BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

*****
Ƙariso wa Saleema tayi tazauna kusa dashi tana faɗin “Mijina yau fa ƴar uwata ke da kai bani ba?”
Murmushi Khalil yayi, duk da abinda ke ransa kenan amma be san yanda zai ce mata ba Cuz baya son tayi tunanin ko ya ƙosa ne, that’s why yabari ko zuwa gobe sai yazauna yaraba musu kwana, sai ma gashi kamar ta fahimce sa take faɗan hakan
Girgiza hannun sa tayi ganin yayi shiru ya tsira mata idanu
“Ko baka ji me nace bane?” Tayi maganar tana faɗaɗa fara’an ta
Basarwa yayi yana taɓe baki yace “naji ki mana Matata, But Ni ba yau nayi ninyan zuwa ba, sai ki bari zuwa jibi inyaso sai in koma ɗakin ta tunda kece babba ai”. Yaƙarishe maganar yana kashe mata idanu tare da janyo ta jikin sa
Bata san meyasa ba sai taji farin ciki aranta da maganar nasa, lumshe idanu kawai tayi tana ƙara lafewa a jikin sa, sai dai kuma bata jin zata iya barin hakan domin yau ta tanadar musu ranan nasa ne da Halwa, a ganin ta yau ɗin ɗakin ta yakamata yaje ba nata ba, don haka taɗago tana gyara zaman ta da kyau tace
“A’a Ni dai na yafe wlh, Ni fa na rigada na bar muku ka soma cin angoncin ka kamar yadda ko wani Ango yake yi na tsawon sati ɗaya, haka Shari’a ta yarje mana sannan sai mu raba kwana, bari ma kagani don Ni nayi muku tanadi”.
Taƙarishe maganar tana miƙe wa tanufi lungun gadon ta ta ɗaya side ɗin taɗauko ledojin da ta’aiki Sale yasiyo mata kaji da kayan maƙulashe
Khalil dake kallon ta yana ganin ikon Allah har ta’iso ta’ajiye masa a gaban sa tana sake zama sannan takalle sa da murmushi tace “gashi nan na tarban Amarya ne”.
Kallon ledan yayi, sai kuma yasaka hannu yaɗago yana duba wa, ɗago ido yayi yana kallon ta
Sai taware masa idanu still tana murmusawa
Be san me zai ce mata ba don haka sai yarungumo ta jikin sa yaɗago ta zuwa cinyan sa tare da haɗe bakin su waje ɗaya
Tabbas yau ya sake tabbatar wa Saleema na daban ce, da ita da Halwa bai san wacce tafi kyakykyawar zuciya ba, duk da Saleema tafi Halwa komi don bazai ce kyawu ne yaruɗe sa ba amma kuma zuciyarsa Halwa take tsananin ƙauna, be san meyasaka hakan ba, a ranan farko da yaganta be san komi nata ba but a kallon da sukai ma juna kaɗai zuciyar sa taharbu da tsananin ƙaunar ta, baya ga haka baya tunanin akwai abinda yaja ra’ayin sa ajikin ta da har yaji yana son ta tunda be san komi nata ba a lokacin, abun dai da zai iya cewa ƙaunar ta kawai daga Allah ne, shine yadasa masa ƙaunar ta a zuciya wanda yake jin sa yana gudana da jinin jikin sa tare da bugun numfashin sa, kullum ƙara jinta aransa yake yi memakon raguwa..
Tunda yahaɗe bakin su Saleema lumshe idanun ta tayi tana sauraron saƙon da yake aika mata dashi, ko kaɗan bata yi tunanin taya sa ba sabida bata son hakan yaɗau lokaci
Ganin dai yana wuce gona da iri sai tajanye jikin ta tana ƙara marairaice fuska ganin yana shirin sake haɗe bakin su, roƙon sa tasoma yi tana faɗa masa lokaci yaja be kamata yazauna anan ba
Daƙyar dai tasamu yabar mata ɗakin don sai da yaƙara ɓata lokaci wajen ta
Yana fita tagyara rigan ta tana faɗawa kan gadon tare da lumshe idanun ta hawaye masu ɗumi suka soma sulmiyo mata, wani irin tsananin ƙaunar mijin ta da kishin sa ne yake nuƙurƙusan ta, amma kuma tasan cewa yanzu ya tashi a nata kaɗai dole sai tayi sharing ɗin sa da wata, ko kaɗan bata jin haushin Halwa a yanzu, idan ma taƙi Halwan da mijinta ai dole sai ya auro wata tunda bazai zauna babu haihuwa ba
Danne zuciyarta kawai tayi taci gaba da rarrashin kanta, sai dai ta daɗe ahaka barci be ɗauke ta ba, sai kawai tatashi taɗauro alwala tasoma raya daren tare da roƙon Allah yaba su zaman lafiya kuma yakaɗe musu sheɗan a zamantakewar su, tare da roƙon Allah ya ƙara mata juriya da haƙuri, domin tabbas ba kaɗan ba zuciyarta tsananin zugi take mata kasancewar ta me fama da ciwo a zuciyan, shiyasa ta kasa jure zafin da take mata har tasaka kuka cikin sallan nata don dai kawai tasamu salama a zuciyar
Share this
[ad_2]