BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

Hannun ta tasaka tasharɓe hawayen fuskarta kafin tanufi titin don ta tsallaka, babu zato tahangi mota tayo kanta duk da kuwa bata san da zuwan motan ba sai ganin ta tayi kusa da ita, ƙwalla ƙara tayi amma ina tuni motan ta bige ta

Dasauri matar dake cikin motan tafito ita da ƴaƴan ta biyu suka yo Kan Halwa

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Matar take faɗa

Yayinda ƴan matan tuni sun saka kuka sabida halin ruɗe wa

“Ku taimaka min.. ku taimaka min na ɗauke ta”. Matar tasake faɗa cike da rawan baki

Daƙyar suka ɗaga Halwa suka nufi motan da ita suka saka ta daga ita har Trolly ɗin ta, matar taja motan suka bar wurin

Direct asibiti suka nufa, dayake sananniya ce wajen Likitan sai yasaka Nurse suka amshi Halwa batare da bincike ba akayi Emargency Ward da ita

A reception suka zauna zaman jiran fitowar likitan

Mintuna kamar 20 yafito yanemi Matar tabiyo sa, bayan sun zauna a Office ɗin sa yasoma mata bayanin abinda ke faruwa

“Ba wani abu bane yasame ta sai buguwa da tayi akanta wanda hakan yaja mata dogon suma, amma da yardan Allah zuwa gobe zata iya farka wa”.

Wannan bayanin na likita shi yakwantar wa matar da hankali, daga nan suka tattauna sannan tafito tasami ƴan matan ta suna jiran ta

Tambayan ta suka hau yi har yanzu suna zub da hawaye don ba ƙaramin tashi hankalin su yayi ba

Kallon su tayi cikin kwantar musu da hankali tace “ya isa haka babu abinda yasame ta illa buguwa da tayi akanta”.

Atare suka sauke ajiyan zuciya suna faɗin “alhmadulillah”.

Murmushi tayi kafin tace “to yanzu yakamata ku koma gida inyaso Ni sai in zauna da ita don baza mu tare anan ba, kuma ban ce ko waccen ku takira Daddynku tafaɗa masa ba don kar hankalin sa yatashi kuna jina?”. Matar Taƙarike maganar da jan kunnen ta

Gyaɗa mata kai suka yi atare suna cewa “to Mami”.

“But Mami ki bari Ni zan kwana da ita mana tunda ba wani abu me wahala bane”. Cewar Safina tana kallon Mami ɗin cike da son amincewar ta

“Ok to bari mutafi gida Ni da Nafisa, but ki kula bana son rawan Kan nan naki kinji Ni? Idan da akwai matsala kiyi kiran Doctor”.

Safina tace “to Mami insha Allahu”.

Daga haka babu abinda suka sake faɗa illa wuce wa ɗakin da aka kwantar da Halwa da suka yi, basu fi mintuna goma ba Mami da Nafisa suka fito suka bar Safina a wajen ta.

_sai muce Allah yabaki lafiya Halwa._

[1/5, 12:58 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

_Fateema Zahra, Hauwa Ali, Wanka Yakubu Isa, Munir Y Abdullah, M. Bintu Thank You for the loving My Book._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Twenty Five*

________????Washe gari da sassafe Mami tadawo Asibitin da breakfast, Safina na gaishe ta ta’amsa tace mata

“Yauwa to tashi kije yi maza Drever na jiranki ki koma gida ki shirya kar kuyi late, ki tabbatar kinyi breakfast kafin ki tafi ko kuma ki ɗiba ki tafi dashi kina jina?”

Murmushi Safina tayi lokacin da tamiƙe tana ɗaukan gyalen ta

“Mami sai kace wata yarinya haka kawai sai inje da Breakfast school?”

Hararan ta Mami tayi tace “Ni dai na faɗa miki kuma na bada sallahu idan ma baki je dashi ba Nafisa zata faɗa min, ai na faɗa miki daga yanzu na dena baku kuɗi, wuce ki tafi kar in saɓa miki uwar shiririta”.

Turo baki gaba tayi tafice batare da tasake cewa komi ba

Ita kuma Mami zama tayi idanun ta akan Halwa wacce ko motsi ba ta yi tun jiya tana nan ayanda take, an naɗe mata kai da bandage sabida ba ƙaramin rauni taji ba

Ajiyan zuciya kawai Mami take sauke wa cike da tsananin tausayin Halwa, kawai aranta tunanin yanda aka yi matashiyar yarinya kamar wannan tafito gidan iyayen ta da tsakar dare take yi.

       Tana nan zaune wajen ƙarfe 09:00am na safe sannan ne Halwa tafarka, don haka tamiƙe da hanzari takira Doctor coz tunda tafarka ɗin tabuɗe idanun ta bata sake motsawa ba, duk sannun da tajero mata taƙi ta amsa ta

Doctor da yazo yadudduba ta yatabbatar bata da wani matsala sannan yace aba ta abinci taci sai tasha magani

Sai da yafita kafin Mami tasoma haɗa mata abin kari, bayan ta gama takalle ta kamar yanda Halwan tazuba ma matar idanu tamkar me neman wani abu ajikin ta

Murmushi tayi mata tace “tashi kisha kinji?”

Halwa batace komi ba tayunƙura tagyara zaman ta, duk da babu abinda ke damun ta amma sosai kanta ke mata ciwo daƙyar take iya motsa shi, amsar Cup ɗin tayi tariƙe da hannu biyu ta kasa sha

Sai da matar takula da ita kafin tace “af na manta baki wanke baki ba ko zaki fi jindaɗin sha”.

Amsar Cup ɗin tayi tamiƙo mata ruwa, sai da tawanke bakin kafin tamiƙa mata Tea Cup ɗin, sannan alokacin tasake ciko mata Plate da Arish da soyayyan ƙwai ta’ajiye mata akan gadon, sai tatashi tafice don tabar ta tasake

Tana fita Halwa talumshe idanunta, aranta kewar gida kawai take yi tare da tunanin makomar ta a yanzu, bata dena tunanin ba take ta tsoma bakin ta tana shan tea ɗin zuciyarta duk babu daɗi

Ta jima ahaka batare da tasan awani hali take ciki ba, har Mami tadawo tatarda ita ahaka ko rabin Cup ɗin bata yi ba, babu ma abinda tataɓa acikin Plate ɗin

Mami kallon ta tayi tana nazartan ta, kafin kuma tatamke fuska cikin serious face tace “har yanzu baki ci komi ba ashe? Bana son shashanci Yi maza ki cinye ki bani Plate ɗin da kofin”.

Kallo ɗaya Halwa tayi mata ta tabbatar matar ba ta ɗaukan raini, nan da nan taji tsoron ta ya kamata ta batare da tayi mata musu ba tayi yanda tace mata tamiƙa mata Plate ɗin kamar yanda tabuƙata

“Good kinyi kyan kai”. Mami tafaɗa bayan ta amsa ta ajiye sannan tafice

Da kallo Halwa tabi ta tana tunanin ita kuma wannan matar daga ina? Menene haɗin ta da ita? Ita dai tasan an bige ta to ko dai ita ce tabige ta ɗin?”.

Tana cikin wannan tunanin ne suka dawo da doctor, magani yaba ta bayan ya tambaye ta “ko akwai abinda ke damun ta?”

Dayake Halwa jin ta take yi tamkar a ƙaya musamman yanda matar nan tanuna mata sai taji ta ƙosa su raba hanya, don haka tace masa babu abinda ke damun ta

Hakan yasa Doctor ɗin ce ma Mami zuwa anjima za’a sallame ta.

       Ƙarfe 02:35pm. Safina da Nafisa suka kawo abincin rana, ganin Halwa ta farka ga jikin ta dasauƙi hakan ya faranta musu rai sosai musamman ma Safina, kasancewar ita akwai ta da son mutane ga fara’a ba kamar Nafisa ba, hakan yasa lokaci ɗaya tashige ma Halwa tana ta janta da Surutu

Itama Halwa sosai tasaki jikin ta zuwan su ba kamar ɗazu ba duk da kuwa ba magana take yi ba iyakan ta murmushi da bin Safinan da kallo me zuba mata surutu.

Da yamma aka sallame su suka taho gida, babban gida ne dasu me kyau sosai, kai da gani kasan ba ƙaramin kuɗi ne da me gidan ba

Suna isa Safina taruƙo mata hannu suka yi ciki, ɗakin su takai ta tahaɗa mata ruwan wanka tashiga

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button