BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

“Ƙyale ta tasaka da kanta Ali, je kabuɗe min Gate”.
“To Hajiya”. Yafaɗa dasauri yana nufan Gate ɗin
Ita kuma Halwa saka Trollyn tayi sannan Mami tarufe suka shiga motan, sai da taja motan zuwa bakin Gate ɗin kafin tatsaya tazuge glass ɗin tana kallon me gadin tace
“Ali idan su Nafisa sun dawo kace musu su duba keey ɗin a inda nasaba ajiye musu, sannan kafaɗa musu su tabbatar sun tafi islamiyya yau bazan dawo ba sai zuwa dare”.
“To Hajiya insha Allahu zan faɗa musu, Allah yadawo dake lafiya”.
“Ameen ya Allah”. Tayi maganar tana maida Glasses ɗin tarufe sannan taja motan taƙarisa fice wa.
.
_To ga fa Halwa za’a koma gida Fans, ko me zai faru?_
[1/5, 2:40 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Twenty Six*
________????Kamar yanda Halwa tafaɗa mata address ɗin gidan su Saleema can tanufa, a cikin motan babu me magana, ita dai Halwa kallon hanya kawai take yi tana kitsa abubuwa aranta da tunanin abinda zai faru idan takoma..
Ƙaran horn ɗin da Mami ta danna ne yadawo da ita hayyacin ta, takai duban ta ga Gate ɗin lokacin har me gadi ya leƙo don ganin wanene, be buɗe musu ba sai da yazo har wajen motan yayinda Mami tasauke Glasses Motan
Har ya buɗe baki da ninyan yin magana sai yahangi Halwa, cike da tsagwaron murna da al’ajabin ganin ta don zuwa yanzu har ma’aikatan gidan sun san abunda yafaru duba da yanda iyayen gidan nasu hankalin su yake a matuƙar tashe da halin da Saleeman ke ciki
Washe baki yayi yace “Hajiya Halwa ke ce?”
Murmushi tayi masa cikin sanyin murya tace “eh Yusha’u”.
“Masha Allah bari in buɗe muku ƙofan to”. Yayi maganar yana nufan Gate ɗin dasauri har da haɗa wa da gudu
Yana shiga yabuɗe musu Mami taja motan zuwa ciki
Har wajen motan me gadin yabi su bayan da yamayar da Gate ɗin yarufe, anan ne suka gaisa da Mami itama Halwa tagaishe sa sannan sukai ciki
Halwa ce agaba don haka ita tabuɗe ƙofan tashiga da sallama a bakin ta
Ummi dake zaune saman kujera ta riƙe waya a hannu tana latsawa, kallo ɗaya kayi mata zaka hango tsantsan damuwar da take ciki
Sallaman Halwan shine yasa taɗago kai sabida jin muryan da bata taɓa zaton ji ɗin ba a halin yanzu, dasauri tamiƙe ganin dai itan ce zuciyarta cike da zallan mamaki tare da wani irin murna
“Halwa..” takira sunan ta idanun ta akanta don tama kasa motsawa
Murmushi Halwa tayi takalli Mami dake bayan ta, sai kuma tasad da kanta ƙasa
Mami gaba tayi zuwa cikin parlour’n hakan yasa itama Halwa tabi bayan ta, sai da suka zauna kafin Ummi tasake samun bakin magana
“Halwa ina kika shiga ne? Ina kika shiga kika bar mu cikin neman ki?” Tayi maganar tana dawo wa kusa da Halwan tare da riƙe mata hannu
Hawaye Halwa tasoma yi, cikin rawan baki tace “don Allah ku gafarce Ni Ummi nabi son Raina na tafi na barku amma bazan sake ba”.
Washe baki Ummi tayi tana rungume ta cike da tsantsan murna, bakin ta sai faɗin “baki yi mana komi ba Halwa, baki yi mana komi ba wlh..”
Mami dai tana kallon su batare da ta furta komi ba
Tsawon mintuna biyu kafin suka nutsu har Halwan dake yin kuka
“Ummi tace tunda kika tafi Saleema taƙi lafiya, kullum cikin neman ki muke yi, yanzu ma haka tana nan ɗakina ta kwanta tana barci”.
Zumbur Halwan tamiƙe tana shirin nufan ɗakin Ummi sai taji saukar muryan Mami tana faɗin
“Oh baza ki gabatar dani bane zaki tafi ki bar ni? Tunda anga uwa dole ki manta dani”. Ta yi maganar ne fuskarta yalwace da murmushi
Juyowa Halwa tayi sai dai bata kai ga magana ba Ummi tariga ta da cewa
“Don Allah kiyi haƙuri wlh murnan ganin ta ne yaɗauke min hankali sam gashi ko gaisawa bamu yi ba”.
Murmushi Mami tayi tace “babu komi ai”.
Sannan suka gaisa kafin Mami ɗin tace “ina son ganin mahaifin ta idan babu damuwa sabida maganar da nazo dashi”.
“To babu komi bari in Kira sa”. Cewar Ummi tana ɗaukan wayan ta.
Halwa ita tuni ta shige ɗakin Ummi ganin sun manta da ita, koda tashiga Saleeman na barci kamar yanda Ummi ɗin tafaɗa, tunda tasauke idanun ta akan Saleeman hawayen ta suka sake gudu wajen fitowa, toshe bakin ta tayi ahankali tasoma takawa zuwa gadon, sai da tazauna sannan tasaka hannun ta tana shafa mata saman goshin ta cike da tsananin tausayin ta, wuni biyu kacal yasa ta wani irin mugun ramewa kai da ganin ta kasan tana jin jiki
Kasa riƙe kukan ta tayi tasoma shashsheƙan kuka duk da kuwa tana dannewa kar yafito fili
Sai dai hakan be tasiri ba don tuni kukan nata ne yatashi Saleema, ahankali tabuɗe idanun ta akayi Sa’a sai tasauke su kan Halwa da hawaye suka cika idanun ta har bata iya gani sosai sai ta rage su da hannu
Kallon ta kawai Saleema take yi batare da ta motsa ba
Sai Halwan tasakar mata murmushi cikin rawan baki tace “ƴar uwa..”
Lumshe idanuwan ta tayi tasake buɗe su akanta amma kuma bata da alaman motsawa, tsira mata idanu kawai tayi tana tunanin ko dai mafarkin da take yi ne a yanzu bata farka ba?
Sake kiran sunan ta tayi cikin sanyin murya tana cewa “Ya jikin naki?”
Sai da tasake ɗan ƙif-ƙifta idanun nata ta yanda zata tabbatar ba mafarki take yi ba, ganin dai har yanzu tana ganin Halwan sai tayi saurin tashi zaune idanun ta akanta takai hannun ta tana taɓa ta
Hakan sai yaba ma Halwa dariya don ta gane me take nufi tana kokwanton ita ce ko ba ita ba
Murmushi tayi taruƙo hannun nata da take shafa mata jiki tace “ƴar uwa Ni ce fa, na dawo gare ki ne”.
Sai kawai Saleeman tafashe da kuka tana rungume ta, cikin kukan take faɗin
“Don meyasa zaki tafi ki bar ni? Kina tunanin zan iya ci gaba da rayuwan farin ciki ne bayan kin tafi? Ƙaunar da nake miki shine zai hana Ni samun farin ciki a rayuwata, wlh da baki dawo ba bazan taɓa yafe miki ba”.
Itama Halwan kuka take yi sosai zuciyarta cike da tsananin rauni, tabbas tayi nadaman tafiya, da yanzu Mami Bata dawo da ita ba shikenan haka zata tafi tabar ƴar uwan ta cikin damuwa na rashin ta, abun da taguda ashe shine zai faru, tayi nesa dasu don farin cikin Saleeman amma kuma tafiyan nata yazama barazana ga rayuwan ta, ko kaɗan bata taɓa tunanin hakan ba, tabbas ƙaunar da Saleema take mata ya wuce tunanin ta
Sun jima ahaka kowa yaƙi sakin ɗan uwan sa, kuma basu fasa yin kukan ba sannan babu wani kalma da tasake shiga tsakanin su
Ummi ce tashigo ɗakin, ganin su ahaka sai tasaki murmushi tare da saka hannu tana share ƙwallan da yacika mata idanu, ahankali tataka wajen su cikin farin ciki tace
“To ya isa kukan haka kunji? Tunda komi ya wuce Allah yasa kin dawo sai mu gode waa Allah”.
Sakin junan su suka yi yayinda Saleema takasa dena kukan
“Please sis ki dena kukan mana kar ki saka inji na tsani kaina mana, domin idan wani abu yafaru dake bazan taɓa yafe wa kaina ba”.