BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

“A’a yau Halwa ce a school ɗin?”.

Murmusawa Halwa tayi lokacin ta ƙariso wajen ta sai taba ta hannu sukai musabaha sannan tace

“Wlh kam ya kike?”

“Lafiya lau ya gida kwana da yawa?” Nafeesa ta faɗa tana murmushin itama

“Alhmadulillah”.

Nafeesa tace “to masha Allahu mu ƙarisa mana yanzu zamu yi Lecture”.

Halwa bata ce komi ba har suka ƙarisa class ɗin da zasu yi Lecture ɗin

Sai da suka zauna Nafeesa tace “ya ban ga Babyn namu ba? Tunda abun ma babu gayyata ba’a ɗauke mu a bakin komi ba shiyasa zumuncin ma ba’a son yi damu”.

Halwa kallon ta tayi sai dai ta kasa cewa komi, bata yi tunanin zuwan da take yi ada zasu fahimci tana da ciki ba, sabida tun lokacin da yasoma girma take zumbula Hijab har ƙasa sannan kuma tana kaffa-kaffa dashi don kar agane, kuma tana saka niƙap a fuskar ta bare su ce zasu fahimta

Abunda bata sani ba da yawa waɗanda take gaisa wa dasu sun san tana da ciki, har gulman ta suke yi ashe tana da aure ne bata faɗa musu ba, daga ƙarshe ma sai suka dena ganin ta gaba ɗaya duk da kuwa suna tunanin cewa ƙila saboda cikin ne tadena zuwa

Murmushi Nafeesa tayi tace “wai kina tunanin bamu sani ba ko? Ai kallon ki kawai muke yi tunda kin ƙi faɗa mana, kinga da mun zo suna ai”.

Itama Halwan murmushin taƙaƙalo tace “eyya kiyi haƙuri Nafeesa”.

“Babu komi ai”. Nafeesa tafaɗa tana dariya

Sai kuma tace “Me muka samu ne?”

Tana murmushi tace “Ahmad”.

“Allah Sarki ki ce sunan Saurayina ne? To Allah ya raya sa ta hanyan gaskiya”.

Ita dai Halwa murmushi kaɗai tayi tana amsa wa aranta

Nafeesa tace “to gashi kuma abubuwa da dama sun wuce ki, an sha karatu wlh ga kuma tests da akai ta yin mana”.

Cikin damuwa Halwa tace “eyya ban ji daɗi ba, yanzu ya zan yi kenan?”

“Kar ki damu zan raka ki wajen malaman sai kije ki nemi alfarma ko zasu yi miki tunda kinga an kusa fara Exams, kinga sai ki siya handouts ɗin da yawuce ki kije kiyi ta karanta wa”.

“Ai kuwa Na gode”. Halwa tafaɗa cike da jindaɗi

“Babu komi ai muna tare”.

Daga nan sun ɗan taɓa hira akan karatun su wanda Nafeesan take ta ƙara mata bayani akai, sai da Malam yashigo sannan suka nutsu suka maida hankalin su ga karatun.

       Kamar yanda Nafeesa tace mata zata raka ta wajen malaman, suna samun free suka tafi, taci Sa’a don wasu daga cikin malaman sun ce gobe tazo zasu yi mata, sai kuma waɗanda suka bata assignment, mutum ɗaya ne yayi mata text ɗin sa nan take, ai kuwa daƙyar ta amsa uku cikin biyar tunda babu wanda aka yi da ita, su ma ɗin wanɗanda ta’amsa turancin ta ne tagwamitsa yanda tafahimta sannan tamiƙa tafito.

Tunda tadawo gida babu abinda tatasa agaba sai karatun, sai wajen ƙarfe biyar tatashi tayi musu abincin dare sannan taƙara koma wa tadasa daga inda tatsaya tunda babu abinda zata yi.

[1/5, 9:31 AM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Twenty Two*

________????Zaman Khalil da Halwa zama ne tamkar ba mata da miji ba, babu abinda ke haɗa su sai gaisuwa, idan yatafi aiki itama sai tatafi school ɗin ta

Zata gyara gidan tayi musu girki kullum bata gajiya amma magana wannan baya haɗa su in ba ya zama dole ba

A ɗan zaman nan da suka yi a matsayin ta na matar sa tuni ta gane ta afka ƙaunar sa, bata da aiki yanzu sai tunanin sa da kuma zaman da suka yi abaya lokacin yana mata magana sosai, karatun da yasaka ta a gaba da kuma soyayyar Khalil wanda bata san sanda tafaɗa ba sun haɗe mata sun yi mata yawa, don haka gaba ɗaya yanzu ta rame ko kaɗan bata da sukunin zuciyarta, ga karatu ga tunanin da yazamar mata jaraba, da farko ta so duk yanda za’a yi ta yakice sa a ranta amma ina hakan ya gagara, wani lokacin har zuwa take yi tazauna kusa dashi tana masa magana ko wai zai riƙa kulata tasamu sukunin zuciya sabida yanda ƙaunar sa ke azalzalan ta, amma yanda tazauna haka zata tashi babu abinda ke haɗa su, hakan na ƙara saka ta shiga mawuyacin hali, har tashiga ɗaki tayi ta kuka tana tirr da zuciyar ta akan rashin adalcin da tayi mata, duk a maza ta rasa wanda zata so sai mijin ƴar uwanta da take ganin ƙimar ta sosai, wanda idan ba ƙaddara da ya haɗa su ba ba ta tunanin zata iya auren sa, a yanda tafahimta Khalil bazai taɓa son ta ba Saleema kaɗai yake so, ita kawai zata yi zaman haƙuri ne har sanda Saleeman zata samu lafiya tasan makomar ta, tunda tarigada ta saka a ranta idan Saleema bata son auren to guduwa zata yi, wannan shine kaɗai hanyan da taga zata iya guje wa auren nan.

            *****

Ahmad na wajen Ummi har yanzu ita take kula dashi, idan tatafi aiki sai kuma Larai tahaɗa su ita da Husna taci gaba da kula dasu, idan kuma ta dawo sai tarage mata aiki wajen amsar Ahmad ɗin, tunda aiyukan sun yi ma Larai yawa, ga aikin gida ga kuma raino.

Har yanzu dai Saleema babu labarin ci gaba, kullum iyayen ta addu’a suke yin mata Allah yatashi kafaɗun ta, idan Ummi taje aiki wuni take yi a wajen ta tunda yanzu ana barin ta tana shiga

Itama Halwa wani lokacin tana zuwa duba ta, takan yi kuka duk sanda taje taga Saleema cikin wannan halin da ba ta sanin a duniyar da take ciki.

Rayuwa taci gaba da tafiya yanzu gashi har Saleema ta shafe wata biyu curr kafin tafarfaɗo, zo ku ga murna wajen ahalin ta duk da kuwa ba wai ta dawo hayyacin ta gaba ɗaya bane tana cikin ciwo sosai, amma dai ahaka kowa ke murna da samun lafiyan ta

An ci gaba da treating ɗin ta har zuwa ɗan wani satikai inda tasamu lafiya sosai alhmadulillah sai abinda ba’a rasa ba, ciwon zuciyarta yanzu shine matsalan ta, but duk da haka an ɗaura ta akan magani

Duk idan Khalil yatashi daga aiki can yake wuce wa, wani lokacin ma idan zai tafi da safe sai ya soma leƙa ta kafin yawuce aikin sa

Haka itama Halwa daga school can take wuce wa tayi zaman ta sai dare idan Khalil yazo sai su taho tare

Hakan na faranta ran Saleema sosai, musamman idan taga ƴan uwanta tare da ita, babu jima wa aka sallame ta gaba ɗaya suka dawo gida

Tunda suka dawo sai kuma Halwa takoma kula da ita, ita take yin mata komi bata barin ta taɗauki ko tsinke, idan har ba wani muhimmin abu suke a school ba bata zuwa, tunda a yanzu ba an cika yin musu lectures bane sabida kusantowar Exams ɗin su, idan kuma suna da Lecture irin guda ɗayan nan ƙin zuwa take yi

Shima Khalil yana bata kulawan sa sosai, yana faranta mata da iyawan sa, sosai yake ƙara jin son Halwa aransa musamman yanda yaga tana ɗawainiya da Saleema ko kaɗan bata gajiya, wani lokacin sai yazauna yay ta tambayan kansa meyasaka yake mata haka? Halwa tana da kyawawan hali da shiga rai ga duk wanda yazauna da ita dole sai ta burge sa, to shi meyasaka bazai yafe mata ba? A yanzu dai ba laifin take aikata wa ba tunda ta tuba, yakamata yabata dama yacire haushin ta a ransa ya amshe ta hannu bibbiyu a matsayin matar sa tunda abinda yafaru ya rigada ya wuce, ko Allah ana masa laifi ya yafe bare kuma shi bashi ne tay ma laifin ba, kawai yayi amfani da hakan ne yana cuta ma kansa bayan kuma yana ƙaunar ta sosai a ransa, shiyasa yanzu yasassauto yake shiga harkan ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button