BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

Hakan ba ƙaramin faranta ranta yayi ba, sosai a yanzu take matuƙar farin ciki saɓanin abaya da koda yaushe take cikin damuwa

Saleema duk bata fahimci komi akan auren Khalil da Halwa ba tunda ba wai faɗa mata akayi ba, kuma Khalil ba kwana ɗakin Halwan yake yi ba, babu abinda ke haɗa su wanda zata iya zargin su, saboda tunda tadawo Halwa takoma ɗakin ta na da tadena kwana a cikin ɗakin Khalil ɗin, kuma tayi hakane duk wai saboda Saleema kar ta zargi wani abun tunda ba’a so tasani sai idan ta samu lafiya

Shima Khalil ɗin ganin haka sai yadena kwana aciki yana bin Saleema ɗakin ta, tunda dai babu daɗi ace yana kwanar mata a ɗaki shi da wata matar

Hakan yasa Halwa ta ƙara ganin ƙimar Khalil a idanun ta, tabbas Khalil mutum ne na daban, tsananin kyawun halin sa tare da kirkin sa ya wuce yanda ake zato, ɗaya ne tamkar da dubu, dole ko kana so ko baka so ka ƙaunace sa, idan har kuwa zaka yi mu’amala dashi dole ne yashiga ranka.

       Ahaka har su Halwa suka soma Exams ɗin su na First semester wanda daga shi ne sai Finally, sai kuma School of Low da zata shiga.

            **** ***** *****

Yau aka yi ma su Halwa hutun school don haka da wuri tadawo yau ɗin tunda Pepper ɗaya suka yi

Saleema na kwance kan two sitter ta ɗage ƙafafunta ta ɗaura saman jikin kujeran tajiyo sallaman Halwan lokacin da taturo ƙofan tashigo, tashi tayi dasauri tana mata oyoyo, suka yi Hugging juna suna dariya cike da nishaɗi sai suka zube saman kujeran

“Ai gwara da Allah yadawo dake da wuri, dama yanzu nake tunanin kiran ki in sanar miki zan je gida don yau da kewar su Abba na tashi, na tambayi Barrister ya bar Ni”. Saleema tayi maganar idanun ta kan Halwa tana dariya

Yamutsa fuskar ta Halwan tayi kamar yanda yazame mata jiki tace “kai sis yanzu sai ki tafi ki bar ni kenan?”

“A’a wlh nayi tunanin ba yanzu zaki dawo ba, Ni har nayi tunanin bari sai gobe ne kuma sai ga ki kin dawo, sai mu tafi tare yanzu”.

Kaɗa kanta Halwa tayi kafin tace “anya zan je kuwa wlh agajiye nike, barci kawai nake so in Yi”.

Saleema tace “to ki kwanta ki huta mana, ina tunanin ma idan naje zan taho dasu Husna ne”.

“Aa Iyeee wlh baza ki kawo mana aiki ba, akan me zaki ɗauko su?”

Wani kallo me kama da harara Saleema tasakar mata

“Me kike nufi?”

Halwa dariya tayi tace “wlh babu komi, amma don Allah ki bar Husnan ki ɗauko Ahmad ne”.

Miƙe wa Saleema tayi tay hanyan ɗakin ta tana faɗin “kar ki damu sister Ni ban ce ki tayani rainon su ba wlh Ni kaɗai zan iya tunda Ni ce uwar su dama ai”.

Bata tsaya jin amsar Halwan ba tashige ɗaki abun ta

Itama Halwa tashi tayi tabi bayan ta don taga fushi tayi da ita

“Haba Sister daga wasa?”

Turo baki Saleema tayi tana hararan ta batare da tace mata komi ba tasoma cire kayan jikin ta

Ganin dai ba tanka ta zata yi ba, sai tace “to nima zan je bari in shirya, tare zamu je taho wa dasu”.

Baki Saleeman tawashe tace “dagaske sis?”

Gyaɗa mata kai Halwa tayi tace “bari ma kigani”.

Tayi hanyan ƙofa tana faɗin “nima bari in je in shirya”.

          ****

Bayan sun gama shirin su drever yakai su gidan su Saleeman

Ummi tayi murnan ganin su barin ma da taga Saleeman ta sake samun sauƙi sosai har wani ƙiba tayi na kwanciyar hankali

“Ummi ina Abba ne don Allah”. Saleeman tafaɗa tana kwaɓe fuska tana kallon Ummi ɗin

Ummi murmushi tayi cike da ƙaunar diyar ta tace “ai yau Abban ki yayi nisan zango, amma ina tunanin zai iya dawowa kafin ku tafi”.

Gyaɗa kanta tayi tamiƙe tana faɗin “wai ina Husna ne ban ganta ba?”.

“Tana wajen Larai wlh, shima Ahmad ɗin don yayi barci ne takawo shi amma da duk suna wajen ta”.

Ɗakin Larai tanufa da ɗan gudun ta tana cewa “bari inje inga Ummina”.

Tun bata kai ba take kiran sunan Husnan har tashige

Ummi dawo da kallon ta wajen Halwa tayi tana dariya wanda itama Halwan dariyan take yi tace

“Ummi wlh Saleema son yaran ta yayi yawa ko kunyan ki bata ji”.

“To ina kuwa zata ji kunya na? Ai Saleema sai ikon Allah, ita da tazauna tana mana kukan cikin ta ya zube wani kunya zata ji anan”.

Dariya sosai Halwa take yi itama Ummin na taya ta

Ummin tace “Allah yay muku albarka yarana, yaba ku waɗanda zasu ji ƙan ku”.

Halwa na murmushi ta’amsa da “ameen Ummi”.

Lokacin Saleema tafito daga ɗakin Larai tana faɗin “itama tayi barcin”.

Dariya Halwa tayi tace “ai da kin taso ta tunda zumuɗin ganin su kike yi”.

Hararan ta Saleema tayi tana zama gefen Ummi tace “bazan tashe sun ba”.

Halwa dariya kawai take mata tana tsokanar ta, ita kuma tana rama wa cike da wasa da dariya

Ummi dai tana jin su bata saka musu baki ba, yau dai tayi ninyan faɗa ma ɗiyar nata auren dake tsakanin Halwa da Khalil, sabida a ganin ta be kamata ayi ta ɓoye mata ba kuma ana cutan Halwan, idan kuma hakan yaci gaba da tafiya tasan sun so kansu da yawa tunda sun gummaci su faranta ran ƴar su sannan su cuta ƴar mutane, yanda tagan su ahaka da tsananin shaƙuwar su bata jin Saleema zata wani damu, don haka ajiyan zuciya tasauke tana aza idanun ta kan Saleeman takira sunan ta

“Na’am Ummi”. Saleema ta’amsa mata tana kallon ta

Ummi tace “nasan kinsan ƙaddara Saleema kuma kinsan duk wanda yacika musulmi dole ne ya yarda da duk wani ƙaddara da tasame sa me kyau ko mara kyau..”

Gaba ɗaya shiru suka yi har Halwa suna sauraron ta, yayinda itama kuma tasoma zayyano ma Saleema duk abinda ke faruwa har da juya mata mahaifa yau sai da tafaɗa mata, kuma tayi hakan ne wai don Saleema tasake ganin girman Halwa, tasan cewa bata cancanci ɗaukan wani mataki akanta ba tunda ta taimake ta ta fanni da dama, tayi mata abunda babu wanda ya’isa yay mata shine kyautar yara har biyu, Halwa ba wacce zatayi kishi da ita bane domin ita ɗin me son farin cikin ta ne

Sai da Ummi takai aya a zancen ta kafin Saleema tamiƙe tsam daga wurin tawuce ɗakin su

Hakan yasa suka bi bayan ta da kallo cike da fargaba aran su

Matse baki Halwa tayi hawaye na cika cikin idanuwanta

Kallon ta Ummi tayi suka haɗa idanu sai Halwan tasauya fuskarta da ƙirƙirar murmushi batare da tasan cewa hawayen cikin idanun ta sun sauka saman kuncin ta ba

“Menene na kuka kuma? Bana son shirme kinji ko?” Ummi tafaɗa tana ɗaure fuskarta

Dasauri Halwan tasaka hannu tana share hawayen jin danshin su sosai saman kuncin ta wanda har ɗiga akan hannun ta suka yi, tana so tayi magana amma kalma ɗaya takasa furta wa, tana so tamiƙe tabi bayan Saleema amma ta kasa tashi

Ummi ce tatashi tanufi ɗakin, inda tasami Saleema kwance saman gadon ta danne fuskarta saman pilow, zama tayi akan gadon tasoma yin mata nasiha me ratsa zuciya tare da kwantar mata da hankali, sannan tana nuna mata koda ba Halwa bace dole ne Khalil yaƙara mata kishiya.

Halwa na zaune a inda take ta haɗe hannayen ta waje ɗaya jikin ta nata tsuma, so kawai take yi tasami damar da zata yi kuka sai dai baza ta iya nuna raunin ta anan ba, bashi da amfani ko kaɗan

Tana nan zaune su Ummi suka fito, idanu kawai taɗaura ma Saleema tana son karantan yanayin da take ciki

Ita kuma Saleema sai taɗauke kanta gefe batare da ta bari sun haɗa idanu ba

Larai ce tafito daga kichen tanufi dainning tana jera musu abinci

Cike da farin ciki Ummi tace “to ku tashi muje kuci abinci tunda an gama”.

Babu musu gaba ɗayan su suka bi umarnin ta, kan dainning suka zauna Ummi na ta jan su da Surutu duk dan wai su saki jikin su ganin yanda gaba ɗayan su suka yi shiru, babu wanda ke saka mata baki sai murmushi kaɗai da suke saki, sai kuma gajerun amsa da ke fitowa a bakunan su

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button