BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 71 to 80 (The End)

“Na’am Dady”. Ya’amsa masa ahankali yana kallon sa

Numfashi yaja kafin yace, “wacece Halwa?”

Wani irin bugawa gaban Haris yayi jin sunan Halwan, still sake tsatstsare Dadyn da idanu yayi ya kasa furta komi

“Kayi shiru ina magana?”

“Alhaji na fa faɗa maka kamar yarinyan nan ce da yayi haukan son ta har yakwanta a Hospital”. Cewar Mamy idanun ta na kan Dadyn

Jinjina kansa Daddy yayi kafin yaɗauki Envelope ɗin dake kusa dashi yamiƙa wa Haris batare da yace uffan ba

Hannu na rawa Haris yasaka hannu kamar zai amsa sai kuma yatsai da hannun nasa yana cewa “Dady menene?”

“Abun da ka shuka ne yake son bibiyan ka Harisu, ashe dama Ciki kayi wa ƴar mutane har da rabon ɗiya atsakanin ku? To ka amsa gashi nan sun maka ka a kotu domin ƙwato mata haƙƙin ta”.

Amsar Envelope ɗin yayi yaciro yasoma warware wa, sai da yagama karanta abinda ke ciki kafin yakalli Dad idanun sa cike fal da hawaye, ba komi yasaka shi shiga wannan yanayin ba sai famo masa gyambon da akayi, hakan na nufin cewa da rabon yasake ganin Halwa a rayuwarsa?

Murmushi yasaki me haɗe da hawaye, gaba ɗaya tsaban farin ciki ya kasa yin magana

Sai da Mamy tace, “Haris kayi magana mana kayi shiru, shin cikin ka ne ko kuwa?”

Cikin zumuɗi yakalli iyayen nashi yace “Wlh nawa ne, yarinyan da nake ta nema shekara da shekaru yau sai gata zan same ta cikin sauƙi, don Allah Dady kafaɗa min aina take yanzu inje inga ɗiyata, ina son ganin ta Dady har yanzu ina ƙaunar Halwa araina, Please Dady kashige min gaba wajen nema min auren ta, na yarda Wlh zan aure ta in dai sabida hakan ne zasu kai Ni kotu”.

Baki sake suke bin Haris da kallo ganin yanda yakoma kamar zautacce

“To kai ban da abun ka ina zan ga yarinyan tunda ba ita ce tazo takawo takardan ba? daga kotu aka aiko don haka sai mu jira zuwa nan da Monday ɗin kamar yanda aka rubuto, yanzu abinda zaka yi kaje wajen Brr. Musbahu kuyi magana Idan nadawo zuwa gobe sai mu san abun yi”.

Marairaice fuska Haris yayi yace, “Dady please asan yanda za’a yi anemo gidan da suke wlh bazan iya zama har zuwa Monday kafin in gansu ba”.

Mamy tace, “To ya kake so ayi ne Haris? Kabari mana zuwa goben kamar yanda Daddyn ka yafaɗa, Ni kaina tun kafin naga yarinyan naji ƙaunar ta araina, wlh Ni farin ciki nayi gwara da suka miƙa case ɗin Court adawo mana da Jikar mu kusa damu tunda cikin naka ne”.

Washe baki Haris yayi yace, “Ai Mamy nasan da cikin tun sanda iyayen ta suka kore ta, kuma na neme ta but ban same ta ba SHINE SILAN ciwo na”.

Girgiza kansa Dady yayi yace “na ga alamu ko kunyan mu baka ji Haris, don baka ji nace zan hukunta ka ba ko?”

Sunkuyar da kansa yayi yana sosa ƙeya fuskar sa cike da murmushi Mamy ma na taya sa

“To je ka wajen aiki lokaci na ƙure wa, amma kasamu ku haɗu da Brr. Musbahu kaji ko?”

“To Dady”. Haris ya’amsa masa yana miƙe wa tsaye

Sallama yayi musu yafice dasauri yana duba agogon hannun sa.

Maida idanun sa ga Mamy yayi yana cewa “kin gani ko? Abinda muka ja wa kan mu kenan silan sangarta yaron nan, da yanzu ban dena siyasa ba shikenan haka za’a ɓata min suna”.

“To ya zamu yi Alhaji? yaro ne ka haife sa yanzu baka haifi halin sa ba, Ni ina ga ko da bamu sangarta sa ba dama zanen ƙaddaran sa ne haka, gashi abinda muka rasa muna fatan samu ashe da rabon zamu samu, wlh Ni har na ɗebe tsammani akan zan ga yaran Haris”.

Murmushi Dady yayi yace “ban da abun ki duka-duka nawa Haris ɗin yake don be samu haihuwa ba har yanzu zaki cire tsammani? Ni ina ga saboda saka ran da muka yi ne shiyasa muke ƙosa wa, tunda dama matar sa ta taɓa ɓari bare muyi tunanin shine me matsalan, yanzu tunda yace “har yanzu yana ƙaunar yarinyan” kinga sai mu aura masa ita tazauna da ƴar ta, kin ga haɗo min kayana in tafi kar inyi late”.

“To shikenan Alhaji Allah yasa mu dace dai”. Tayi maganar tana miƙe wa don bin umarnin sa.

**** **** **** ***** *****

     Abun zai baku sha’awa zaman Halwa da Saleema, sun ɗau kansu tamkar ba Kishiyoyin juna ba, kamar yanda kuka san suna zaune a baya haka yanzu ɗin ma suka ci gaba da zama da junan su, su kansu suna manta cewa Miji ɗaya suke aure bare har suyi kishin juna, ƙaunar da suke wa juna ƙauna ce ta tsakani da Allah

Shi kansa Khalil yana matuƙar alfahari dasu da jindaɗin kasancewar su mata a gare shi ganin yanda suka haɗa kansu fiye da Da, komi tare suke yi basu banbanta komi a tsakanin su, baza ka taɓa gane wanene me girki ba sai idan dare yayi wajen kwana, shine Khalil zai shiga ɗakin wacce take dashi, gyaran gida, girki, komi da komi tare suke yi, zaman su sai son BARKA, sai dai muyi musu fatan ɗaurewa ahaka. ????

      Yau ma Halwa ce tatambayi Khalil ɗin zuwa gidan su, domin tayi ƙudurin zuwa musamman don ganin Mama da kuma Zainab ƙawar ta, akoda yaushe suna ranta shiyasa yau tatambaye shi

Khalil be yi mata musu ba ya amince, duk da yaso yabi su sai dai aiki sunyi masa yawa, ga cases da yake dasu ciki kuwa har da nata, yanzu be da lokacin zama agidan ma

Saleema cewa tayi zata bi ta don haka suka yi shiri tare, kaya iri ɗaya suka saka, Jan Material Less ɗinkin riga da Skert, har da Gyalen da suka saka White colour da takalmin ƙafafun su iri ɗaya ne

Tubarakallah Masha ALLAH sun yi kyau matuƙa, kallo ɗaya kayi musu zaka san hankalin su akwance yake, in banda ƙyalli da ɗaukan ido babu abinda suke yi

 

Kasancewar yau Saturday Husna bata je school ba don haka har dasu aka shirya cikin kayan su masu tsananin tsada wanda yayi musu kyau ainun, duk wanda yaga yaran sai sun bashi sha’awa

Saleema da kanta tayi musu dreving, Halwa tazauna gefen su tana riƙe da Ahmad, yayinda Husna take zaune a baya.

       Tunda suka shiga anguwan nasu Halwa take baza idanu tana kallon lungu da tsaƙo na cikin anguwan cike da tunano rayuwan ta na baya, har sanda suka kai ƙofar gidan su, gidan da tayi rayuwa aciki tare da sauyawan ƙaddaran ta

Numfashi tasauke lokacin da Saleema tatsai da motan dai-dai ƙofar gidan, fitowa suka yi gaba ɗaya yayinda Saleeman taɗauki Husna dake ta faman tsalle-tsalle

Gidan suka nufa suka shiga ciki da sallama

Wata matashiyar yarinya ne zaune tana haɗa lagwani a risho ta’amsa musu sa’ilin da taɗago kanta tana kallon su

Su ma dai kallon ta suke yi, yayinda Halwa taɗauke kanta daga gare ta tana bin gidan da kallo, gaba ɗaya an sauya gidan da sabbin abubuwa, musamman face_face da akayi wa gidan da kuma penti da akayi wa ko ina na gidan wanda ada babu shi..

Maganar budurwan ce tadawo da Halwa cikin tunanin ta tamaida idanun ta kanta, but aranta kuma tana mamakin wacece yarinyan don ita tasan ba cikin dangin su take ba bare kuma na Baba

“Ko dai matar Yaya Nura ne?” Tatambayi kanta aranta

“Ku shigo mana kun tsaya anan”. Budurwan tayi maganar lokacin da tamiƙe tana share hannayen ta ajikin zanin ta

Shigowa suka yi suka nufo ɗakin da tanuna musu wanda ada ya kasance na Baba ne, shiga suka yi da sallama budurwan na biye dasu, sai da suka zauna tukun tasake fita tashiga ɗaya ɗakin, babu jimawa sai gata da ƙaton Jug cike da ruwa aciki, ajiye musu tayi tana faɗin

“Bismillan ku”.

Babu wanda yayi ƙoƙarin ɗauka yasha a cikin su illa haɗa baki da suka yi wajen cewa “alhmadulillah mun gode”.

Yayinda Halwa taƙara da faɗin “don Allah baiwar Allah wajen Mama muka zo”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button