BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

Itama Nafisa sai gata ta shigo da Trolly ɗin Halwa ta’ajiye mata tafice

Safina na zaune bakin gado tana jiran Halwa har tafito, murmushi tayi mata tace

“Aunty ga kayan naki nan sai ki shirya ina zuwa”. Taƙarike maganar tana miƙe wa cike da zumuɗi

Gyaɗa mata kai Halwa tayi tare da mata murmushi, har tafice tana kallon ta kafin tazauna gefen gadon tana zuba tagumi, ta ɗau lokaci ahaka har Nafisa tashigo ɗakin batare da ta sani ba, sai da tataɓa ta kafin taɗago kai dasauri tana kallon Nafisan, ko kaɗan ba wai ta gane ko wacece acikin su ba duk da kuwa taji sunayen su tun a Hospital, but tsananin kaman da suke da juna baka banbance wacece Nafisa wacece Safina, iyakan dai a fuska idan kakalli Nafisa zaka iya shaida ta sabida bata da fara’a ko kaɗan, miskila ce na ƙarshe saɓanin Safina ko yaushe haƙoran ta awaje suke

Murmushi Nafisa tasakar mata ganin yanda tatsare ta da idanu tana son tantance Nafisa CE ko Safinan

“Ki taso Mami na kiran ki”. Tafaɗa ahankali tana juyawa tayi hanyan ƙofa

Ɗan numfashi Halwa taja batare da ta ɗauke kanta daga kallon Nafisa ba har tafice, yanda tanuna mata ɗin tuni ta gane ba Safina bace

Miƙe wa tayi tabuɗe kayan ta taciro riga da skert na atamfa kalan Baby pink sai ratsin Milk da aka yi amfani dashi wajen zanen Flower jefi-jefi, bayan ta gama saka wa taɗau siririn gyale baƙi tayafa akanta sabida bata saka ɗan kwalin kayan ba sannan tanufi ƙofa tafice

Suna zaune gaba ɗayan su a falo, Halwa da tafito ƙasa tasamu tazauna cikin sanyin muryanta tayi wa Mami sannu

Amsawa tayi idanun ta akanta kafin takalli su Nafisa tace “ku tashi ku bamu wuri”.

Babu musu suka tashi, sai ma suka yi ƙofar fita suka fice gaba ɗaya

Juyo da idanun ta kan Halwa tayi tace “yauwa so nake yanzu ki faɗa min abunda yasa kika baro gida, ayanda nafahimta da nazarin da nayi miki hasashe na ya bani kin baro gida ne sabida wani dalili naki hakane?”

Halwa da kanta ke ƙasa ta kasa ɗago kai bare ta’amsa mata, sosai matar take bata mamaki da kuma yanda halin ta yake, kai da gani kasan ba ƙaramin jarumar mace akayi a wajen ba, dakakkiyar mata me tsananin kwarjini da baiwa..

“Kinyi shiru ina magana? bana son ina maimaita ma mutum magana biyu kinji Ni?”

Dasauri Halwa tagyaɗa mata kai cikin tsananin shakkar matar da yakamata tun ganin ta da tayi

“Ki buɗe baki kiyi min magana ba gyaɗa kai nace kiyi ba”.

Cikin rawan baki Halwa tabuɗe baki tasoma sanar mata da abinda take buƙatar ji a wajenta, iyakan abinda tasanar mata tafito gida ne sabida anyi mata aure da mijin ƴar uwanta, ganin tanuna kamar bata ji daɗi ba shine ita kuma tabi wannan hanyan don guje ma auren”.

Jinjina kai Mami tayi idanun ta kafe kan Halwa ɗin, cikin kausashshiyar murya tace “wato kin zaɓi guduwa ne don kawai ƴar uwanki bata ji daɗin wannan haɗin ba? Kin nemi ki baro iyayen ki sabida ki faranta mata ko?”

Cikin zub da hawaye Halwa tasake duƙar da kanta, cike da raunin murya tace “nayi hakan ne kawai saboda farin cikin ta, Ni bazan so in shiga rayuwanta ita da mijin ta ba, sannan zan so takasance cikin farin ciki ko dan ciwon da take fama dashi”.

Shiru ne yabiyo bayan maganar ta illa shashsheƙan kukan ta dake tashi

Wajen shuɗewar mintuna biyar kafin Mami tace “shin ke kina son Sa ko kuwa bakya son sa?”

Baki na rawa tace “Ina son sa”.

Murmushi Mami tasaki tana kaɗa ƙafafuwan ta, sai da taja lokaci kafin tace “shikenan yanzu abinda Yakamata zuwa gobe zan maida ki gida saboda babu ta yanda za’a yi in barki kibi duniya akan wannan banzan dalilin naki, idan yaso in namayar dake sai in faɗa musu su raba auren tunda baki son zama dashi, kinga babu ke babu guduwa kenan, tashi ki wuce na sallame ki”.

Jiki a sanyaye Halwa tamiƙe takoma ɗakin su Nafisa, tana shiga tazauna kan gadon tana ci gaba da tsiyayar da hawaye kamar an kunna famfo

Ba wai maganar mayar da itan bane yaɗaga mata hankali, jin cewa zata faɗa a raba auren ta da Khalil, ita ji take yi a yanzu ta gummaci tatafi da auren sa tayi ta yawo da araba auren, hakan zai saka zuciyarta tayi sanyi daga zugin da take mata na tsananin ƙaunar sa da take yi, auren Khalil akanta shi zai sa duk inda taje takasance cikin farin ciki, ko babu komi zata mutu da auren wanda tafi ƙauna fiye da ranta a yanzu ɗin atare da ita.

Ita kuma Mami murmushi tayi lokacin da Halwan tashige ɗaki, sosai aranta ta tausaya mata domin tunda take bata taɓa ganin irin wannan sadaukarwan da Halwa tayi ba, kina son mutum amma sabida farin cikin ƴar uwanki ki zaɓi rugujewar rayuwan ki gaba ɗaya akanta, gaskiya samun me hali irin Halwa da wahala, tana da kyakykyawar zuciya matuƙa, tana iya sadaukar da komi nata akan masoyi

(Hmm nace Mami don ma bakisan sauran sadaukarwan da tayi mata bane)

Mami tana zaune da ƴaƴan ta biyu Nafisa da Safina masu shekaru 16 a duniya, twins ne su kuma daga kansu bata sake haihuwa ba, mijinta babban soja ne sosai yana aiki a Kaduna

Baza ku gasgata maganar nan da ake cewa matar Soja itama Soja bane sai kun haɗu da Mami, Kai in taƙaice muku tsaurin idanun Mami da dakakkiyar zuciyar ta ta ninka na mijinta da shine ma Sojan, bata da tsoro ko kaɗan gata macece me tsayawa akan komi da yashafe ta da tsananin jarumta, bata nuna gazawar ta a komi, tana da fara’a sosai sai dai ba ta yin sa sai a inda yadace, shiyasa Nafisa a halayya ita taɗauko, sai dai ita Mami ba wai miskilanci ne da ita ba dakakkiyar macece da bata ɗaukar raini koda yaushe, wannan dalilin ne zaka ga tamkar bata cika wasa ba

Yanzu haka ita ma’aikaciyar gwamnati ne me amsar zunzurutun albashi don babba ce sosai a wajen aikin su.

         *WASHE GARI*

Wajen ƙarfe 10:00am. Mami tasaka Halwa tashirya

Dama tuni su Nafisa sun tafi school, Safina har da kukan ta jin cewa a yau ɗin Halwa zata tafi, domin sosai jinin ta yahaɗu da Halwa ɗin a kwana ɗayan nan da tayi agidan, ta ɗauke ta tamkar babban Yayarta wacce suka fito ciki ɗaya shiyasaka tasaki jiki sosai da ita, taso Mami tabar su yau dai rana ɗaya kar suje school atafi dasu kai Halwa gida, amma ina Mami taƙi yarda, daga ƙarshe ma sai da tayi kamar zata mangare Safinan kafin tatafi school da kuka

Ita kanta Halwa sosai taji ƙaunar Safinan aranta, sai bata ji daɗin yanda Mami tayi ɗin ba, sai dai bata da bakin magana iyakan nata idanu ne domin wargi ma wuri yaka samu

Bayan Halwa tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na Baƙin yadi da zanen Flower da aka yi da dack orange Colour, fitet ne rigan sai tayi Rolling da gyale me ruwan madara irin me taushin nan sosai ya rufe mata har bandage ɗin kanta

Janyo jakan tayi tafito Parlour inda Mami ke zaune tana jiran ta, kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kai tana ci gaba da latsa wayan nata

Ita dai Halwa tana nan tsaye a waje ɗaya ko ƙwaƙƙwaran motsi bata iya yi

Kamar shuɗewar mintuna goma kafin Mami tatashi tayi wa Halwa nuni da hannu alamun su je

Gaba Halwa tayi dasauri tana jan Trolly ɗin ta, koda tafita sai da tajira Mami ɗin takullo ƙofa tazo tasame ta kafin su ƙarisa wajen motan

A lokacin har me gadi ya ƙariso wajen yana kai gaisuwa wajen Mami

Amsa masa kawai tayi tana buɗe Boot

Dasauri yanufi wajen Halwa yana ƙoƙarin amsar jakan nata don yasaka mata a Boot ɗin, but Mami tatsai dashi da faɗin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button