BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 71 to 80 (The End)

Shi kansa Haris yayi mamakin furucin nata da yanda tafaɗa cikin tsananin fushi tamkar ba Halwan da ya sani ba abaya, duk da dama ta sauya masa sosai amma hakan be sa ya kasa gane ta ba, kuma yasan irin hakan take masa magana domin dai bata sauya ba a yanda ya santa

Yana shirin sake magana

taja ƙofar da ƙarfi ta rufe kanta aciki, domin dai babu yanda za’a yi tabar wajen dole sai ya matsa, ita kuma baza ta iya juran sake jin maganar sa ba, ta matuƙar tsanar sa fiye da kowa a duniya

Hannun sa ya kai zai ƙwanƙwasa Glasses Motan, sai jin murya daga bayan sa yayi, wanda ya dakatar dashi daga abinda yayi ninya

“Malam don Allah kayi haƙuri ka bar nan wajen, Halwa yanzu matar wani ne baka da hurumin da zaka iya mata magana kaji ko?”. Cewar Saleema dake tsaye gefe tana kallon duk abinda suke yi tun ɗazu

Shima dai kallon ta yayi tamkar sakarai, babu abinda ke kai kawo a zuciyar sa sai ce masa da tayi “Halwa matar wani ne”. “Kenan tayi aure?” Ya tambayi kansa batare da zai iya samun amsar ba

Be sake motsawa ba, tamkar gunki ya zama sabida ba ƙaramin taɓa sa maganar yayi ba, har be san ma a wani yanayi yake ciki ba

“Excuse me zan wuce”. Tayi maganar tana kallon sa ganin be da ninyan jirga wa

Ɗan ja baya yayi kaɗan ya matsa mata kamar wanda be da jini a jiki

Buɗe ƙofan tayi ta’amshi Ahmad daga hannun Halwa, sannan tayi mata maganar tafito

Ko kallo be ishe ta ba sanda tafito, gaba kawai tayi tabar Saleema na rufe ƙofan kafin tabiyo bayan ta

Idanu kawai ya kafa ma bayan ta hawaye na sintiri a face ɗin sa.

[1/20, 5:15 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Thirty One*

________???? Kafin Shari’an su Halwa akwai Shari’an da Khalil ya soma yi

Na wani yaro ne da yayi wa ƴar aikin gidan su fyaɗe, tun wajen watanni uku da soma Shari’ar sai yau ne ake shirin ƙarƙare shi

Kasancewar uban yaron me kuɗin gaske ne, tun a zaman farko da yaga Khalil na shirin yin nasara akan su, shi ne sanadin da ya samo ƴan daba suka je suka harbe shi, sun so su kashe sa ne gaba ɗaya sai Allah be basu Sa’a ba

Lokacin da Alh. Sheƙau (kar ku ce da Sheƙau ɗin sambisa nake yi fa lolx ????) ya basu aikin; to ya bar ƙasan ma gaba ɗaya shi da ɗan sa tunda ya samu beli, ƴan daban kuma da suka yi aikin sun tabbatar masa Khalil ya mutu duk da kuwa su ma daga baya suke jin yana da rai, sun so su sake komawa asibitin su kashe sa but a time ɗin akwai jami’an tsaro, to sai suka yi wa Alh. Sheƙau bayanin cewa sun wulla Khalil barzahu, don haka ya biya su kuɗin su sukai gaba a bin su

Sai kwanaki biyun nan suka dawo ƙasan sabida a yau ɗin za’a koma kotu a yanke hukuncin ƙarshe, sun saki jiki babu abinda zai faru tunda an kashe musu Khalil, duk da a time ɗin har da Brr. Tahir ya taya shi shari’ar, amma sun fi so su ga bayan Khalil tunda shine yadage sai ya amsar wa yarinyan haƙkin ta.

     Yau kuma da aka shiga kotu sai hankalin su yayi mummunan tashi ganin Khalil a raye be mutu ba

Shi kuwa Khalil murmushi kawai yayi yana bin su da kallo, don shi tuni ya gane Alh. Sheƙau ne ya saka a kashe shi, be faɗa ma kowa bane don baya son maganar tayi tsawo, duk da kuwa yana da hanyan da zai sa a hukunta Alh. Sheƙau komin girman sa a ƙasan kuwa, tunda yana da gwamnati a hannu, but be yi hakan ba ya ƙyale su tunda dama zargi yake yi, amma yau da ya gansu sai ya tabbatar da zargin sa

Be damu kansa ba kawai Shari’an ya gabatar, kuma cikin ikon Allah ya ƙwato wa yarinyan haƙƙin ta, inda aka yanke wa Yaron Alh. Sheƙau hukuncin zaman gidan yari na shekara 8 sakamakon kama sa da yin wa yarinya fyaɗe, kuma babu Beli, sannan kuma dole zai bada kuɗi dubu ɗari cif don nema mata magani.

     Hakan ya faranta ran mutane matuƙa, ya saka wasu kuka da hawayen su sabida tsaban farin ciki, da yawan su kuma hakan ya taɓa faruwa da yaran su, sai dai rashin samun wanda zai taimake su ba sa iya ƙwato wa ƴar su haƙƙin ta, amma kuma wannan hukuncin da aka yanke wa mutum ɗaya ya sa zuciyoyin su fari da wanke duk wani tabo da ƙuncin dake cin su

Kowa sai sanya wa Khalil albarka yake yi, tare da addu’ar gamawa da duniya lafiya, gaskiya yayi na mijin ƙoƙari, kuma samun irin su a duniyar mu masu jajircewa wajen tsayawa tsayin daka don hukunta masu laifin fyaɗe, hakan zai saka a rage yawaitan su a duniyar mu, idan suka ga ana musu hukunci to dole zasu dena abinda suke yi

Sai dai kuma matsalan al’umman mu suna jin tsoron su fito da irin wannan maganar su bayyana wa mutane don ƙwato wa ƴar su haƙƙin ta, suna ganin tamkar sun tona wa kansu asiri ne, kuma hakan zai ja musu tsangwama a wajen mutane, wannan dalilin yasaka suke ɓoye wa har a kasa hukunta masu laifin fyaɗe, su kuma hakan ke saka wa suna ci gaba da aikata laifin tunda babu abinda ake iya musu.

    Don Allah mata duk wanda hakan ya faru da ita, ya jajirce wajen ƙwato wa kansa haƙƙi, iyaye su ma su dage su tabbatar an hukunta wanda ya aikata ɗin, hakan na taimaka wa sosai wajen rage yawaitan laifukan, Allah ya ƙara tsare mu da zuri’armu baki ɗaya Ameen.

Daga wanann Shari’an ne aka shiga na su Halwa, alokacin ne Halwa da su Mama suka ga juna, sai dai babu halin magana tunda Alƙali na ciki

    Shima Nura ya ganta, sai dai ita bata ganshi ba, mamaki sosai ya cika sa ganin yanda ta sauya gaba ɗaya tamkar ba ita ba, tsananin kyan da tayi masa ma ya kasa ɗauke idanu akanta, yanayin canjin rayuwan da ta samu duk da su ma suna da rufin asiri sosai, amma kuma yanzu tana cikin daula ne dole kaga sauyawan Halwa, ga ta dama tun farko tana da kyan ta da dirin jiki, but yanzu komi nata ya sake canja wa tayi kyau matuƙa, skin ɗin ta tuni ya sake haske tare da wani irin fresh, Kai da gani kasan babu wahala a rayuwan ta, jin daɗi da kwanciyar hankali ya zauna mata, bare uwa uba tana tsaka da cin amarcin ta ne, ƙyallin amarci da Albarkan aure ya sake fito da ita.????????

 

       Koda Khalil ya tashi ya gabatar da kansa a matsayin Lauyan dake kare wacce ta kawo ƙara, komawa yayi ya zauna

Sai dai su Haris basu da lauya, domin tuni Haris yace “be buƙatar lauya a halin yanzu, ya yarda zai amsa laifin sa sannan a bashi ƴar sa”. Don haka ya ga babu amfanin ya samu Lauyan ma

Dadyn sa da Mamy basu ji daɗi ba, amma babu yanda zasu iya tunda yace “zai amsa laifin sa”.

      Brr. Khalil ne ya miƙe yafito gaban kotun bayan ya nemi iznin magana da Halwa

Fitowa tayi tatsaya a inda aka tanada don tsayawar masu amsa tambayoyi

Khalil ya tambaye ta sunan ta da sunan mahaifin ta, sannan kuma ya buƙaci ta ba ma kotu Labarin asalin abinda yafaru a ranan da mummunan ƙaddaran yafaru da ita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button