BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 71 to 80 (The End)

Babu abinda zasu ɗauka na tsohon gidan su, komi sabo aka sanya agidan
Mom ita ta ɗaukar musu me gyaran jiki, don tana so su fito sosai, har gida ake bin su ana musu komi, an zana musu lalli me tsananin kyau, sai aka yarfa musu kitso wanda ya sake fito dasu ainun, idan ka gansu sai ka ɗauka sabbin amare ne, sabida duk abinda ake ma Amare ƴan gata an yi musu.
A ranan tarewan suka koma can sabon gidan nasu, tare da ƴan uwa na kusa
Zuwa ƙarfe 04:00 gidan ya cika maƙil da jama’a, su Mama da Baba ma duk sun hallara gidan, iyayen Haris ma sun zo, Zainab da ƙanwar Mijin ta har da mahaifiyar sa da Umman ta ma duk sun zo, su Zaituna ma sai da suka zo mata kara
Ana fara taron su Halwa suka fito, duk kansu sun sha kyau cikin Milk ɗin Material me tsananin tsada, doguwar riga aka yi musu fitet gown, sai akayi kwalliya da ston masu ƙyalli, an yi musu Light makeup da ya ƙawata fuskar su, takalmin su da gyalen da suka yi Rolling duka kalan baƙi ne, sun yi kyau Masha Allah, ba ma zaka iya tantance wacce tafi ba a cikin su
Ƙaramin cikin Halwa ya fito ɗass yayi mata kyau matuƙa, ga haske da tasake yi sosai sabida cikin
Haka Husna da Ahmad su ma an shirya su, tubarakallah Masha Allah kowa ya gansu sai sun burge sa
Mamy tunda ta hangi Husna ta ɗauke ta tana ta nan-nan da ita.
An gudanar da taro lafiya an gama lafiya, kowa ya tafi da tarin ɗumbin kyaututtukan da aka raba
Sai dai aka bar ma su aiki da gyara gidan
Su ma su Saleema ciki suka shige, suka ɗaura alwala saboda kiran sallan magriba da aka yi, sallah suka yi suka cire kayan jikin su suka sauya da wani atamfa me ruwan kuka da ratsin ja da baƙi, ɗinkin riga da skert ne iri ɗaya komi da komi, parlour suka fito suka zauna suna hiran Waliman cike da nishaɗi
Husna da Ahmad tuni barci ya ɗauke su, Dattijuwar matar da suka ɗauka me aikin su, ita tayi musu wanka ta shirya su a kayan barcin su ta kai su ɗakin su.
Sai da aka kira sallan isha’i kafin suka tashi suka je suka gabatar suka sake dawowa.
Shima Khalil ɗin be dawo cikin gidan ba sai da yayi sallan isha’i sannan ya shigo.
.
???????????? ???????????????????? ???????????? ????????????????????????
[1/21, 1:38 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
???????????????????????????????????? ???????????????????????????? ????????????????????????
♠️
????????????????????????????:✍️ ????????
???????????????????????????? ????????????????’????????
(????????????????????ℎ ???????????????????? ???????????????????? ????????????????)
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????
®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓
???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️
????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????
????.????.????????/
????????????????????????????????????????????????????! ????????????????????????????????????????????????????!! ????????????????????????????????????????????????????!!!
????????????????ℎ ???????? ???????????????? ???????????????? ???????? ???????? ???????????????? ???????????????????? ???????????????????????? ???????????????????????? ???????????????????????????????? ????????????. ????????????????ℎ???????? ????ℎ????????????????, ????????????????ℎ ???????? ???????????????? ???????????????? ???????????????????????? ???????????????? ???????? ???????????? ???????????????????????? ????????’???????????????????? ????????, ???????????????????????????????? ???????? ???????????? ???????? ???????????????????? ???????????????? ????????????????ℎ ???????? ???????????????? ???????????? ???????????????? ???? ???????? ????????????????ℎ.
????????????????????????????????????????
???????? ???????????????????????????????? ???????? ƴ???????? ???????????????????? ???????????????????????????????? ???????????????? ɗ????????????.
???????????????? ????????????
.
_______________________________
???????????????????????????? ???????????????????????? ????????????????????
________???? Kallon su yayi duk kan su kafin ya lumshe idanun sa ya buɗe yana zuba murmushi, hannun sa ya saka acikin aljihun sa ya ciro Keeys kana ya kalle su, batare da yace uffan ba, yaja hannayen su ko wacce ya saka mata keey ɗin, be bari sun yi magana ba yace da su
“Keey ɗin mota ce, kyauta na a gare ku”.
Duk kan su ɗago keey ɗin suka yi suna murmushi cike da farin ciki, kafin kuma su rungume sa cikin tsagwaron murna suka soma masa godiya, Halwa har da hawayen ta
Hannu yasaka kawai yana shafa kansu kana yace, “to ku tashi muje ku ga motan ko”.
Babu musu suka tashi suka fice, ai kuwa motocin sun bala’in burge su, ga su masu tsada ne daga gani, na Saleema green CE, ita kuma na Halwa fara, sai da duk kan su suka shiga ciki suka dudduba sai santi suke yi, duk da Saleema ba yau ta saba yin mota ba, but kyautar mijin nata sosai ya faranta mata, kuma ji take yi kamar ma bata taɓa yin mota ba sai akan wannan
Shi Khalil ma dariya sukai ta bashi, ganin abun nasu yaƙi ci yaƙi cinye wa sai murnan santi suke masa, sai da ya ja hannun su suka yo ciki sannan suka haƙura.
Dayake ranan a ɗakin Halwa yake, ai kuwa ranan yaga gata, sosai ta zage ta faranta masa rai
Shi kansa yasan yau ya samu tukuici.
Washe gari ma haka masu zuwa taya su murna sukai ta shigowa, musamman waɗanda suke cikin anguwan, da yamma kuma suka je nuna wa su Ummi motan nasu, Saleema ita ta tuƙa nata, shi kuma Khalil ya tuƙo na Halwa, tana zaune a gefen sa, sun jima agidan har magriba kafin su wuce gidan su Khalil ɗin, can kuwa sai wajen sha ɗayan dare suka baro gidan.
Tun daga ranan kuma sai Khalil yake fita da Halwa koya mata motan, idan be samu time ba tare suke fita da Saleema tana koya mata, ahaka har aka shafe tsawon watanni biyu lokacin ta ƙware sosai, gashi ta soma aiki, duk da wajen aikin su ɗaya da Khalil, wani lokacin tare suke zuwa, bare ma yanzu da cikin ta yashiga watanni shida, so be barin ta tana tuƙi sosai, tare suke tafiya.
Itama Saleema ya buɗe mata Chamis, a shagunan dake bakin layin anguwan su anan ya kama mata hayan ɗaya, duk idan zata tafi tare da Ahmad take tafiya, duk da yanzu yayi wayo sosai babu inda ba ya yawata wa da ƙafan sa, har magana ya soma, amma ba ta barin sa agida, sosai take ƙaunar yaron koda yaushe yana liƙe da ita, shiyasa ma har ƙyuya yake dashi, don be cika yarda da kowa ba sai ita.
Yau ɗin kasancewar Asabar ne gaba ɗaya a cikin su babu wanda ya fita, suna zaune a Parlour duk kan su
Khalil da Halwa suna zaune a ƙasa sun yi baja-baja da takardu, shi ke aikin ita kuma tana taya sa, yayinda Saleema ke kwance saman dogon kujera, ta ɗaura Ahmad a jikin ta dake barci, idanun ta a lumshe suke, jefi-jefi suke ɗan taɓa hira, Husna na can gefen dainning table da kayan wasan ta, ta baza su sai yi take yi tana surutun ta.
Sosa kanta Halwa tayi da hannun da take riƙe da Bairo, sai kuma ta ɗan juya kai ta kalli Saleema tace mata “sis Wai yau naji ki so slowly ne, ko wani abun na damun ki?”
Ɗan buɗe idanun ta tayi kaɗan kafin ta saki murmushi tace, “a’a babu abinda ke damuna, yau dai kasala nake ji wlh”.