BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 71 to 80 (The End)

Ƙamshin turaren sa shi yasanar da ita zuwan sa, juyowa tayi dai-dai lokacin da ya’iso gaban ta idanuwan su suka haɗe waje ɗaya yayinda suka sakar wa juna murmushi
Ita tasoma gaishe sa, ya’amsa mata cikin fara’a yana janyo ta jikin sa, sannan yatambayi lafiyan ta da yanda tatashi
Murmushi tayi cike da tsananin ƙaunar sa aranta ta’amsa masa da “alhmadulillah Mijina, da fatan ƴar uwata tana ƙoshin lafiya?”
Sai da ya ɗan ja numfashi idanun sa na kanta yace “Lafiya ƙalau tatashi, but yanzu ta koma barci ne”.
Narke fuska tayi tace “amma kuma baka yi Breakfast ba zaka tafi?”
“No sauri nake yi ina da aiki a Office in naje zan yi a can, ki kula min da kanki, Allah yamiki albarka”.
Yamatso da bakin sa yasakar mata kiss a libs ɗin ta, har ya janye bakin sa sai kuma yamaida yahaɗe bakin su yayi socking na tsawon sokonni biyar kafin yajanye bakin sa, idanun sa yazuba mata yana kallon ta yayinda talumshe nata idon cike da tsananin shauƙi
“I Love You so much”. Yafaɗa ahankali still yana kallon ta
Buɗe idanun ta tayi suka shige cikin nasa, yau ne ranan farko da ta iya juran kallon cikin idanun sa har na tsawon wasu mintuna batare da ta janye ba, tsantsan farin ciki ne yacika ta har takasa motsawa bare tasauke idanun nata har tafurta wani kalma
Murmushin sa me kyau yasaki yana saka hannu yaja hancin ta domin sosai yagane bata cikin tunanin ta a lokacin
Ɗan ƙifƙifta idanuwan ta tayi kafin tace “I Love You too My husband”.
Sai kuma takau da kai tana murmusawa
Hannun sa yaɗago yakalli agogo kafin yasake kallon ta yasakar mata Peck a goshi yace “na tafi Byeee ki kula kinji”.
Gyaɗa masa kai tayi sai kuma tace “Allah yatsare yadawo da kai lafiya”.
“Ameen”. Ya’amsa ta yana juyawa yafice dasauri
Ta daɗe tsaye a wajen tun fitan sa batare da tayi yunƙurin yin wani abu ba, in banda murmushi babu abinda take sakar wa, sai da tagaji don kanta kafin tajuya ga Ruwan zafin da take tafasawa, lokacin tuni ya tausa har ya gaji, dasauri tazuba citta da kanumfari a ciki, sai tasaka Lipton taƙara ruwa don ya gama ƙonewa, rufewa tayi taci gaba da sauran aiyukan ta
Cikin mintuna ƙalilan tagama komi sannan takwashe takai kan dainning, daga nan ɗaki tawuce tasillo wanka tashirya cikin jan atamfa me ratsin ruwan hanta, ɗinkin doguwar riga me hannun fanka, sosai rigan tabuɗe daga ƙasa kuma tayi mata kyau ainun, sai taɗaura ɗankwalin normal tayi Light makeup da yaƙara fito da ita sosai
Parlour tanufa da waya a kunne suna gaisawa da Ummi da takira ta.
Bata daɗe da zama ba itama Halwa tafito, har tayi wanka ta shirya cikin ƙananun kaya ????Baby Peach colourn riga da Skert, rigan me santsi ne da dogon hannu da aka saka bottles, tana da coller sannan kuma shara-shara ne domin har farar Vest ɗin da tasaka a ciki ana gani, skert ɗin kuma me Robber ne me ƙaramin tsagu ta baya dack peach colour, sai tasaka baƙin ɗankwali taɗaure kanta tare da zagaye gashin ta da ta taufke a tsakiyar kai
Masha Allah tayi kyau sosai duk da bata yi kwalliya ba, sai dai ta saka Powder da kazal a idanun ta, fuskarta sai fitar da annuri yake yi tana ƙyallin amarci, kallo ɗaya kayi mata zaka san tana cikin farin ciki da walwalan da yakasa ɓoyuwa a face ɗin ta.
Lokacin da ta’iso Saleema ta gama wayan takalle ta tana murmushi tace “Ƴar uwa kinyi kyau sosai wlh, wannan ƙamshi da kike yi haka kowa yaganki ya ga Amarya?”
Dariya Halwa tayi lokacin da tasami wuri kusa da ita tazauna tana faɗin “kai Sister ban da sharri”.
“Wlh dagaske nake yi, baki ga sai shaining kike yi ba, halan baki kalli madubi bane?” Saleema tasake faɗa tana tsatstsare ta da idanu ta sigan tsokana
Hararan ta Halwa tayi tace “Uhm to Ni dai ban gani ba gaskiya”.
Saleema tace “to ina ga idanun ki ne, amma dai bari Barrister yadawo sai ya bambance mana gaskiya, yanzu tashi muje mu yi Breakfast dama yanzu nake Shirin kiran ki”.
Tashi suka yi suka nufi wajen dainning ɗin inda Halwa tuni ta sauya hiran nasu.
Da rana da Khalil yadawo be jima ba yasake fita, sabida yace musu akwai abinda zai je yayi ba zai dawo ba sai dare, don haka su kaɗai suka zauna suka buɗe shafta suna ta hira
Da yamma sai ga Larai ta kawo Husna da Ahmad, Murna wajen Saleema kamar me, tsaban murna har rawa ta dinga yi tana shilla Ahmad tana cafewa shi kuma yana wangale mata wawulan bakin sa
Ai itama Husna sai tasaka mata kuka akan ba’a ɗaga ta ba
Me su Halwa zasu yi ita da Larai in ba dariya ba, sai suka koma tonon Saleema ɗin ganin yanda take ta nishi daƙyar taɗaga Husna dake mata kukan taɓara tana cewa “ita be ishe ta ba a ƙara ɗaga ta” yarinyan sai uban wayau kamar me
Shi dai Ahmad tunda aka kwantar dashi kan kujera wasan shi yaci gaba da yi don be san ma me suke yi ba
Basu bar Larai ta tafi ba sai da takai musu har magriba sannan tawuce gida.
[1/19, 6:29 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Twenty Nine*
________???? *ONE WEEK AGO*
Suna zazzaune akan dainning table suna yin breakfast wayan Haris tayi ƙara, sai da yakai Cofin shayin sa baki yakurɓa kafin yakalli wayan, ganin sunan Dady yafito ɓaro-ɓaro sai yayi saurin ajiye Cup ɗin yana kai hannu yaɗauki wayan tare da yin peacking yana karawa a kunne
“Aslm alaikum Dady..”
“Eh Dady ban fita ba but yanzu zan fita”.
“Ok to”.
Cire wayan yayi daga kunnen sa yaɗau tissue yana share bakin sa, be ce komi ba sai da yamiƙe yajanye kujeran da yatashi sannan ya dube su yace
“Ni zan wuce but bazan dawo ba yau sai zuwa dare insha Allahu sabida akwai inda zan je”.
Miƙe wa Zubaida tayi don ta rakasa, yayinda Fahima tayi masa adawo lafiya tana ci gaba da breakfast ɗin ta
Har bakin ƙofan Parlour takai sa kafin tamiƙa masa briafcase ɗin sa suka yi sallama yafice
Mota yahau sai Family House ɗin su domin amsa kiran Dady da yayi masa.
Bayan ya shiga da motan sa tanƙamemen gidan nasu wanda yakasance me tsananin kyau da burge wa, duk da iyayen sa kaɗai ne agidan ada, but a yanzu Daddyn nasa ya dawo da ƙannin sa biyu da iyalan su suna zaune agidan, kasancewar su kaɗai Allah yaba ma iyayen su that’s why mahaifin Haris ke ji dasu sosai, shiyasa da yadena siyasa a yanzu sai yagina wannan tanƙamemen gidan kuma yayi musu umarnin dawowa kowanne da nasa Part ɗin.
Fitowa yayi a motan yanufi cikin gidan, koda yashiga parlour’n; Daddyn sa ne da Mamyn sa zaune cikin damuwa, shi kansa Haris da yashigo ya tabbatar ba lafiya ba ganin yanda sukai tsamo-tsamo fuska duk babu walwala, gaishe su yayi suka amsa masa
Dady ne yadube sa fuskan sa da damuwa yace, “Haris”.