BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 71 to 80 (The End)

Khalil dake faman aiki a Lapton yana jin su be saka musu baki ba, ahaka suka ci gaba da zaman, sai dai zuwa lokacin Saleema ta dena saka musu baki gaba ɗaya, numfashi kawai take sauke wa a hankali tana sake ƙanƙame Ahmad dake jikin ta, kwana biyu kenan da zuciyarta take mata zugi duk ta hana ta sukuni, sai dai bata ba da ƙofan da za’a gane wani abun na damun ta ba, don ba ta son ta tayar musu da hankali, sai ta mayar da hankalin ta kan shan maganin ta, sai dai yau gaba ɗaya jikin ta ya matsa mata tunda bata sha ba, har soma kumbura tayi wanda in ba kayi mata kallon ƙurilla ba; ba lallai kagane hakan ba

Ci je leɓen ta tayi ahankali, kafin ta buɗe idanuwan ta da zuwa yanzu sun sauya kala, sun koma kore-kore, miƙe wa take ƙoƙarin yi jikin ta na rawa tana son zame Ahmad dake kanta

Ɗago kai Halwa tayi ta kalle ta, sai kuma tayi saurin faɗin “sis meke damun ki ne wai? Lafiyan ki ƙalau kuwa?”

Sai alokacin shima Khalil yaɗago kai jin tambayan da Halwa take mata, da alamun ruɗu a muryan ta, shima dai saurin tambayar Saleeman yasoma yi ganin yanda duk ta sauya lokaci ɗaya, gashi jikin ta sai rawa yake yi tana faman cije baki, miƙe wa yayi ya koma kan kujeran yana tallabo ta yasake cewa “lafiya kuwa meke damun ki? Ko wani waje na miki ciwo ne?”

Murmushi tayi tana lumshe idanun ta kafin tace, “ban sha magani na bane yau, shine zan tashi in ɗauk..”

Be bari ta dasa Aya ba yakatse ta da faɗin “ya salam! Meyasa to? Wannan ganganci ne ai”.

Sai yaja tsaki yana faɗin “nima bansan me ya hau kaina ba yau ɗin ban tambaye ki ba, tun safe ma baki sha ba ko?”

Gyaɗa masa kai tayi kawai

Kallon Halwa yayi ransa duk babu daɗi yace, “je ki ɗauko min maganin”.

Dasauri tatashi tana zare hannun ta da tariƙe na Saleeman, ɗakin ta tawuce ta ɗauko magani ta kawo masa, sai ta koma ta ɗauko ruwa cikin Fridge tasake dawowa ta miƙa masa

Shi da kansa ya bata, sannan yace ta kwanta ta huta, idan anjima jikin babu daɗi sai su nufi asibiti

Halwan ɗaukan Ahmad tayi tamayar dashi ɗaki, don Saleeman ta samu sake wa akan kujeran.

    Gaba ɗaya sauran wunin ranan sai suka yi a rashin walwala, musamman ma Halwa da duk motsin ta yana kan Saleeman, gwara-gwara Khalil ya fita gab da magriba, kuma be dawo gidan ba sai da akayi isha’i.

       Ita kuma Halwa taliya ta girka musu me sauƙi bayan ta idar da sallan magriba, zuwa lokacin ne Saleema ta tashi, duk hankalin Halwa kacokan yana kan ta sai tambayar ta take yi ko akwai inda yake mata ciwo? Komi ita take mata

To dayake dama jikin dasauƙi, ita dai Saleema sai dai tabi ta da murmushi duk da har yanzu zuciyar ta be dena zugi da radaɗin da yake mata ba, har sanda Khalil ɗin yashigo gidan shima ya hau tambayan ta, sai dai yaji daɗin ganin ta wasai da lafiyan ta, don har hira suka koma suna yi, nan ne hankalin su ya ɗan kwanta.

    Washe gari Sunday har yamma Saleema lafiyan ta ƙalau, domin a ranan ma tafi samun lafiya fiye da jiya, sai dai da dare jiki yaƙi daɗi dole suka dangana ga asibiti.

     Duk wani makusantan su tun a daren tuni yaji labarin rashin lafiyan ta, su Ummi duk sun hallara asibitin hankalin su duk a tashe, musamman yanda suka ga likitocin sai kai komo suke yi a ɗakin da aka kwantar da Saleeman, kuma sun ƙi ce musu uffan bare su san meke wakana.

    Zuwa goman dare, lokacin wajen awanni uku da shigar da saleema sannan likitan ta ya nemi ganin su, gaba ɗaya suka ɗunguma wajen su, doctor ɗin be musu wata ƙwaƙƙwaran bayani ba, illa kwantar musu da hankali da yayi, sannan ya faɗa musu baza su samu ganin ta ba har sai gobe.

     Zuwa lokacin Halwa tasha kuka kamar zata ƙarar da hawayen ta, da zasu tafi gida cewa tayi babu inda zata je, daƙyar su Ummi suka lallaɓa ta suka koma gida har Khalil ɗin aka bar Ummi ita kaɗai, tunda su ma su Abba duk sun dawo, kowa ya tafi da fargaba a halin da Saleema take ciki.

     Zuwa washe gari tuni duk sun hallara, har lokacin dai babu wani labari daga wajen doctors, sai daga baya tukun Doctorn ya nemi gana wa dasu, dalla-dalla yayi musu bayani

Zuciyarta ta rigada ta gama kumbura har ta kai matakin da dole sai dai ko ayi mata Theater da gaggawa a cire mata a sauya mata, ko kuma tarasa ranta domin ya daina aiki gaba ɗaya

Babu wanda be girgiza ba da jin wannan zance, amma ya suka iya da ikon Allah?

Tuni anyi cuku-cukun yanda za’a samu ayi mata aikin a cikin kwana biyu, Abroad za a fitar da ita

Sai dai kuma Allah shi yafi su ƙaunar ta, a kwana na uku ranan da ake saka ran tafiya da ita, a ranan Allah ya amshi abun sa, Saleema ta amsa kiran Allah batare da ta sake shaƙan numfashin duniya ba, tunda tun lokacin da aka kawo ta komi na jikin ta ya dena aiki sai da na’ura.

     Musalta muku yanda Familyn nan suka shiga ɓata lokaci ne, domin dai alƙalami na bazai iya muku bayanin tashin hankali da ruɗun da suka kasance ba, tun a asibitin ma Halwa da Ummi suka zube ƙasa a sume, shi kansa Khalil sai da jiri ya ɗibe sa aka kwantar dashi, ga dai shi idanun sa biyu sai dai komi nasa ya dena motsi har sai da yayi kusan awanni biyu ahaka, (ma’ana yayi suman Ido buɗe ne) sosai mutuwar ta shige sa, tabbas kuka rahma ne ga bawan da yashiga ruɗin rayuwa, sai dai Khalil ya kasa samun hawayen da zai zubar don yaji daɗi da salama a zuciyar sa, wannan dalili ne yasaka zuciyar sa tayi masa nauyi fiye da tunanin mutum, be iya ma buɗe baki yayi magana kawai ya zama tamkar status ne

Itama Ummi an yi Sa’a ta farka tun a time ɗin, shi kam Abba dauriya kawai ya ara ya yafa wa kansa, but duk da haka sai da yayi ta sharan hawaye sabida ya kasa jurewa.

     Halwa dai bata farka ba har aka kai Saleema gidan ta na gaskiya, mugun hawa jinin ta yayi, kasancewar tana da hawan jini tun lokacin cikin Ahmad da aka harbi Khalil, bata farka ba sai a washe gari, sai dai duk wanda yake ɗakin a lokacin dole ne ya zubar da hawaye sabida tausayin ta, sai da Nurse suka yi mata alluran barci kafin suka samu sukuni, Dattijuwa me aikin su ita aka bari a wajen ta, tunda duk sun tafi gida karɓan gaisuwa

Sai a daren ranan ne Khalil yasha kukan sa ma’ishi, tare da raya daren don nema wa Saleema gafara wajen Allah Sarki, a zaune ya kwana a ranan, kuma koda safe be samu yayi barci ba ya tafi asibiti ganin lafiyan Halwa, bata farka ba alokacin, sai ya nufi gidan su Saleema inda anan ne ake karɓan gaisuwa.

        Sai da yamma ne aka faɗa musu ta farka, dole suka ɗunguma zuwa wajen ta

A kwana biyu kawai ta fita hayyacin ta, ga ciki da take fama dashi, gashi kuma ba’a son masu irin laluran ta da tashin hankali, amma ya aka iya, sai dai kwantar mata da hankali kawai da suke tayi tare da mata nasiha me ratsa zuciya, da kuma nuna mata yin tawakkali ga duk wani ƙaddara da yasame mu, Mom CE me ƙarfin halin mata wannan maganan, don ita Ummi ma tana gida ba da ita aka zo ba

Sai dai Halwa ta kasa barin kukan, domin ko tayi yunƙurin dena wa, da zaran ta tuna Saleema ce ta rasu sai kukan ta yadawo sabo, an yi rarrashin duniya taƙi yin shiru, dole suka zuba wa sarautar Allah ido, duk idan kukan nata ya dawo yi take yi kawai babu me tsayar da ita, sai idan ta gaji don kanta sai tayi shiru anjima ta sake dasa wa, gaba ɗaya duk ta ya mutse ta saka wa kanta ciwo na ƙarfi da yaji, domin dai sai da tayi wajen sati ɗaya a asibitin kafin a sallame ta, ga hawan jinin ta da yaƙi sauka, likitoci sun yi mata maganar hakan zai iya shafan lafiyan ta da abinda ke cikin ta amma taƙi sauraron su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button