BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

A dai-dai lokacin da hawayen suka sauka kan kyakykyawar fuskar sa.
.
_kai gaskiya *SALEEMA* kina ganin rayuwa._
_anya baza mu bar Halwa taƙara gaba abinta ba abar Barrister da Saleeman mu? Tunda naga kamar kun fi sonta dashi._
_ko kuma daga nan Saleema tatafi tabar mana Halwan mu da Barrister._
_don haka yanzu ina son jin ra’ayoyin ku, ku zuba min ƙuri’a duk wacce tafi Fans tsakanin *SALEEMA* da *HALWA* to ita ce zamu bar ta da *BARRISTER* sai na ji ku._ ????????????????????
[1/5, 12:23 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
“`Wannan shafin naku ne masoyana Fhadeela, Fateeymuhammad, Auta Safna, Nana Faruk, Nafisa Ibrahim, Mum Afnan $ Yumna.. kuji daɗin ku da wannan page ɗin domin naku ne kyauta, na gode da ƙaunar ku gare ni.“`
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Twenty Four*
________???? Jiki na rawa Khalil yamiƙe yanufi Fridge ya ɗauko ruwa yazo ya yayyafa mata a fuska, bata motsa ba sai da yasake zuba mata sosai kafin takawo numfashi alamun ta dawo hayyacin ta, bata buɗe idanun ta ba sai dai hawaye dake fitowa ta cikin idanun suna gangarowa gefen kunnen ta
Kiran sunan ta yasoma yi but taƙi ta amsa masa duk da kuwa tana jin sa, hankalin sa ne yasake tashi yana shirin ɗaukar ta sai wayan ta tasoma ringing, ɗauka yayi ganin Ummi ne me kiran sai yayi peacking
Daga can Ummi ce tasoma magana da faɗin “Hello My dear”.
“Aslm alaikum Ummi ba ita ce ba”.
“Ok Khalil Kai ne ashe, to lafiya dai ko?” Ummi tafaɗa gaban ta na faɗuwa
“Ummi babu lafiya, Halwa ce tabar gida ita kuma Saleema gata nan akwance har suma tayi sabida tafiyan nata”. Yayi maganar ahankali cikin dauriyan murya da dannewar tashin hankalin sa
Cike da tsananin tashin hankali Ummi tace “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ta tafi kuma me yafaru ne?”
Bata jira kuma amsar sa ba sai tace “gani nan zuwa gidan yanzu insha Allahu”.
Wayan takatse tana ɗaukan gyalen ta tayafa tare da jakar ta tafito Parlour
Daidai lokacin da shima Abba ya fito daga nashi ɗakin yana saɓa malin-malin, hannun sa riƙe da takardu, su yamanta shine yadawo ɗauka
Kallon sa tayi yayinda shima yake kallon nata
“Lafiya na ganki ahaka meke faruwa?”
Ummi kamar zata yi kuka saboda tashin hankalin da take ciki tace “Abban Saleema wlh babu lafiya, wai Halwa ce tabar gidan ga kuma Saleema can hankalin ta atashe har suma sai da tayi”.
“Subhanallah.. mu je muje gidan”. Abba yafaɗa yana yin gaba dasauri Ummi na take masa baya
*****
Shashsheƙan kukan Saleema ne kaɗai ke tashi cikin parlour’n, tana jingine jikin Ummi, Abba kuma na zaune gefen Saleeman sun saka ta tsakiya, yayinda Khalil ke zaune a kujeran dake Facing nasu
Tunda suka zo suke faman rarrashin ta but taƙi yin shiru sai ma ƙara tayar musu da hankali da take yi, musamman yanda suka ga in tayi tari jini ke fita, kuma taƙi tashi akaita asibiti illa nuna musu cewa babu abinda ke damun ta ita Halwa kawai take son tadawo, baza ta taɓa iya rayuwa babu Halwa ba, taɓara dai irin na ƴaƴan gata shi tazauna tana ta musu, yayinda su kuma suke ta faman lallaɓa ta Ummi har da ƙwallan ta, kai da gani kasan ba’a hankalin ta Saleeman take ba
Shi kanshi Khalil tsananin tausayin ta ne ya cika sa, shima yayi rarrashin but taƙi kula sa sai kuka take yi tana surutai
Abban ne yace su koma gida in yaso sai akira Doctor yaduba ta, daga nan sai anemi Halwan ko za’a ganta, don haka suka tattara gaba ɗaya har Khalil da yaɗauko Ahmad yamiƙa wa Ummi suka bar gidan, su sun wuce gida shi kuma Khalil yabi cikin anguwa ko Allah zai sa yahaɗu da Halwa
Idan kukaga Khalil a yanzu zai matuƙar baku tausayi, sosai yashiga damuwa akan tafiyar Halwan, gaba ɗaya zuciyarsa ta kasa sukuni tun sanda ya karanta takardan nan, yana ji ajikin sa ta tafi kenan, wannan dalilin ne yasaka yashiga matsanancin tashin hankali, sai dai juriya da ƙarfin hali da yake dashi hakan yake saka wa baza ka gane a halin da yake ciki ba
Yayi yawo sosai babu inda be je ba wai ko zai ganta, duk da Halwa bata da wajen zuwa but inda be yi tunanin zata je ɗin ba duk ya duba, haka yaƙarishe yawon sa yawuce gidan su, inda anan ne yafaɗa musu halin da ake ciki
Su ma Dad da Mom sun tashi hankalin su matuƙa, anan ne ma Dad ɗin yake faɗa musu labarin Halwan da alaƙan su dasu Saleema
Lokacin da Dad ɗin yagama faɗa musu komi sai kawai hawaye suka ciko idanun Khalil, miƙe wa tsam yayi yafice daga parlour’n yadoshi part ɗin su inda ɗakin su yake na Da
Akan gado yakwanta yana lumshe kyawawan idanun sa, haushi da takaicin kansa kawai yake yi
Meyasaka ya ɗau laifi ya ɗaura wa baiwar Allah batare da yasan musabbabin rayuwan ta ba? Shin meyasaka yamanta cewa ƙaddara irin wannan zai iya samun ta batare da laifin ta ba?
Shin meyasa mutane suke ɗaura laifi ga macen da suka ganta tana rayuwan ƙasƙanci? Shin sun tambaye ta dalilin da yasa har tafito gida take wannan rayuwan? ko kuma sun manta cewa wasu sanadin fyade ne yajawo musu rabuwa da gida akan tsangwama da kyara da ake musu, menene laifin su don ƙaddara ta faɗa musu ake koran su? Shin mun manta da cewa idan suka tafi zasu ci gaba da wannan rayuwan ne ko kuwa su faɗa hannun ɓata gari wani abu yasame su ta sanadiyar mu ne.. Allah dai yatsare mana imanin mu yasa mufi ƙarfin zuciyar mu, ya Allah ka kare mana zuri’armu daga faɗa wa mummunan rayuwa..
Ajiyan zuciya kawai yake sauke wa, ya jima a haka kafin daga bisani yamiƙe yaɗauro alwala jin ana kiran sallah yafice.
Wasa-wasa har dare babu Halwa bare labarin ta
Izuwa lokacin har ƙarin ruwa sai da aka yi ma Saleema, sai da akayi mata alluran barci sannan suka samu sukuni domin yanda tashiga wani hali hakan ya ɗaga wa iyayen ta hankali, babu daman tayi tari sai jini ya fito, gashi Doctor yayi musu bayanin cewa idan har taci gaba da kasancewa ahaka to tabbas akwai matsala domin zuciyarta ta gama kumbura sosai
Abba yaso akai ta asibiti but likitan yace abar ta zuwa safiya idan jikin ya sake tsanani.
Bata farka ba sai washe gari, Ummi ita ta taimaka mata tayi wanka tashafa mata mai tare da saka mata kaya, sabida ko kaɗan bata da ƙarfin jiki bata iya yin komi da kanta, sosai suke ta lallaɓa ta suna faɗa mata kalamai masu daɗi yanda zata kwantar da hankalin ta
Abinci ma abaki Ummi taba ta sannan taba ta maganin ta tasha.
**** **** **** **** *****
Tunda Halwa tafito daga gidan sai tasaka kuka, tafiya take yi batare da tasan inda zata nufa ba, ahankali take jan Trolly ɗin duk da kuwa zuciyarta cike take da tsoro matuƙa ganin yanda garin yaƙara duhu gashi babu kowa sai haushin karnuka, but bata jin zata iya tsaya wa hakan yasaka taci gaba da tafiyan ta tare da danne tsoron ta cikin rai, tafiya ɗaya sai ta waiga ahaka har tafito titi inda anan ne take ɗan ganin motoci suna wulƙa wa