BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 71 to 80 (The End)

⚖
???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????
®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓
???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️
????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????
????.????.????????/
????????????????????????????????????????????????????! ????????????????????????????????????????????????????!! ????????????????????????????????????????????????????!!!
????????????????ℎ ???????? ???????????????? ???????????????? ???????? ???????? ???????????????? ???????????????????? ???????????????????????? ???????????????????????? ???????????????????????????????? ????????????. ????????????????ℎ???????? ????ℎ????????????????, ????????????????ℎ ???????? ???????????????? ???????????????? ???????????????????????? ???????????????? ???????? ???????????? ???????????????????????? ????????’???????????????????? ????????, ???????????????????????????????? ???????? ???????????? ???????? ???????????????????? ???????????????? ????????????????ℎ ???????? ???????????????? ???????????? ???????????????? ???? ???????? ????????????????ℎ.
????????????????????????????????????????
???????? ???????????????????????????????? ???????? ƴ???????? ???????????????????? ???????????????????????????????? ???????????????? ɗ????????????.
???????????????? ????????????
.
_______________________________
???????????????????????????? ???????????????????????? ????????????
________???? Bayan sati Uku da faruwan abun Hutun su Halwa ya ƙare, ta koma school yanzu bata cika zaman gida ba, tunda yanzu sauran su ɗan watanni ne su ƙarashe, karatu suke yi sosai.
Sai ga Zainab wani ranan asabar ta kawo musu ziyara, ai kuwa sun yi farin ciki matuƙa, ranan wuni suka yi hira har yamma kafin Aliyu yazo ya ɗauke ta, sun rabu cike da kewar juna
Washe gari kuma sai ga iyayen Haris sun zo wai ganin Husna, tare da matan Haris ɗin da wasu makusanta cikin Familyn su, duk da kuwa da yawan su ganin ƙwaƙwaf suka zo yi
Tarba me kyau Halwa da Saleema suka yi musu
Tunda suka zo Mamy da Daddy suka naniƙe Husna ko sakin ta sun ƙi yi, dayake har ciki Daddy yashiga, ƙaunar yarinyan sosai yashige su, yanzu basu da abunda suke tunawa sai ita, tunda yanzu ɗan su yana magarƙama, har hawaye Mamy take share wa idan ta kalli Husnan, tana jin soyayyar yarinyan sosai aranta duk da kasancewar ta shegiya, amma su suna son ta a matsayin jikar su
Sun roƙi Halwa taba su ita su tafi da ita, amma firr Halwan taƙi, sai ma faɗa musu tayi ta kyautar da ita yanzu, don haka su yi haƙuri
Babu yanda zasu yi haka suka haƙura, sai dai sun sake neman alfarman zasu riƙa ɗaukan ta tana musu hutu.
Da zasu tafi Daddy ya ajiye masu kuɗi me yawan gaske, duk da Halwa taƙi amsa, sai Khalil ne yace “ta’amsa” tukun ta amsa.
Bayan kwana biyu kuma sai ga Mamy ta sake dawowa da kaya niƙi-niƙi, wai ta kawo ma Husna ne, har da Ahmad sai da takawo mishi nashi
Ranan ma Halwa tana school daga ita har Husnan, sai Saleema da Khalil ne da shima dawowan sa kenan, sun amshi kayan tare da yin mata Godiya
Ƙin tafiya tayi, har sanda aka dawo da Husna ta ganta kafin tatafi.
Rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi babu daɗi, gashi har su Halwa sun rubuta Exams ɗin su ta ƙarshe, yanzu kuma sai jiran result.
**** ***** ***** ****
Itama Nazeefa a wannan shekaran ne tagama Secondary School ɗin ta, koda result ɗin ta yafito sai Dad yatambaye ta Aure ko karatu? Ita kuma tace masa karatu take so taci gaba, tunda har yanzu soyayyar Khalil ne aranta bata taɓa tsayawa da kowa ba, ko da tace auren take so ba ta da wanda zata iya fitar wa, kuma ba ta jin ma zata iya aure yanzu idan har ba ta cire soyayyan Khalil bane aranta, duk da tayi iyakan ƙoƙarin ta amma ta kasa manta sa, don haka ta samu Dad tafaɗa masa tana son tayi school ɗin nata ne ba’a state ɗin nan ba, ko ba komi tasan idan tayi nesa dashi zata manta shi
Dad be yi musu ba kuwa, yace mata ta zaɓa inda take so
A.B.U Zaria ta zaɓa don nan ne yafi mata, duk da kuwa bata san school ɗin ba, amma yanda take jin labarin sa tasan ba ƙaramin makaranta bane tunda yayi fice a ƙasar Nigeria.
Dad sai da yatara Sameer da Khalil ya faɗa musu komi don jin shawaran su, nan Khalil yaba da shawaran akai ta Abroad tayi acan, cikin su babu wanda yanemi ja da maganar nasa tunda suna ganin shine yakawo ta gidan, don haka shi yafi iko da ita fiye da kowa, Mom CE ma tanemi ta hana, amma kuma ganin Nazeefan tana murna sai tasaka albarka kawai ta ɓame bakin ta
Ƙasan Sudan Nazeefa ta zaɓa, domin tafi son fannin Islamic shi za ta karanta, su ma su Dad sai hakan yayi musu daɗi.
Cikin ikon Allah aka fara mata shirye-shiryen tafiyan ta, Sameer ne akan komi har sai da komi ɗin ya kammala, sai kuma tafiyan ta nan da ɗan watanni kaɗan.
*** **** **** ******* ****
Yau su Halwa sun tashi da farin cikin haihuwar Hakima ne, wajen ƙarfe 10:00am. Suka shirya suka tafi gidan Sameer ɗin
A lokacin ma tuni ƴan uwan Hakiman sun soma zuwa, kasancewar agida ta haihu, kuma lafiyan ta lau da ita da Babyn ta, wannan karon ma namiji ta haifa
“Masha Allah”. Abin da su Saleema suke ta faɗa kenan da suka ga yaron, sak Sameer basu da maraba, dayake shima Aamir ɗin Dadyn nasa yabiyo, sai yaron ya koma tamkar Aamir sanda yake ƙarami ( na kula jinin su shi da Khalil ƙarfi ne dashi lolx????)
A can suka wuni suna ta hira, Abida ma ta shige cikin su ana tayi da ita, dayake yanzu ta ajiye batun soyyayyar Khalil agefe bare tayi kishi dasu, yanzu ma haka har ta fitar da mijin aure acikin waɗanda suke zuwa wajen ta, tunda tasan wanda take so ɗin ba samun sa zata yi ba, shiyasa tayi wa kanta faɗa, wata biyu masu zuwa zasu sha biki
Har yanzu tana zaune agidan Hakiman ne, tunda iyayen su sun rasu, shine Hakima ta ɗauke ta, kuma Sameer cewa yayi shine zai mata auren.
Sai dare Khalil yazo ya wuce dasu.
To rayuwa dai haka taci gaba da tafiya, zaman su Halwa sai son BARKA, babu ruwan su da faɗa ko kishin juna, sun zama tamkar ƴan uwan juna ba kishi ne ya haɗa su ba, komi tare suke yi, shi kansa Khalil yana alfahari da samun su matsayin matan sa, babu abinda zai ce wa Allah sai godiya, farin ciki kullum sake wanzuwa yake yi agidan sa, ko wacce cikin su yana matuƙar ƙaunar ta kuma yana jin ta arai da magudanan jinin sa, babu ma wanda zai iya tantance wacce yafi so, sai dai shi Khalil ɗin yana ji aran sa yafi ƙaunar Halwa, a ganin sa fa. ????
An yi suna lafiya an gama lafiya, yaron yaci sunan mahaifin Hakima, Abdulrahman, zasu ringa ce masa Haneef.
???????????????????? ???????????? ???????????????? ????????????.
A wannan shekaran abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da zamowar Halwa cikakkiyar Lauya, yau ta amshi certificate ɗin ta
Ko wani masoyin ta yau yana taya ta farin ciki
Don haka Khalil shi da kansa ya shirya mata gagaruman walima don faranta mata
Kasancewar yanzu yayi sabon gini, zasu tashi a anguwan da suke zaune, ya tsara musu babban gida wanda ya ninka wanda suke ciki a yanzu, ko wacce da nata Part ɗin, sai dai kuma haɗe yake da babban Parlourn na su gaba ɗaya
Saura kwana biyu su tare don haka ake ta faman shirye-shirye babu kama hannun yaro, tunda abun ya haɗe musu biyu ne, ga Waliman taya Halwa zama Barrister, ga kuma Waliman koma wa sabon gida.