙarshe sai yamiƙe yana jan kujeran baya yawuce abin sa yakoma ɗaki
Ajiyan zuciya Halwa tayi aranta tana mamakin yau kuma lafiyan sa ƙalau? To waya babu ƙaƙƙautawa sai kace wani ɗan Film
Miƙewa itama Saleema tayi tawuce ɗaki bayan tayi mata bayanin zata je tayi wanka tayi shirin barci sabida yau da wuri zata kwanta, duk gaba ɗaya ta gama tara gajiya a jikin ta, kasancewar bata jin ƙarfin jiki hakan yasa aikin yayi tasiri duk yasaukar mata da gajiya
Gyara zama Halwa tayi kan kujeran dainning ɗin, aranta itama tana son taje tayi wankan tayi shirin kwanciya amma tunawa da cewa kayan ta na ɗakin Khalil sai bata yi gigin zuwa ba, Allah yaso ta da wayan ta a hannu sai tayi zaman ta abunta tasaka Game tana yi.
Shi kuwa Khalil tunda yashige zama yayi bakin gado, ya daɗe yana wayan kafin yasauke idanun sa kan agogo, lokacin ƙarfe 10:30pm. Sai yamiƙe yashige toilet yayi wanka yafito, Direct sip ɗin kayan sa yanufa, yana buɗe wa idanun sa suka sauka kan kayan Halwa, mamaki ne yakamasa
Shiru yayi yana tsirawa kayan idanu, ya jima ahaka kafin yarufe yana buɗe ɗaya side ɗin yaciro jallabiya fara da gajeren wando, sai da yafeshe da turaren sa me ƙamshi kafin yasaka yafito zuwa ɗakin Saleema, ko kaɗan be lura da Halwa dake zaune kan dainning ba, tunda yakalli cikin parlour’n yatabbatar babu su sai yashige ɗakin Saleeman a tunanin sa ko suna ciki.
Halwa dake zaune tana kallon fitowar sa da shigewar sa ɗakin Saleeman, hakan yasa tasauke ɓoyayyen ajiyan zuciya don tasan maybe bazai fito ba ya shiga kenan,
Bata san meyasa ba tunda Saleema tayi mata maganar ɗazu sai jikin ta yayi sanyi, komi tana yin sa ne tare da fargaban me zai biyo baya tunda har yanzu bata san makomar ta wajen Khalil ba, “shin zai amshe ta a matsayin matar nasa ne ko kuwa zasu ci gaba da zaman da suka yi ne na baya?” Wannan amsar ne bata sani ba don haka tatashi tanufi ɗakin nashi.