BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 71 to 80 (The End)

“Mama kuma? Ai babu Mama gidan nan gaskiya, ko dai Aunty Zulaiha?” Yarinyan tafaɗa idanun ta akan Halwa
Girgiza mata kai tayi tace, “ina nufin masu gidan nan na asali, but kin san yaya Nura amma?”
Shiru yarinyan tayi tana tunani, sai kuma tagirgiza kanta tace, “a’a gaskiya sai dai kunyi ɓatan kai ne, nan daga Ni sai Auntyna da Mijin ta muke zaune anan ɗin, kuma shi sunan sa Aƙilu ne ba Nura ba, babu wasu kuma dake gidan nan, amma dai abinda nasani Mijin Aunty Zulaiha siyan gidan yayi, to ban sani ba ko waɗanda kike neman su ne suka tashi kenan?”.
Murmushin yaƙe Halwa tayi bata iya cewa komi ba
Ganin haka yasa Saleema tace, “to don Allah ko kinsan inda suka koma?”
“Wlh ban sani ba”.
“To shikenan bari mu tafi mun gode”. Cewar Saleema tana miƙe wa tsaye
Itama Halwa tashi tayi suka fito waje, takalman su suka saka suka yo wajen gidan
“To yanzu ina zamu je?” Saleema tayi tambayar time ɗin da suka iso jikin motan su
Kallon ta Halwa tayi fuskarta da alamun damuwa tace, “wlh ban sani ba, Allah yasa ba wani abun bane yafaru dasu wlh hankali na ya matuƙar tashi, Nasan babu yanda za’a yi su siyar da gidan su in dai ba wani abu bane ke faruwa”.
“A’a ki dena faɗar haka, babu komi insha Allahu ki cire komi aranki kinji ko?”
Murmushi Halwa kawai tayi tana sake rungume Ahmad dake hannun ta
Saleema tace, “To ko dai zamu tambayi maƙota ne?”
“A’a muje gidan su Zainab Nasan zamu ji komi acan idan ma wani abu ya faru ne”.
Motan suka shiga suka nufi gidan su Zainab da babu nisa da nan ɗin, Saleema nayin parcking suka fito suka shiga gidan suna doka sallama tun daga zauren gidan
Umma na cikin ɗaki ta’amsa musu sallaman tana fitowa, duk da ta kalle su but bata gane Halwa ciki ba illa maraba da tayi musu tace musu “su shigo daga ciki”.
Sai da suka zauna taba su ruwa sannan suka gaishe ta
Ta’amsa cikin fara’a tana sake duban su
“Sai dai ban gane ku ba wlh, ko dai wajen Zainab kuka zo?”
Murmushi Halwa tayi tace, “laa umma Halwa ce fa, baki gane Ni ba?”
Sake kallon ta da kyau Umma tayi sai kuma tace, “oh ikon Allah Halwa kece? Wlh ban gane ki ba ko kaɗan gaba ɗaya kin sauya min, Allah Sarki ashe da rabon zamu ganki?”.
Still Murmushi Halwa take yi, tasake gaishe da Umman
Ta’amsa mata cike da fara’a tana bin ta da idanu
“ALLAH Sarki tamkar ba ke ba abin ki, waɗannan yaran naki ne?” Umma tayi maganar tana kallon Husna da talafe a jikin Halwan, yayinda Ahmad ke kan cinyan ta shima kwance
“A’a Umma ga mahaifiyar su nan”. Halwa tayi maganar tana nuna Saleema
Jinjina kanta Umma tayi tace “Masha Allah to Allah ya raya su ta farkin Gaskiya”.
“Ameen Umma, Ina Zainab ko bata nan ne?”
“Ai Zainab tayi aure kusan watanni bakwai kenan”.
Halwa cikin tsantsan farin ciki tace, “Umma yanzu Zainab tayi aure ashe? Allah Sarki ashe bazan ga auren ƙawata ba?”
Umma na murmusawa tace, “ai kam Zainab tayi aure, ai dayake babu nisa da nan ɗin da gidan ta, sai in saka yara ma sukai ki idan zaki je”.
“To umma amma naje gida ban ga su Mama ba, ko wani abun ya faru ne?”
Umma tace, “ai su Mama sun tashi tuni, ai ba anan anguwan ma suke zaune ba, Nura ya sai musu sabon gida, ashe baki sani ba?”
Murmushi Halwa tayi tana gyaɗa mata kai, kafin kuma tace, “eh umma ban sani ba wlh”.
“To kin tafi can Gombe kin ɓoye ba dole ba, ina ga kema har auren kinyi bamu da labari ko?” Umma tafaɗa cike da fara’a
Still Murmushi Halwa tayi bata ba ta amsa ba
Sai Saleema ce taba ta amsa da “Eh umma itama tayi aure ai”.
“Allah Sarki to Allah ya sanya alkhairi, bari inje maƙota in Kira yaro sai yakai ku gidan Zainab ɗin”. Umma taƙarishe maganar tana tashi tafice.
[1/20, 4:52 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Thirty*
________???? A ƙofar gidan da Zainab take aure Saleema tafaka motar ta ta kamar yanda yaron da Umma tahaɗo su dashi yace musu, fitowa suka yi tare da sallaman yaron suka shiga cikin gidan, sallama suka yi duk kan su wanda yajawo fitowar Mahaifiyar Aliyu daga ɗaki
Amsa musu tayi cikin fara’a tare da musu maraba
Halwa ce tayi mata bayanin wajen Zainab suka zo
“Allah Sarki, to ku shiga tana nan ai, ku bi tanan ne ga hanyan sasan ta nan, sannun ku da zuwa”. Still tayi maganar cike da fara’a tana sake musu sannu
Inda tanuna musu nan suka shiga, a bakin ƙofar ɗakin suka yi sallama
Zainab dake zaune a tsakar ɗakin ta, ta baje ƙafafuwa da ɗan ƙaramin cikin ta da be wuce watanni huɗu ba, yanzu ne ma yake shirin shiga na biyar ɗin, dayake ta taɓa yin ɓari, yanzun ma salat take yanka wa tana so tayi kwaɗon shi taci
Jin sallaman su yasanya tatsai da yankan tana ɗago kai ta’amsa musu tare da basu iznin shigowa
Shigowar kuwa suka yi Halwa ce a gaba
Hakan yasa Zainab tasauke idanun ta kan Halwa ɗin duk da bata gama gane ta ba, sai tawaro idanu tana son gasgata gizau ɗin da idanun ta ke mata
Lokacin tuni sun gama shigowa, yayinda Halwa kuwa kallon ta kawai take yi tana zuba murmushi, a take anan wani irin farin ciki yamamaye ta sakamakon ganin Aminiyarta wacce suka fi kowa shaƙuwa tun ƙuruciya, babu abinda ke raba su akoda yaushe har tasowar su, sai gashi rana tsaka sun rabu wanda basu sake ganin juna ba tsawon shekaru kusan biyar
“Halwa”. Zainab tafaɗa da rawan baki still itama tana bin ta da idanu batare da ta motsa daga inda take zaune ba
“Zainab ɗina”. Halwa itama tafaɗa ahankali idanun ta na kawo ruwan hawaye
Ai tuni Zainab ta yunƙura tamiƙe cikin tsananin murna ta nufo ta tarungume tana sake kiran sunan ta batare da ta furta wani kalman ba, kuka suka fashe dashi na tsananin kewar juna da farin ciki.
Saleema da tuni ta nemi waje ta zauna, Ahmad na hannun ta dayake tun shigowar su ta’amshe shi, kallon su kawai take yi cike da tsantsan tausayin su, kasancewar ta me rauni itama tuni ta soma hawaye batare da ta san tana yi ba
Sun daɗe rungume da juna suna ta sambatu da nuna kewar da sukai wa junan su, kafin kuma suka saki juna suka sami waje suka zauna, bakin su gaba ɗaya yaƙi rufuwa Cuz farin cikin da suke ji a yau ɗin
“Wlh bansan da bakin da zan iya nuna murnan da nake ciki ba da ganin ki Halwa, nayi kewar ki nayi kewar ki fiye da yanda kike tunani, tun ina saka ran dawowar ki har sai da kika saka nacire rai da ganin ki, nayi kewar ki wlh”. Zainab taƙarike maganar nata tana me share ƙwallan da yacika mata idanu
Murmushi Halwa tayi tace “kiyi haƙuri Ƙawata, kina raina bazan taɓa manta wa dake ba, naso zuwa a lokuta da dama sai dai Allah be nufa haɗuwar mu ba sai yanzu”.
Hannu Zainab tasake saka wa tashare hawayen ta, sai kuma takalli Saleema dake kallon su har yanzu ta kasa cewa uffan