BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 71 to 80 (The End)

Hakan yasa Halwa tace “Sunan ta Saleema, ƴar uwata da tamaye mini gurbin ki, da ba don ita ba ban san ya rayuwata zata koma ba, ita ce tamaye min farin cikina dana rasa abaya..”
“Haba ke kuwa kiyi shiru mana mu gaisa”. Cewar Saleema tana katse mata maganar ta
Baki a washe Zainab tagaishe ta duk da kuwa Saleeman ba wai ta basu tserayan shekaru bane, da shekara ɗaya ta girme musu
Cikin fara’a Saleeman ta’amsa cike da ƙaunar Zainab ɗin aranta
Sai da suka gama gaishe-gaishen nasu har Zainab ɗin tatashi takawo musu drinks, Ahmed ta’amsa daga hannun Saleema takoma tazauna tana faɗin
“Kema ƴar lukuta zo nan wajena”.
Husna dake maƙale jikin kujera tana jan igiyoyin kwalliyan da akayi, tataho dasauri ganin Saleema ita take kallo, dayake yarinya ce me shegen wayau ga son mutane
Ɗaukan ta Zainab tayi taɗaura saman kujeran tana cewa “Yauwa ƴan mata na, ya sunan ki?”
“Husna”. Tafaɗa tana jujjuya jikin ta cikin wasa
Kallon Husnan tayi da kyau, sai taɗago tana duban Halwa tana murmusawa tace “wlh sak irin ku ɗaya, daga gani yarinyan nan taki ce, ashe kema kinyi aure?”
Dariya kawai Halwa tayi batare da tace komi ba
Saleema ce taba ta amsa da “Eh”.
“Allah Sarki rayuwa kenan, ashe babu rabon muga auren juna, amma mun gode Allah tunda Allah ya haɗa mu da ran mu da lafiya”.
Sai kuma takalli Ahmad tace “kai kuma ya sunan ka ɗan kyakykyawa?”
Husna ce taba ta amsa da faɗin “cunan sa Ahmad, amma kincan mene Aunty Mamy take ce mici?” ( Tana nufin Halwa)
“A’a sai kin faɗa?” Zainab tafaɗa tana shafa mata kai
“Tana ce mici Amadidi”.
Dariya suka yi ban da Halwa da tayi murmushi kaɗai kana tace
“To Sarkin surutu faɗi ba’a tambaye ki ba”.
“A’a ki ƙyale ta tayi surutun ta, ai duk surutun ta baza ta kai ki ba na sani”. Cewar Zainab tana dariya
Yayinda Saleema ke taya ta, ɗan barkwanci suka taɓa na tuna baya kafin Zainab ɗin tace
“Wlh na shiga damuwa lokacin da su Mama suka faɗa min kin bi Dangin mahaifin ki Gombe, ban san meyasa naka sa yarda cewa wani abun ne yafaru dake ba, domin Ni dai har ga Allah nasan baza ki taɓa tafiya batare da kin sanar min ba”.
Murmushin takaici Halwa tasaki tuno da abinda yafaru da ita a shekarun baya, sai dai ko kaɗan baza ta taɓa iya ɓoyewa Zainab sirrin ta ba, ita ɗin Aminiyarta ta ce wacce suka shaƙu matuƙa, kuma ta san ko babu komi zata taya ta jimamin abinda yafaru da ita, don haka tagyara zaman ta tasoma bata labarin komi da komi tun tafiyan ta har zuwa yanzu, abinda ta ɓoye mata kaɗai shine haihuwar Ahmad, don ko kaɗan bata kawo shi a zancen ta ba
Sai da Zainab ta dinga share hawaye sabida tausayin ƙawarta
“Ashe abun da yafaru dake kenan? Meyasaka su Mama suka aikata miki hakan? Dama akwai ranan da zata zo su guje ki? Waɗannan wasu irin mutane ne masu baƙin hali marasa yarda da ƙaddaran Allah, tirrrr da su wlh, tun farko shiyasaka zuciyata takasa amince wa da abinda suka faɗa mana”.
Numfashi Halwa taja kana tace “Ni har yanzu ban ga laifin su ba Zainab, abinda nasani kawai shine Yaya Nura da yaƙi faɗa musu gaskiya, na tabbata wlh da ya sanar musu dole zasu yarda, har yanzu na kasa manta kalaman da Yaya Nura ya faɗa min aranan, bayan komi a gaban sa yafaru, shin meyasa ya aikata min hakan? shine abinda nake so in sani”.
“Ya kuwa zaki sani tunda maci amana ne shi, idan be faɗa musu gaskiya ba su basu san ƙaddara bane? Ko kuwa basu fi kowa sanin halin ki bane? Dama sun yi ne da gayya don su kore ki sai gashi Allah yasa baza ki taɓa muzanta ba, wlh sun bani mamaki ko a mafarki bazan taɓa yarda zasu iya juya miki baya ba”.
Haka Zainab ta dinga faɗa kamar zata ari baki, sai zagin su take yi musamman ma Nura da tafi tsanar sa a yanzu, bata dena ba sai da tayi ta gaji don kanta
Anan ne Halwa take faɗa mata tana son zuwa inda suka koma tagan su, gashi sun fito Umma bata faɗa musu ba bare su san gidan
Zainab ce mata tayi “ai Ni wlh ko na sani bazan faɗa miki ba balle ma ban sani ba, me zaki je kiyi musu tunda su suka kore ki? Wlh kar ki soma ki je tunda sun kore ki; ki bar su har abada”.
Sai anan Saleema tasaka musu baki
“A’a hakan be kamata ba, su ɗin dolen ta ne kuma makusantan ta, kar ki manta Ƙanwar mahaifiyar ta ce, ko babu komi taci darajan ta, insha Allahu zamu je ko ba yau ba, kuma duk abinda suka yi su da Allah ne ba mu da hurumin ɗaukan mataki”.
Ita dai Zainab taɓe baki tayi bata sake tanka zancen ba, sai ma sauya wa da tayi nan da nan suka ɓarke da hira, daga ƙarshe Zainab ɗin tatashi don yin musu girki, amma basu bar ta ba don tare suka shiga kichen ɗin gaba ɗayan su suka yi girkin, koda zasu ci ma a Plate ɗaya suka ci cike da nishaɗi.
Sai yamma sakaliya sannan suka baro gidan Zainab, yayinda itama tayi musu alƙawarin zuwa nan ba da jima wa ba, duk da dama Halwa ta faɗa mata zasu shiga Kotu jibi, kuma tayi mata alƙawarin zata saka Aliyu ya kawo ta Court ɗin, domin baza ayi babu ita ba.
***** ***** ****** ******
*MONDAY*
Tun ƙarfe 07:00am. Brr. Khalil yafice a gidan.
Su kuma su Halwa sai wajen ƙarfe 09:00am. Suka gama shiryawa, dayake sai ƙarfe Goma ne za’a shiga court ɗin
Husna tuni an shirya ta drever ya tafi da ita school, shi kuma Ahmad tare dashi zasu tafi yana hannun Saleema, sai da suka shiga mota ne sannan Halwa ta’amshe shi tunda Saleema ce zata tuƙa su
Direct gidan su Khalil suka wuce, saboda zasu taho tare da su Mom ne
Lokacin da suka je ba wani zama suka yi ba Mom tafito suka tafi, tunda dama ita kaɗai zata bi su, yau Monday Nazeefa na school, shima Dad yana da aiki don haka bazai samu zuwa ba
Kafin goma sun isa court ɗin, acan suka haɗu da Ummi har da Zainab da tayi musu alƙawarin zuwa
Abun mamaki kuma har da Mama da Baba da Nura a wajen, duk da Halwa bata gan su ba, su ma ɗin basu gan ta ba, amma su sun zo ne kasancewar Nura yace musu za shi ana Shari’a da uban gidan shi, shi ne Baba yace “be kamata su zauna agida ba dole su je, ko don martaba uban gidan sa tunda yayi musu halarci, a sanadiyar sa ɗan su ya sami kuɗi sosai, sannan basu da masaniyar komi akan Halwa ce wacce za’a yi Shari’an da ita
Nan kuwa basu sani ba, Haris ne yasaka shi tilas yazo, kuma yace “idan be zo ba zai iya tona masa asiri, don haka gwara yazo yaga me zai faru, be san cewa Haris wayau yayi masa ba don ya rigada ya shirya amsa duk wani tuhuma da ake musu sabida samun ƴarsa, sannan kuma ko hakan zai sa Halwa ta yafe masa har ta aure sa.
Lokacin da suka isa Halwa aka bari a baya, tana rungume da Ahmad tana shirin fitowa sai ganin Haris tayi a gaban ta
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Tafaɗa a fili sa’ilin da tayi tozali dashi
Gaban ta ne yayi matsanancin faɗuwa, sai dai bata nuna firgitan ta a fili ba, ta kai duban ta gare shi fuskarta a ɗaure tamkar bata taɓa sanin sa ba, tana shirin sake yunƙura wa tafito taji muryan sa ya daki dodon kunnen ta
“Halwa ashe zamu sake haɗuwa? Nasan bani da bakin da zan roƙe ki; ki yafe min, but duk da haka ina neman afuwar ki, wlh nayi nadaman abunda…”
“Kai da Allah dakata min”. Takatse sa da faɗin hakan tana me banka masa harara tamkar zata maƙure sa dan baƙin cikin ganin sa da jin muryan sa
“Ka ɓace min agaba ko in maka wulaƙacin da sai kayi nadaman zuwan ka duniya”.