BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 71 to 80 (The End)

Tiryan-tiryan tasoma faɗa wa kotu abinda yafaru

Tsit kotun tayi ana sauraron ta, tuni masu saurin kuka da tausayi sun soma zub da hawaye, sabida sosai abinda yafaru da Halwan ya matuƙar basu tausayi

Ita kanta tana ba da labarin ne tana kuka, sabida yanda take jin ƙunci da baƙin ciki a zuciyar ta tamkar lokacin da ake keta mata haddi ne

Zina tabo ne babba ga duk wanda ya tsinci kansa a halin; dole ne ya koka, musamman waɗanda akayi musu ta ƙarfi, su kansu masu aikata wa da za su gane illa da girman laifin da suke yi, wlh wlh da har su mutu baza su dena kuka ba saboda tsoron haɗuwar su da ALLAH????, ya Allah ka kare mu da kariyan ka, bamu da wayau ko dabara ya Allah ka kare mana zuri’armu daga faɗa wa mummunan makoma. ????????

Har sanda ta dasa Aya tana shashsheƙan kuka

Khalil kallon ta kawai yake yi cike da tsantsan tausayi tare da tarin ƙaunar ta a ransa, ji yake yi tamkar yajawo kayan sa yarungume ta ya rarrashi abin sa, amma kuma babu hali ????, don haka yaja numfashi yana lashe bushashshen laɓɓan sa, cike da sanyin murya yace mata “taje ta zauna”. Sannan ya juya ya fuskanci Alƙali ya nemi iznin ganin Haris

Fitowa yayi ya tsaya inda Halwa ta tashi

Khalil kallon sa yake yi tamkar ya kama sa ya maƙure shege????, sai dai babu hali, don haka ya murtuke fuska yasoma masa tambayoyi

Babu abinda Haris ya musa a tuhuman da ake masa, sai ma ƙara wa da yayi da abinda basu sani ba, ya faɗa musu komi da yanda ya nemi taimako wajen Nura.

      

        Tirƙashi! nan ake yin ta fa, ai nan da nan kotu ta hargitse saboda jin bayanan Haris, waɗanda suka san Nura kuwa kamar su: Mama, Baba Zainab Halwa, da su Saleema, daskare wa suka yi sabida tsantsan mamaki da Al’ajabi

Halwa bata iya ko motsi ba, don ba ta tunanin kunnen ta ya jiye mata dai-dai, shiyasa tabi Nuran da kallo wanda tuni Khalil ya buƙaci ganin sa, zuba masa ido kawai tayi tana sauraron abinda zai fito daga bakin sa

Lumshe idanuwan ta tayi da suka cika da hawaye, ko kaɗan baza ta iya juran abinda yake faɗa ɗin ba, don haka tasaka hannun ta biyu ta toshe kunnuwan ta tana fashe wa da kuka me tsananin sauti

Duk mutanen wajen sai da suka kallo ta, sosai ta basu tausayi wasu har da zubar mata da hawaye

Ita kanta Saleema dake kusa da ita hawayen take zubar wa, tasaka hannu tariƙo mata nata hannayen, cikin rawan murya tasoma rarrashin ta

Halwa bata dena kukan ba, sai ma ɗaura kanta da tayi saman cinyoyin ta tasoma rerawa kamar zata shiɗe, babu abinda zuciyarta ke maimaita mata sai sunan Nura, taya hakan ma zai faru? Taya ɗan uwanta masoyin ta, wanda tafi yarda da shi a baya fiye da kowa, shine zai yi sanadin shigar ta wannan halin, meyasa? Me tayi masa?

Guduma Alƙali yabuga don hayaniyar kotun tayi yawa, tsit kake ji an yi duk da kuwa har yanzu Halwa bata dena kukan ba, amma kuma ba’a ji acikin kotun sai can wajen su

Khalil bayani ya sake yiwa kotu kafin yakoma wajen zaman sa ya zauna

Sai da Alƙali yayi rubuce-rubucen sa kafin ya ɗago yasoma yanke hukunci, hukuncin ɗaya ne aka yanke musu daga shi Nuran har Haris, domin dai basu da maraba tunda duk laifi ɗaya suka aikata, don haka an yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na shekara 8 batare da beli ba, sannan kuma dole Haris zai biya kuɗin rainon masa ɗiya da akayi, kuma bashi da damar amsar ɗiyar sa sai idan mahaifiyar sa ta amince.

   Sosai iyayen Nura suke kuka sabida abinda suka ji, tabbas yau suna nadaman abunda suka yiwa Halwa, shin da wani ido zasu kalle ta? Sun kore ta sabida gudun zubewar mutuncin su, ashe ɗan su shine SILAR KOMAI, Mama tafi kowa shiga tashin hankali, tana ganin tafi Nura ma laifi, domin abinda ta aikata wa ɗiyar ƴar uwanta yafi na Nura muni, shin ina hankalin ta yaje ne a lokacin da har ta manta wacece Halwa a wajen ta?

Suna ji suna gani aka tasa su Nura, amma ko kallon inda yake ba suyi ba, suna ji da ƙuncin dake ransu.

     Halwa kuwa sabida shiga ruɗu da kukan da take yi, tuni numfashin ta ya rabu da gangan jikin ta, ta kasa jure abinda taji, ta rasa taya ma zata ɗaura abun akan mizani, shin dama akwai ɗan uwa irin haka da zai iya cutar da ƙanwar sa sabida kuɗi?

Hankalin Khalil da su Ummi ya tashi sosai, musamman ma Saleema, ai nan da nan Khalil ya ɗauke ta ya fice da ita suka take masa baya, mutane sai kallon su suke yi kowa da tunanin da yake yi aransa

Asibiti Direct aka wuce da ita, domin a cikin su babu wanda yayi tunanin zuba mata ruwa ko zata iya farfaɗowa.

???????????????????? ???????????????????????????????? ???????????????????????? *2*

     Tuni su Halwa sun koma gida, sai dai har alokacin sun kasa gane kanta, abinda Nura yayi mata ya matuƙar saka ta a Shock, kuka kawai take yi ta kasa yin shiru

Khalil da Saleema in banda zaman rarrashi babu abinda suka zauna yi

Sukuku ta koma, gaba ɗaya ta dena walwala, to idan ɗan uwanka yayi maka haka, wanene ma bazai maka ba? Nura ya cuce ta, duk tsanar da take yi wa Haris, sai taji gaba ɗaya ma ya gushe ya koma kan Nura, tsantsan tsanar sa ne ya ɗarsu a ranta, ji take yi ta tsane sa fiye da mutuwar ta, kuma ba ta tunanin zata iya yafe masa har ta koma ga mahaliccin ta.

        Bayan kwana biyu sai ga su Mama da Baba sun zo har gida neman gafarar Halwa, kuka suke yi suna roƙon ta, yayinda itama take nata kukan tare da rungume Mama, tabbas tayi kewar iyayen nata fiye da zaton me karatu, taya zata ƙi yafe musu bayan su ne iyayen da tabuɗe idanu tagan ta tare da su? Bata taɓa kallon wasu a iyayen ta ba sai su, su ne tatashi tasani; su ne kuma suka raine ta, ko waɗanda suka haife ta bata jin su kamar su

Shiyasa tanuna farin cikin ta da ganin su, ko babu komi iyayen ta sun dawo gare ta, shekaru kusan biyar basa tare, gaskiya tayi kewar su matuƙa, kuma ko kaɗan bata kalle su da abinda ɗan su yayi mata ba.

      Mama kuwa kunya da dana-sanin abinda suka aikata mata yasa ta kasa kallon Halwan, gashi sabida son zuciyar su sun aikata babban kuskure, sai dai Allah ya yafe musu.

.

???????? ????????????????ℎ ???????? ???????????????? ???????? ???????? ???????????????? ℎ???????????? ???????????????? ???????? ???????? ????????????????, ???????????????????????? ???????????????????????????? ???????? ???????????????? ???????? ‘???????????? ???????? ???????????? ????????ka ???????????????????? ???????? ℎ???????????????? ????ℎ???????????? ???????????????????????????????? ????????, ???????????? ????????ka ???????????????? ????????, ???????????????? ???????? ???????? ???????????????????????? ???????? ???????????????????????? ℎ???????????????? ???????? ???????????????????????? ???????? ???????????????? ???????? ????????, ???????????????????? ℎ???????????????? ???????????????????????? ???????????????????????????? ????????, ????????????????ℎ ???????? ????????????????????????.

[1/20, 5:29 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

 ???????????????????????????????????? ???????????????????????????? ????????????????????????

                         ♠️

????????????????????????????:✍️ ????????

???????????????????????????? ????????????????’????????

(????????????????????ℎ ???????????????????? ???????????????????? ????????????????)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button