BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

      Saleema bata tashi ba sai wajen ƙarfe 10:00am. Wanka tasoma yi sannan tashirya cikin doguwar riga na yadi me ruwan kuka, ɗinkin fitted gown ne sannan sai aka yi kwalliya da red stone a gaban rigan, ɗaura ɗankwalin simple tayi sannan tanufi kan gadon taɗauki Ahmad tazauna tasoma cire masa kaya

A lokacin yafarka yana saka mata kuka

Rarrashin sa tasoma yi tana ci gaba da kwaɓe masa kayan, bayan ta gama ajiye shi tayi tashiga Toilet tahaɗa masa ruwa a bawo tafito taɗauke sa, wanka tayi masa tadawo tashirya sa, sai da tahaɗa masa abincin sa taba shi sannan takwantar dashi tafito Parlour

Direct kan dainning tanufa sai dai ganin babu komi a wajen sai taja ta tsaya, shiru tayi na ɗan daƙiƙa kafin tasaki murmushi

Daman tasan za’a rina, Halwa zata shiga wani hali a sabida yanda tanuna mata a jiyan, ita har a zuciyar ta ba wai haushin Halwa take ji ba, tabbas dai taji kishin ta da Ummi tafaɗa mata yanzu tana matsayin kishiyar ta ne, amma kuma abinda yaƙara saka ta damuwa ce mata da akayi an juya mata mahaifa, sosai tashiga wani irin ruɗu da yahaddasa mata jin haushin Halwan a lokacin tare da tsananin kishin ta har takasa haɗa idanu da ita bare tayi mata magana, sai dai kuma ba wai tayi ne don muzguna mata ba tayi hakan ne kawai don samun damar yin tunani da zuciyar ta batare da tafito da damuwar ta fili sosai don su gani ba

A jiya kwana tayi tana sallah sabida gode ma Allah da yakawo mata Halwa cikin rayuwanta, sannan ta kwana tana roƙon Allah yaba su zaman lafiya a zaman da zasu yi, ta sani cewa zuciya bata da ƙashi duk ƙaunar da suke yi wa junan su tunda har kishi yahaɗa su tabbas sai sun ɓata, don itama jiya ba ƙaramin ƙarfin hali tayi ba da danne zuciyarta har zuwa yau ɗin da tatashi sakayau babu abinda ke damun ta, burin ta a yau ɗin tafaɗa ma Khalil yaraba musu kwana su zamto matan sa su duka.

Numfashi taja tana saka hannunta ta sosa goshin ta kafin tanufi ɗakin Halwa, tura ƙofan tayi tashiga da sallama tana wurwurga idanu cikin ɗakin ganin babu ita, bakin gadon tanufa tazauna a tunanin ta ko tana cikin Toilet, sai dai har tsawon shafewan wasu mintoci babu Halwa babu dalilin ta

Miƙe wa tayi tanufi Toilet ɗin tasaka hannu tayi Nocking, jin shiru sai tatura ƙofan tashiga taduba babu kowa, fito wa tayi tana sake bin ɗakin da kallo, a ranta kuma tana tunanin inda Halwa taje, tuna ko tana kichen ne yasaka ta fita tadoshi kichen ɗin, sai dai nan ɗin ma babu ita

“Haa’a to ina taje ne wannan matar?” Tafaɗa a fili lokacin da tafito Parlour tana sake kewaye parlour’n da kallo

Numfashi taja kafin tafice dasauri, Garden ɗin gidan tanufa tasoma dube-dube sai dai duk inda tasan zata iya ganin Halwa agidan ta duba babu ita, hankalin Saleema ya soma tashi sosai, cikin ruɗu tanufi bakin Gate

Me gadi tunda yahange ta yatashi yana muzurai

Tana isowa tambayan da tasoma yin masa sai da hantan cikin sa yakaɗa, amma cikin ƙarfin hali yabata amsa da cewa “wlh Hajiya Ni dai yau ban ga gilmawan ta ba, rabon da na ganta tun jiya da kuka dawo cikin gidan nan”.

Goshin ta ta dafe cike da tashin hankali, sai kuma tasake kallon sa tace “to ko ka ga sun fita da Barrister ne?”

“O’o O’o shi kaɗai yashiga motar sa yatai abin sa”.

Juyawa tayi dasauri har tana cin tuntuɓe, yanda zuciyarta lokaci ɗaya takawo mata banzan tunanin cewa ta gudu ne hakan yasaka hankalin ta yay mummunan tashi, har tana tuntuɓe tana faɗi wajen isa ɗakin Halwan da mugun saurin ta, Direct gaban Sip ɗin kayan ta tanufa tabuɗe tasoma duba wa babu komi aciki

Dayake ta dawo da kayan ta ɗakin, akwatunan auren ta kuma Khalil ya ɓoye mata a Library ɗin sa.

Wani irin mugun bugawa ƙirjin ta yayi, tana shirin zube wa ƙasa tahangi farar takarda dake kan gadon an danne rabin sa da pilow wanda tun shigowar ta ɗazu bata kula dashi ba, dasauri ta’isa wajen taɗau takardan tana buɗe wa gaban ta na faman faɗuwa, rubutun tabi da kallo kafin tasoma karanta wa

_Aslm alaikum ƴar uwata, nasan zaki ga wannan saƙon ne a lokacin da nayi nisa da rayuwan ku, kar ki damu bare ki ɗaga hankalin ki, Ni naga dacewar barin ku sabida wasu dalilai na, i know zama daku a yanzu be da wani amfani sabida naga kamar ina son shiga rayuwan ki ke da mijin ki, wlh sister bani da ninyan ƙuntata ma rayuwan ki, babu wanda ya tambayi ra’ayina akan aure na da Yaya Khalil, shiyasa yanzu na gummaci barin ku akan nazauna da auren sa batare da son ki ba._

_Abu ɗaya nake roƙon ki kiyi min alƙawarin zaki kula min da kanki, kar ki taɓa saka damuwa a ranki duk inda nake zan rayu ne cikin farin ciki tare da kewar ki a raina, sannan ki roƙa min Mijin ki yasake ni sabida bana son in zauna da auren sa a kaina._

_Allah yaba ku zaman lafiya da ɗorewan lafiyan ki ƴar uwat…”_

Yanda hawayen idanun ta ke sintiri saman fuskarta yasa takasa ganin sauran rubutun, gaba ɗaya ta jiƙe takardan da hawayen ta, kuka tafashe dashi tana zame wa ƙasa tafaɗi, kuka sosai take yi wanda yahaɗe mata da tari sai yi take yi babu ƙaƙƙauta wa, magana take son Yi amma Ina da zaran ta soma buɗe bakin sai takasa furta wa sabida tari da kukan da take faman yi, babu abinda harshen ta ke iya ambata sai sunan Halwan tana wani irin kuka me cike da tsantsan firgici tare da fita hayyaci

Zabura tayi dasauri tatashi tanufi ɗakin ta da gudu riƙe da takardan a tafin hannun ta, wanda tamatse sa gamm ta kasa saki, wayan ta taɗauka tafito Parlour tasoma neman layin Khalil, ringing ɗaya yaɗauka

Kuka tasake fashe wa dashi da ƙarfi tana tattaro numfashin ta wajen har haɗa kalmomin da zata faɗa masa

“Hal..wa.. ta tafi ta gudu.. ta bar ni, ta tafi.. Halwa…”.

Kasa ƙarisa maganar tayi sabida wani irin tari me haɗe da gudan jini da yataho mata

Khalil dake zaune kan kujeran Office ɗin sa, tun sanda yasaka wayan a kunne yasoma jiyo kukan Saleeman hankalin sa yay ƙololuwar tashi, tambayan ta yake yi ko lafiya duk da yaji tana magana but ya kasa jiyo me take cewa sai sunan Halwa da take faɗi, dasauri yaharhaɗa kwarmatsan sa yasaka wayan a aljihu batare da ya kashe ba, keey ɗin motan sa ya ɗauka yafito da mugun sauri duk hankalin sa a tashe, sosai yashiga ruɗu da faɗuwar gaba don yasan babu lafiya

Cikin mintunan da basu gaza 10 ba ya’iso gidan.

Saleema na nan zaune a inda take, izuwa lokacin tayi kiran Numban Halwa ya kai sau ashirin but amsan ɗaya ne a kashe yake Numban

Shigowar Khalil yayi dai-dai da sakin wayan da tayi tana sake fashe wa da kuka

Gaban sa ne yafaɗi time ɗin da ya sauke idanun sa akanta yaga jini a bakin ta, ga kuma wanda yaɗiga a ƙasa, cikin kiɗima yatunkare ta dasauri yana duƙawa gaban ta yariƙo ta tare da tambayan ta abinda ke faruwa

Amma ina ta kasa magana illa ƙara Volume ɗin kukan ta da tayi, daƙyar taɗago hannun ta tamiƙa masa takardan dake ciki

Dasauri yasaka hannu ya’amsa yana warware wa sabida yanda tacukuikuye shi duk ya yage, wani irin rawa jikin sa yasoma yi ganin abinda ke ƙunshe a takardan, idanun sa yakai kan Saleema da tuni numfashin ta ya rabu da gangan jikin ta, lokaci ɗaya sai ga hawaye sun cika masa idanu yana zama dirshan a ƙasa tare da dafe kansa da yasoma mugun sara masa, cikin wani irin sarƙewan murya yace

“Why Halwa? Why kike azabtar da rayuwana? Me na miki?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button