BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

Bayan sun gama suka dawo Parlour

Saleema bata zauna ba ta wayance tashige ɗakin Larai akan zata wurin Husna.

     Har suka gama wunin su Saleema bata sake bari magana ta haɗa su da Halwa ba, yamma na yi Saleeman tace zasu tafi ganin Ummi ma zata wuce wajen aiki, haka suka yi sallama suka fito tare da Ahmad da Larai tahaɗo masa kayan sa tunda Ummi tace baza ta tafi da Husna ba, kuma dama yanzu Husnan ta soma zuwa school ɗin ta ba ma wuni take yi a gidan ba

A cikin mota ma tsit suka yi babu me magana, Halwa ta kasa yin mata magana ne sabida fargaba, ta rasa wani kalma ne zata iya amfani dashi wajen furta ma Saleeman, musamman yanda taga ita kanta bata son kula ta bare kallon ta, sai hakan yasake saka ta damuwa da tsoro cikin zuciyarta

Suna shiga gidan suka fito cikin motan atare, Saleema na rungume da Ahmad tana ƙoƙarin jan Trolly ɗin sa da drever yaciro mata a Boot

Sai Halwa tayi saurin miƙa hannun ta dake faman rawa tace “sister bari in taimaka miki”.

Saleema bata ce komi ba tabar mata tajuya dasauri tawuce

Bin bayan ta da kallo Halwa tayi har sai da tashige cikin gidan, ahankali taja ƙafafun ta a matuƙar sanyaye tanufi ciki itama cike da rashin ƙwarin jiki, tana shiga da sallama idanun ta suka sauka kan su ita da Khalil ɗin dake zaune riƙe da Ahmad ajikin sa yana masa wasa, kallo ɗaya kayi masa zaka ga farin ciki tsantsa a fuskar sa wanda ganin tilon ɗan nasa ne yasaka sa wannan tsantsan murnan

Tunda tashigo shima yaɗago kansa yana kallon ta, wani irin kallo yake aika mata dashi me cike da zallan soyayya da nuna shauƙi ga duk wanda yagani

Hakan yaƙara saukar ma da Halwa kasala da mutuwar jiki, idanuwan ta tajanye daga kansa wanda suka kawo ruwa lokaci ɗaya tana ɗaura wa akan Saleema dake wasa da hannun Ahmad

Daƙyar tasoma jan ƙafafun ta bayan tacire idanun ta daga kallon ta tashigo cikin parlour’n, bata ce komi ba tayi hanyan ɗakin Saleeman tashige don ajiye mata Trollyn

Hakan yasa Khalil yabi ta da kallo cike da wani irin yanayi ganin yanda tasauya lokaci ɗaya duk da kuwa be ga hawayen idanun ta ba, amma ya tabbata akwai abinda ke damun ta

“Me yasami Maman Husna naganta ahaka?” Yayi maganar lokacin da yamaida idanun sa kan Saleema

Murmushi Saleeman tayi tace “babu komi wlh me kagani?”

Numfashi kawai yaja batare da yace komi ba yamaida idanun sa kan t.v

Lokacin Halwa tafito tanufi ɗakin ta tashige har da rufe ƙofan da keey, ahankali tazame ƙasa a jikin ƙofan tahaɗa kanta da gwiwa tasoma rere kuka, kuka take yi sosai wanda tatoshe bakin ta da gyalen ta ta yanda babu me jin ta, ita kanta bata san kukan na menene ba, sai dai tasan yana da alaƙa da yanda Saleema tanuna mata, wannan dalilin yasaka zuciyarta take mata wani irin zugi wanda ta san cewa dole ne rabuwar ta da wanda zuciyarta take bege a halin yanzu, alƙawari ne taɗauka kuma dole ta cika shi baza ta taɓa yin sanadin da Saleema zata sake shiga ƙunci a rayuwan ta ba, wanda ta tabbatar da cewa muddun tazauna batare da son ta ba bata jin zata yi farin ciki

Bata tashi a wajen ba sai da aka yi kiran sallan magriba, tamiƙe ahankali jiri na ɗiban ta sabida tsananin kukan da tasha, har gaban ta bata iya gani haka talallaɓa tashige Toilet taɗauro alwala

Sallah tayi tazauna nan bata tashi ba, sai da aka kira sallan isha’i sannan tatashi ta gabatar.

Lokacin da Khalil yadawo daga sallah shi kaɗai yazauna a Parlour, shiru-shiru yana jiran yaga sun fito amma babu wanda yafito cikin su, tashi yayi yashiga ɗakin Saleema nan yaganta zaune tana aikin gyaran kayan Sip da tawargazo gaba ɗaya tana maida wa

“Wai baza ku fito mu ci abinci bane?” Yace da ita lokacin da yaƙarisa gaban ta yana saka hannun sa ɗaya yadogare da Sip ɗin

Kallon sa tayi tace “zan zo amma yanzu Ni dai bana jin yunwa ne sai anjima”.

“Ok bari inje ɗaki nima ina da aiki”. Abinda yafaɗa kenan yajuya yafice

Yana fita yatsaya yana kallon ɗakin Halwa, shiru yayi yana tunanin yaje ko kar yaje, haka kawai yaji gaban sa na faɗuwa, gashi kuma yana jin babu daɗi ganin yanda tashigo a ɗazu kuma ya san bata sake fito wa ba har yanzu tunda tashiga

Numfashi yaja yanufi ɗakin sa yashige.

        *****

Ƙarfe 11:30pm. Lokacin gidan yayi tsit baka jin ƙaran komi

Ahankali Halwa dake zaune a ƙasa jikin gado tamiƙe tasaka Slippers ɗin ta taja Trollyn dake gaban ta shaƙare da kayan ta, cikin sanɗa tafito tana tafiya ahankali har ta’isa bakin ƙofan parlour tasaka hannu tamurɗa keey ɗin tabuɗe tafice

A haraban gidan babu kowa sai hasken lantarki da ya haskaka gaba ɗaya wajen, inda akwai duhu nan take raɓa wa tana bi duk da kuwa zuciyarta cike take da tsananin tsoro, amma abinda take hango wa shine kawai tabar gidan, bata son ko kaɗan tasake kwana a gidan nan

Tana isa bakin ƙofa taci Sa’a babu me gadi, sai dai ya rufe ƙofan ya shige ɗaki ya ɗan kwanta zuwa anjima sai yatashi yaci gaba da aikin sa

Ahankali tasaka hannu tazare saƙatan ƙofan taja Trollyn ta dasauri tafice batare da ta rufo ƙofan ba.

.

_uhmm wlh yau na gaji nasha typing da yawa, nayi muku har gobe ne ku karanta rabi yau sai ku bar rabin gobe????, Asha karatu lafiya Fans, Ina matuƙar ƙaunar ku._

[1/5, 12:13 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

_Wannan shafin naku ne *Mommyn Teema* tare da *Mmn Adnan/Yusra* ku more da wannan ɗin ???? ina godiya da ƙaunar ku gare ni._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Twenty Three*

________???? Washe gari da safe Khalil ne yasoma tashi yay Shirin sa na zuwa Office, dayake yau ɗin yana da aiki sosai don haka da wuri ya shirya be tashi Saleema ba yafito Parlour, yasan cewa Halwa ce ke yin musu girki a yanzu shiyasa yanufi dainning ɗin kanshi tsaye, amma me? abun mamaki babu breakfast ɗin

Tsayawa yayi yana kallon wajen cike da tsantsan mamaki, yasan bata taɓa late ɗin yin musu abin kari ba, musamman da tasan yanzu yana yawan fitan safe sosai

Ganin dai tsayuwar sa babu amfani sai yajuya yashige ɗaki yaɗau briafcase ɗin sa yafito, kasancewar sauri yake yi duk da kuwa yana son shiga yadubo ta ko lafiya sai dai kuma be yi hakan ba yanufi ƙofa zai buɗe yafita, abun mamaki ƙofan abuɗe yagani babu keey, sosai yayi mamaki a ransa yatsaya yana tunani ko dai jiya basu rufe ƙofan bane? shiru yayi yana son tuno wa, tabbas jiya ba shi yarufe ƙofan ba maybe su Saleema sun manta ne, da wannan tunanin yabuɗe ƙofan yafice

Motar sa yashiga yaja yay bakin Gate yana danna horn

Me gadi dake zaune bakin ƙofan a saman benci yayi saurin tashi yawangale masa Gate ɗin yafice

Sai a lokacin Gate man ɗin yasaki wata wawan ajiyan zuciya, tunda yatashi da asuba yaga ƙofan abuɗe yake a cikin ruɗu, yasan dai Khalil baya fita sallan asuba sai idan ta ɗauro, kuma ajiyan yariga kowa tashi agidan bare yay tunanin wani ne yazo yabuɗe, saboda ma yatabbatar da zargin sa sai da yatambayi ma’aikatan gidan duk suka ce masa basu bane, to yanzu jira yake yi yaji ko Oga Khalil zai yi masa maganar wani abun ya faru a daren jiya but ganin ya fita batare da ya tunkare sa da wata magana ba shine yaji dama-dama aransa, domin dai yana da tabbacin ya rufe ƙofan, kuma be sake dawowa wajen ba sabida barcin da yasha jiyan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button