CAPTAIN RASHEED COMPLETE HAUSA NOVEL

CAPTAIN RASHEED COMPLETE HAUSA NOVEL

CAPTAIN RASHEED COMPLETE HAUSA NOVEL

Rasheed na parking motar kafin kace me har Sadiq yayi wuf ya fice daga motar a guje yayi cikin gida ,mom na parlour ya wuceta ko gaisuwa babu ,ya barta da sake baki ????, Rasheed na fitowa daga motan ,dariya ta ci shi sosai yace ” nifa bani naje na ciyo mama abinci ba don haka bazaka barni da d’aukan wannan k’aton jakar taka ba!!” Shima ya bi bayanshi yana wasa da makullin motar tasa:mrgreen:

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/9, 4:55 PM] Jeeddah ja’o????: ????☄CAPTAIN
RASHEED☄????1⃣1⃣〰1⃣5⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

Yana shiga Falo ya hangi mom zaune ,kafin ya ce komai ta riga shi da cewa ” yaya naga mai gidan nawa haka? Sunan da take k’iran Sadiq kenan dayake sunan su d’aya da Abba ,abunka da bafulatana ???? ganin Rasheed bai amsa mata ba ,ta zare glashin idon ta ,ta sake maimaita abunda ta fad’a, Rasheed da ya kusa kecewa da dariya yace babu komai mom ,daman yana fama da intestinal disorder ne , yanzu ma motarshi na chan bakin hanya ya kasa driving, yana magana yana Sosa ‘keya ,mom tayi murmushi irin nasu na manya tace its alright bari zan duba shi ” kai kawai ya girgiza mata shima ya haye sama yana dariya ,shi ba komai ke bashi dariya ba sai ,juyewa da Sadiq ya ambata????. Oh ni hauwa’u!!! da ganin Rasheed kasan rigimamme ne musamman in yana tare da friends ????‍????‍????‍????.wannan kenan!!!

☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄
GOMBE STATE????
Rana ake yi kamar me ☀ta fito daga wata silver coloured mota kirar Nissan maxima takalmin k’afarta black stilettos masu uban tsayi ta fara sauk’ar wa ta jima a haka kafin daga bisani ta fito ,wata yellow jallabiya ne a jikinta mai adon duwatsu black and white tayi rolling kanta da multicoloured gyale wanda yayi matching da kayan nata ,sai simple beaded bracelet da ta saka bak’i shima ,ba fara sosai bace amma baza’a sakaya ta a jerin bak’ak’en mata ba ,siririyar fuska gareta daga ka ganta kasan ta tashi cikin gata ,sannan kuma siririya ce ba wata k’ibar a zo a gani gareta ba sai wani shan kamshi take tana yamutsa fuska. Abuja quarters ne inda ta tsaya d’in d’aya daga cikin unguwannin da ake ji dasu a garin Gombe kenan. Juye juye take tayi kamar me neman wani abu ,chan kuma ta d’auko wayarta daga purse din dake hannun ta ta kira wata number ” hello !! Ke nifa na rasa gidan gaba d’aya na kasa gane wanne ne a ciki kawai ki fito ki kai ni!! OK toh ina jira kiyi sauri pls its sunny out here!” Abunda ta fad’a kenan ta katse wayar. Bata dad’e ba kuwa wata y’ar budurwar chocolate brown amma kyakkyawa ta fito sai washe 32 take yi:D suka dunguma suka shiga gidan tare………

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/10, 7:53 AM] Jeeddah ja’o????: ????☄CAPTAIN
RASHEED☄???? 1⃣1⃣〰1⃣5⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

     Sadiq na zaune saman mota a parking lot na gidan nasu ,Rasheed ya fito d’auke da traveling bag nashi ya kafa waya a kunne sai faman zuba yake, sai da ya iso gurin motar yace ” imtihaal zan k’ira ki anjima ,pls I’ll be on my way to Gombe state ,gobe bikin cousin d’ina ,I missed you soooo much !???? take care !” Sai ya katse wayar ,Sadiq yayi dariya yace sarkin surutun naka Mukam ta yaye mu gaba d’aya ,by the way how is she doing there in Malaysia? ” Rasheed yayi murmushi yace ” lapyarta k’alau ” nan suka shiga mota don tun safe su Inna suka tafi ,su sun tsaya sabga, yanzu karfe biyu ga uban rana amma haka suka d’auki hanya suna tafe Rasheed na zolayan shi ” Kar fa kace mu tsaya ka juye don bazan iya ba:roll:”………

    Basu suka sauk’a a garin Gombawa ba sai wajen to nine, a gajiye ko kayan su basu d’auka a mota ba suka wuce side d’in da suka saba zama in sun zo ,akayi sa’a kuwa tun isowar su Inna ta sa an share an gyara don tasan halinsu da iya tafiyan dare, daga sukayi wanka da sallar maghrib da esha ai nan suka zube sai bacci ,gwara ma Rasheed cikin dare ya koma saman gado ya kwanta amma sarkin barcin kam ko juyi bai yi ba sai da aka k’ira sallar asubah????.
   Sukayi alwala , da yake akwai wasu kayan nasu a dakin suka saka ,sai masallaci basu ma dawo cikin gidan ba sai wajen seven thirty (7:30)am, ko da suka shigo main house suka shiga don gaida y’an uwa, kakar shi Maryama wato maman Inna ita ta fara hango shi, tace toh sai kuyi ta yi nima ga jika na ta zo “:D da dariya ya karaso domin ita Inna ba k’arami aikin ta bane ta maida namiji zuwa mace and vice versa, ya zauna gefen ta yace ” me sukayi miki ne kakcy?” Abunda yake kiranta da shi kenan, ta had’e rai tace kagan su nan basa sona 6ingel am!! Tun jiya sun samu yan uwansu sun ya dani ,toh nima ga jika na ya zo ” Rasheed ya sake kwanta wa jikinta yace kwarai ma kuwa !!” Mommy Yayar Inna ne sunanta na asali zubainatu amma auna kiranta da Adda jube, akwai mutum biyu maza tsakanin ta da Inna wato maman Rasheed ,uncle Hasheem, da Hamman last born nasu kuma Goggo Aisatu. A takaice mata uku kenan maza biyu a gun mahaifiyar su. Mahaifin su ya rasu ba da dad’e wa ba. Mommy wato Adda jube ta mik’a mishi food flask dauke da p. Soup na cow tail tace ga breakfast naku sai kuje ku karya an kai muku sauran ya karb’a rai a dagule yace ” ni fa mommy madara kawai zan sha” nan mommy ta had’e rai tace ” yanzu da sassafen nan so kake inje in tatso madarar saniya ,in tafasa maka ko kuma a ina zan samu madara !! Kai dai wallahy fulatancin nan bazai kaika ko ina ba fa ,kai Sadiq tashi Kaje ka karya ka barshi in ya ji yunwa zai je ya ci ai!” Su kakcy an tab’o d’an jikalle nan tafara azalzalar mommy da masifa don kaf jikanun ta babu wanda take ji dashi kamar Rasheed. Tashi tayi da kanta ta ce ” muje ni ina da madara tun jiya yana furji yayi sanyi muje ko kindirmo kake buk’ata akwai sai wanda kayi niyya ” ya mike ya bita yana danna wayarshi ko kallon su Inna bai yi ba balle Sadiq da suka zo tare.
   Karfe goma aka d’aura auren Mujaheed cousin din Rasheed da Nusaiba Daneji. Taro akayi ba kad’an ba amma Rasheed bai ma san wainar da ake toya wa ba don tun da ya shiga gurin kakarshi bai fitoba suna chan yana ta mata hira yadda ya saba ,don shi yafi sabawa da ita akan kowa. Sadiq se k’iran wayar Rasheed yake bai san cewa mutumin ya bar wayar a cikin d’aki ba wanda yake amfani da shi kuma ko sim card babu a ciki ,don game kawai yake tayi da wayar. Wajen 10:30 tukunna ya fito yaga gida cike mak’il da jama’a da ‘kyar ya wuce ,filin gidan ma duka an d’aura canopies ana reception da sauri ya wuce ya bud’e side nasu ,yayi wanka ya kimtsa cikin farar shadda tayi mugun yi masa kyau ,ya kafa hula bak’a abunka da d’an fari ya fitar da shi sosai ,ya fito sai dube dube yake ,karaf ya had’a ido da Abba:oops: wani kallo ya watsa mar ,ya nuna masa ranshi a 6ace yake, Rasheed ya sunkuyar da kai ya nemi gurin zama bai ma san inda ya zauna ba sai da ya yi adjusting ya ga ashe ,Sadiq ne da Al’amin. Al’amin ya 6alla masa harara yace fi sabillilah har na iso ace kana chan kana shirme kamar ba bikin Mujaheed d’in ka ba ,ina ka shiga ne haka? ” Sadiq de bai ma ko kalle shi ba ,shima bai ku lashi ba don baya so ya takalo wa kanshi rigima……..

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/10, 3:43 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄???? 1⃣6⃣〰2⃣0⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

      Ana gama reception Rasheed ya mik’e don ya nemo ango ,Sadiq yace ” toh masu kaka!! Saura in Kaje hiran ka manta akwai dinner da dare kayi zamanka :roll:” Al’amin de dariya kawai yake yi don yasan hakan zata iya faruwa. Rasheed ya daka musu harara yace ” Baku ma tsaya kunga inda zani ba kun fara surutan naku ,toh Mujaheed zan nemo ,kuma I need a quite place nayi magana da Imtihaal naga missed calls nata har hud’u. Sadiq yace ” Hmmmm daga nan kuma sai gun kakcy ko?!” Bai tanka masa ba ya wuce ,su kuwa suka bushe da dariya…..

☄????☄???? Bayan sallar isha aka fara programs ,amarya da ango ansha kyau , k’awayen amarya ma haka , amaryar sai juye juye take yi da alama wata take nema ,chan wata daga k’awayen nata ta gano hakan ta zo tambayar ta ko me take buk’ata? ” Babu komai Hanan kawai banga Ilham bane ,ko ba tare muka fito bane ?” Hanan tace ” Haba amarsu ! Saikace ba kisan halin mutumiyar taki ba? Ai tana chan waje tak’i shigowa ,wata’kila in ruwan saman ya sauk’o zata shigo” kafin ta gama rufe baki kuwa aka fara ruwa…
Daidai bakin k’ofar shiga ta d’auki glass na cherry drink tana shigowa tana taku tabbas tayi stealing show d’in kam ba kad’an ba ,ankon bikin ne a jikinta kamar yadda sauran k’awayen suka sanya fushia pink da silver goggoro yau kam dai simple makeup tayi amma tayi kyau ,tahowa kawai take yi tana danna wayarta ,hannu daya ta rik’e glass cup ,suka ci karo da Rasheed da ke neman hanyar fita yana waya, duk wannan drink din ya zube a kayan shi ,gashi shadda ce fara da ita ,duk kallo ya koma kan su.
” Kai Malam baka gani ne ko kuma makaho ne kai da zaka na tafiya ba tare da ka duba inda kake tafiya ba? How arrogant!! Mtsew!!!!” Abunda ya ziyarci kunnen Rasheed kenan ,Sadiq sarkin zuciya har ya mik’e Al’amin ya hana shi , shima Rasheed din murmushi kawai yayi yana rike da inda drink d’in ya zuba ,ya fice ya barta tsaye a gurin sai tauna takeyi ,ta sake yin wata tsakin da ta ga su Sadiq sun bi bayanshi, duk da Sadiq baya son raini haka ya hak’ura ya wuce bai kulata ba ……. Haka dai aka gama dinner kowa ya watse.

      Karfe shida na safe suka yi sallama da family su kakcy har mota ta rako jikallen ta ????. Abunda yarinyar nan ta mishi yayi matuk’ar 6ata mishi rai ,shi kanshi ya rasa dalilin da yasa ya kasa tanka mata……

      Two weeks later::

  Tafe yake yana waya da mutumiyar tashi ,wato Imtihaal ,wani ‘kara da yaji wata mota tayi yasa ya katse wayar da sauri ya juya. Hayak’i duk ya karad’e gurin , saida ya washe tukunna ta fito sanye da kayan sojoji saman shi ta d’aura lab coat ta kama gashin kanta kamar doughnut ta kasa sannan ta d’aura hular soji ,Barrett a kan ,tana tafe tana waina key d’in motar da ke hannun ta. Kai tsaye ta nufi office na lieutenant….. Tabbas Rasheed ya gane fuskar ta duk da ma yau shigarta daban da na ranar dinner d’in……


  Toh fa !! Masu karatu d saga begins here!! Ni kaina bansan iyakar tsanar da Rasheed ke mata ba amma muje zuwa …….

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/11, 9:21 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄???? 2⃣1⃣〰2⃣5⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

    Wata muguwar dariya yayi ya wuce yana wayarsa ko gurin bai sake waiga wa ba. Ya shiga gida kenan bai jima ba ,wayarshi tayi ringing ya duba yaga Abba ne ,” ka shirya Kazo yanzu da sauri zamu shiga emergency meeting ,ina fatan Sadiq na tare da kai ,your presence is needed ” yes sir” !! Kawai shine amsar da ya bayar ,ya shige bathroom……

   Suna shiga defence headquarters , ya ga motar Ilham ne a gaban nasu ,kawai ya kara gudun motar da gangan ,ya buga mata bayan mota har danger motan ya fashe ,yayi wata muguwar dariya ya kau da kan motar shi ya wuce parking lot yayi parking motar shi ya barta a gurin tana ta surutai kamar mahaukaciya???? ,da gudu tabi bayan shi ta sha gaban su gashi ta tsuke cikin khaki. ” suna had’a ido ta sunkuyar da kai ,ta gane shi sosai ,gashi kuma ko a matsayi ya fita (rank). ” lapiyar ki kuwa? Kika tare min hanya ,ko dai kin tab’u ne? Sadiq kuwa bashi da aiki sai hararar ta don tun farko ya tsani yarinya , ganin bata da abun cewa yasa ta matsa suka wuce ,cikin ranta kuwa tace ” Oooo I see !! Wato rama abun da na maka kayi ko,in dai wannan ne kuwa ka d’ebo ruwan dafa kanka zan hadu da kai ne ,gani na kake yi baka san hali na ba:roll:.

       Fitowan su daga meeting ta ci karo da shi da General ma’ana Abba ,abunda ya ziyarci kunnenta shine Kalmar DAD da ya ce wa General d’in. Ta wani juya idanuwa tace ” lallai wannan yana da k’arfi ta ko wanne fanni ,wato don shi d’an General ne sai ya wulak’anta ni ko?zan yi maganin ka! ” suka wuceta suna discussion nasu ta bishi da kallo ,yayinda shima ya tsareta da ido, duk abunda ta fada kuwa Sadiq ya ji ta ,don bata san yana bayanta ba , tana juyawa ta ci karo dashi,gata da tsoro tuni ta rikice ta rasa yanda zata yi ta bud’e wata k’ofa ta shiga ta rufe k’ofa, daga waje Sadiq ya bushe da dariya yace ” tabdi yarinya kin yi gudun gara ne kuma kin tadda zago????

Office din Rasheed ta shige bata sani ba ,yana zaune yana fama da computer yaji an bud’e k’ofa a zaton shi ma Sadiq ne kawai ,sukayi ido hud’u ,idanuwan shi kadai kan bata tsoro in ya zaro su ,ta d’an daure ta juya zata fita ,yace ” come here!!! Ta juyo gami da watsa masa harara yace ” excuse me!!! Wannan kallon fa? Ta kauda kai gefe ,yayi dariya irin na mugunta ya watsa mata wasu files yace ” ki kai wad’annan wa captain Sadiq and pls hurry baby !!” Baby da ya k’irata yayi mugun bata haushi ,ganin hakan shi kuwa ya samu abin yi:D. Ta juya ta fice rik’e da files d’in.

  A kofar fita ta hango Sadiq yana faman bud’e k’ofar mota ga dukkan alamu fita zai yi ,da sauri ta nufi inda yake ,tana isa ya tada motarshi ,ya sauk’e glass d’in motar yace ” ya dai?” Ta mik’a masa files d’in ” gashi captain yace in kawo maka ” Sadiq yayi wata y’ar dariya yace ,sorry ki rik’e yanzu Ina sauri pls Kar ki 6ata min lokaci ,in na dawo sai ki bani in kuma ban dawo ba mu had’u a barracks???? ya daga glashin motar ya yi tafiyarsa ya barta anan baki a sake. Bak’in cikinta ,tun da take ba’a tab’a cin mutuncin ta haka ba. Ta juya jiki a sanyaye ,tace ,zan rama ne!!”

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/11, 4:46 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄???? 2⃣6⃣〰3⃣0⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

     Saman motar ta take a kan hanya metres kad’an daga headquarters d’in tana hango motar captain Rasheed ya danno kai kawai sai ta watsa wasu k’ananan k’usoshi a kan kwaltan ,ta ci kunu tana danna wayarta ta toshe da bak’in gilashi saboda rana da ake yi, duk da Rasheed ya ga abun da ta aikata kafin ya iso hakan bai hana shi bin hanyar ba ,kamar yadda take tsammanin gani ,tayun motar duk sun sace ,yayi parking a gefe ya jingina da motar ya fiddo wayar shi daga aljihu ya kara a kunne ya k’ira daga chan wani ya taho mishi da mota ,ya karb’a makullin sukayi wasu yan maganganu mutumin ya koma da baya ,ita kuwa tana zaune cikin mota ta shagala sai shek’a dariya take yi bata san wainar da ake toya mata ba , duk tayun motar ta Rasheed yasa Wannan sergeant d’in ya sace ,sai ji tayi tana yin k’asa, ba shiri ta fito tana ta dube dube a rikice ta rasa yadda zatayi ,ga zafin rana , ta fito ta banke k’ofar motan tana hararan Rasheed shi kuwa murmushi kawai yayi ya ja motar sa yayi gaba:D.

       Yana tafe yana cewa lallai ma yarinyar nan ain in tana cin k’asa kamata yayi ta kiyayi na shuri!! Ya sake AC yaci gaba da tuk’in shi, sai da ya isa gida ya yi wanka ,har yaci abinci ,suna hira da Inna a palour Sadiq ya kirashi yana d’agawa yaji sai dariya yake ta yi kamar mahaukaci ” kai meye haka ka k’ira mutum kuma sai dariya kake kamar sintacce? Sadiq yace yanzu naga mutumiyar taka ,tana ta faman tafiya ga rana ,kaga ni ba gida zan dawo ba da na taimaka mata” jin haka ta bawa Rasheed tausayi yace ” bari na koma na d’auko ta ,haushi take bani yarinyar ta maida ni kamar wawa ,sa’an ta.

        Tafiya take tana ta faman share gumi , duk wuyanta ya bushe gashi ba kowa ta sani a garin ba ma balle ta k’ira, motar Rasheed ce ta bullo ta tsaya a gabanta ,tana k’arasawa gurin ya bud’e k’ofar motar ba tare da ya fito ba ,ta tsaya tana ta shan kamshi, ganin ya saka hannu zai rufe yasa ta shigo ba shiri ,abun ya bashi dariya matuk’a ya girgiza kai ya tada motar. Tafiya suke babu wanda ya yi ko tari ,yasan zata ji kishirwa ,ya d’auko ruwa chilled a cooler ya bata ,kamar bazata karb’a ba kuma naga ta mik’a hannu,ta kafa kai bata sauk’e ba saida ta gama shanye ruwan???? sannan tayi relax a jikin kujerar sanyin AC na ratsa ta ta koina.

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/12, 8:33 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄???? 3⃣1⃣〰3⃣5⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

      K’ofar gidan su ya dire ta ,bud’e k’ofar motan tayi ta fice ba tare da yi masa godiya ba,shikam ya ma kasa sa key a motar balle yayi tunanin tafiya ya bita da kallo don yaga iya gudun ruwanta, har tayi nisa ta dawo kai a ‘kasa tace ” nnn… Aa  gode !” Ta fad’a ne kamar wanda aka tilastawa sai ta fad’a. A fusace ya fito a motan ,ya shak’e ta ya manneta da motan yace ” ke wace irin jahilar mace ce? I have been doing you Favour’s amma bari kiji in fad’a miki ,yau kin kaini mak’ura , a girme na fiki, amma bakisan ki girmama na gaba da ke ba ,who the hell do you think you are!!! Since from d first day I saw you naji na tsane ki !! I will give you this as a warning!! ,ki fita daga harka ta ,kar ki sake wani abu ya had’a ki dani ko da wasa don sai na miki wulak’ancin da bazaki tab’a manta shi ba har ki gama rayuwar ki!! Mark my word!!!!” Yana kai wannan ya juya ya barta a gurin ido cike da hawaye wad’anda suka kasa gangarowa har saida ya ja motarshi ya bar gurin.

       Daren ranar Ilham ko runtsawa bata yi ba ,gaba d’aya abin duniya ya dameta ,daga ta rufe ido shi take gani ,” lallai nasan ban kyauta ba , kuma gashi na kasa samun nutsuwa! ???? tabbas dole in bashi hak’uri but how? Gaskiya bazan iya giving up so easily haka ba !!!! Ilham kenan !! Ni kaina Jeeddah ja’o na ce tana da ji da kai !!!
      Karfe sha d’aya na safe Rasheed ya shigo office d’in lieutenant kawai sukayi ido hud’u da ita ,ya kauda kansa gamida mik’a wasu file’s ma lieutenant d’in yace ” ina buk’atar reports within the next five hours ,ni zanje d’auko Imtihaal  daga airport, kuma pls in har akwai wani sudden abu ka sanar da ni???? lieutenant ya Sara mishi yace ” yes sir!!”  Rasheed ya juya ya fice ,bai ko sake kallon inda take ba.

☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄

   Tafe take tana dariya rigar jikinta mai dogon hannu ne fari sai ta d’aura jacket na khaki a saman tasa wani skirt flattered bak’i ,Kyakkyawar gaske amma babu gyara ,don ita Sam a birkice take ,gashin kanta bak’i ta saka wata hula hat???? itama bak’a???? shirin de na hauka tana goye da jaka k’atuwa ,ga kuma trolley tana ja,tana hango Rasheed tsaye yana jiranta ,ta fara d’aga masa hannu tun daga nesa ta rugo da gudu ta k’araso inda yake ,ya ja hancin ta yace ” welcome home my precious!! ” abunda yake kiranta da shi kenan ya kama mata kayan suka fice daga airport sai barracks!!
       Imtihaal akwai kyau ba na wasa ba a haske kuwa ta fi Ilham sosai ,saidai babu tsari a mode of dressing, yadda taga dama haka take shirinta kuma ga zafin zuciya musamman in aka mata dariya akan shigarta , kaf barrack babu wanda ya yi mata farin sani sai Rasheed don duk kusan d’abiun su d’aya ne, duk da ya fita nesa ba kusa ba. Saidai mace ce mai son murmushi ,da kuma bada dariya ,in har kana cikin 6acin rai tazo gunka toh har mantawa zakayi ma, sojojin nan babu wanda kuma baya shakkar ta da kuma 6acin ranta don baza su ga da kyau ba in har hakan ta kasance, in kuma tana tare da Rasheed shi kanshi rigimamme yake zama ???? don tun asali dama rigimammun ne cliq nasu su hud’u ita da Rasheed sai Sadiq sarkin zuciya sai kuma Air force officer wato Al’amin, shi da yake ba a nan yake ba zuwa yake yi in ya samu tym…….

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/12, 12:29 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄???? 3⃣6⃣〰4⃣0⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

      Hirar su suke ta shek’a wa har suka iso gida ,ita y’ar gidan major ne kuma abokanai ne da Abba wato General, itama soja ce amma ta fannin bincike,Babu kuma wani wanda ya kaita k’warewa a Wannan fannin ,saboda haka ne ma ta fita Malaysia don karanta psychology and was successful! Babu abunda ya fi soyuwa a zuciyar ta irin Rasheed duk da shi kawai ya d’auke tane a matsayin best friend nashi wanda babu wanda ya kaita kusanci da shi ,ko su Sadiq ma basu san wani halin Rasheed yadda ta sani ba.

      Bayan ta huta, karfe hud’u na yamma ta fito zata gurin Rasheed ,ta saka wani over size Jean’s trouser blue, da wata rigarta shirt light blue takalmin k’afarta sneekers ne blue da fari, ta kafa irin hular nan me kama da na sanyi????????, hannun ta rik’e da wayarta ta saka dayan kuma a aljihun ta babu abunda ya dameta tafiyarta kawai take yi, horn d’in motar da taji a bayanta yasa ta juya ,Rasheed ne cikin motar Army ,ya ja birki ya tsaya kusa da ita yana murmushi ,yace ” hop in!! ” ma’ana ta shigo motar , shiganta ke da wuya ,sai ga Ilham ta iso ,ta d’an Kwankwasa glass d’in motar ,bai wani damu ba ya sauk’ar don jin da wacce ta zo yau kuma. “Nazo ne in baka hakuri captain, I know I was wrong since from d very beginning, pls accept my apology” murmushi kawai Rasheed yayi ya d’aga glass d’in motar shi yayi gaba ya barta nan tsaye jiki a sanyaye. “Bro Wai waye wancan d’in” tambayar da Imtihaal ta fara jefan shi da shi kenan, yace ” don’t mind her precious! Bata da tarbiyya ne kwata kwata ,I want her to learn some morales☺ suna tafiya yana bata labarin abunda ya faru tsakanin shi da Ilham. Ta d’an yi murmushi tace ” forget that nutty girl and let’s have some ice cream???? yayi parking suka tsaya shan ice cream har kusan magariba sannan suka dawo,ya ajiye Imtihaal a k’ofar su sannan ya koma gida ,yana zuwa bakin gate nasu abun da ya gani ya bashi mamaki ???? da kuma haushi……

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/13, 9:50 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄????4⃣1⃣〰4⃣5⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

    Wai ke wace irin jarababbiyar mace ce? Abunda Rasheed ya fara furtawa kenan ,Ilham tayi murmushi tace ” captain nifa bazan bar gurin nan ba in har am not convinced kayi accepting apology na ba! I told you am d one who made d mistake,kuma na gyara kum………. Kafin ta k’arasa yayi murmushi yace “Fine!! Apology accepted little miss you may now take your leave(zaki iya tafiya) tayi murmushi tace ” thanks for that,ta juya ta nufi hanyar gida ,yana tsaye yana kallonta ,yadda take tafiya ma kad’ai abun kallo ne ,ya rasa gane yadda akayi tsanarta tabar zuciyar shi, yayi giving up so easily,yarinyar tana neman shiga zuciyar shi ne tabbas kuma duk yadda yayi ya kawar da tunanin ta a wannan dare sai ya kasa.
     Bangaren Ilham ma dai hakan take domin kuwa ya dad’e da samun mafaka a zuciyarta ,wannan kuma shine karo na farko da hakan ta faru da ita.

   A kwana a tashi yau kwanan su biyar da zama friends ,tunanin Rasheed duk ya gushe gaba d’aya tym d’in da ya saba bawa Imtihaal ya koma kan Ilham, shi a iya sanin shi Imtihaal friend nashi ce bai san ita a zuciyarta ya fi hakan ba ,Sadiq da Al’amin kad’ai suka san hakan ,suma ba don ta sanar da su ba sai don wani takardanta da suka gani ta manta a motan su ,duk wani feelings nata akan Rasheed ta rubuta. Sadiq tun da yaga yanda suka fara shakuwa da Ilham yasan akwai matsala babba ba kad’an ba.

    Rasheed na zaune a office nashi shi da Ilham suna hirarsu Imtihaal ta shigo da murmushin ta ,amma tana ganin Ilham ta turnuk’e fuska ta k’arasa ciki rai a dagule duk ta rasa abun da ke mata dad’i. ” precious! Tun d’azu nake so in k’ira ki muka tsaya hira!” Cewar Rasheed kenan. Ba tare da ta saurare shi ba ta d’auki wasu files da ta ke saman table nashi ta fice, ya bita da kallo cike da mamaki, bud’ar bakin Ilham tace ” k’anwar ka kamar bata sona! Yayi murmushi yace ” she’s my best friend” Ilham ta d’an juya ido tace ” oh I see, am sorry! ” ya ce no it’s ok she’s more like a sister to me,kuma ba bata sonki bane ,hala an 6ata mata rai ne, kinga its almost lunch time ,muje mu ci abinci mana” Ilham tayi murmushi ta mik’e suka fita tare.
      Tun fitar Imtihaal ta ke kuka har takai office nata ,Sadiq yaga wucewar ta har zai tsokane ta yaga halin da take ciki sai ya fasa ya nufi office din Rasheed ,ganin shi da Ilham ya bashi haushi ,ya juya ya tafi ,Rasheed zai k’ira shi yaga ya juya shiyasa ya kyale shi. Imtihaal ta gama aikace aikacen da zata yi a office ta fice,tana fita a motarta su kuma suna dawowa suka yi ido hud’u da Rasheed amma ta d’auke kai ,abunda bata saba ba. Though abun ya d’aure mashi kai amma ya wuce itama ta wuce. Daidai inda zaiyi parking Sadiq kuma yana mota shima zai fita ,duk da sun had’a ido ,ya ja motarshi ya fice da ya lura cewa Rasheed gurin shi zai zo……………

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/13, 3:01 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄???? 4⃣6⃣〰5⃣0⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

       Wutar d’akin dim light ne kalar blue hakan ya k’ara kyau a d’akin ,Kwance take tana danna laptop nata ,ta kifa ciki a kan pillow ta rungume teddy bear da hannun ta na hagu ,gashin kanta kuwa a kitse yake ya biyo ta wuyanta ,duk da ma ba wani tsayi ne da shi na sosai ba ,saidai ya kusa kirjin ta, hawayen idonta ne ya gangaro ya d’iga a kan wata takarda da ke gaban ta kusa da system din. Tana cikin wannan halin wayarta tayi k’ara, sunan Rasheed da ta gani ne yasa ta ajiye wayar ya kira har kusan sau shida yaji shiru ,kuma tabbas ya san ba bacci take yi ba sai ya hak’ura. Kira na bakwai ta d’aga wayar zata wurga gefe sai ta lura ba Rasheed bane ,K’awarta ne Rukayyah kaxs tana zama Kaduna ,ita kuma ta karanci cosmetology (karatun duk wani abun da ya shafi kwalliya)a London bata ma dad’e da dawowa ba. Imtihaal ta share hawayen fuskarta sannan ta d’aga wayar ,suka sha hirar su Ruky tace mata zata zo Abuja next week, Imtihaal cikin murna sukayi sallama da Ruky kaxs sannan ta kwanta. Rasheed kuwa bayan nan ma yayi ta trying number busy har ya gaji ya bari ,shi Sam ya kasa gane matsalar Imtihaal dat day…….

    K’arfe takwas na safe ta fito daga chan nesa ta hango Rasheed da murnan ta ta nufi wajen shi don ta fara surprising nashi saboda yau ne birthday nashi da gudun ta takarasa tana d’aga masa hannu. Rasheed ma ya mik’e yana murmushi ,ya daga hannu yana waving sai da ta k’arasa gurin da yake tsaye kawai taga ashe ba ma ita yake gani ba ,da Ilham yake jiki a sanyaye ta juya da gift din hannun ta ta nufi hanyar gida ,sai Lokacin da ta juya kawai ya ganta ,kafin ya tsayar da ita Ilham ta shiga gaban shi tace ” Happy birthday captain!!! Gami da mik’a masa wani box an yi wrapping. Yayi murmushi yace ” thank you ” Ilham ta kauda kai tana wata murmushi wanda na kasa ganewa munafurci ne ko kuma me????………

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/13, 9:23 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄???? 5⃣1⃣〰5⃣5⃣
Na ????Jeedah ja’o????

         Har aka kusa gama celebration na birthday party nashi Imtihaal bata zo ba ,yayi k’iran har ya gaji, tun da Imtihaal ta taso bata tab’a fashin zuwa wani occasion da ya shafe shi ba tun ma bata san ciwon kanta ba ,amma yau kad’ai tayi breaking record. A gajiye suka koma gida shi da Sadiq da Al’amin don shi ma ya zo ,  Rasheed ya zauna bakin gado yana Kallonsu suna ta hidimomin gaban su, guys ko wani zai fad’a min abun da ke damun My precious!!!?  Sai da yayi tambayar har kusan sau uku sannan suka dubi inda yake ma ,Sadiq yayi k’arfin hali yace ” banda abunka Rasheed ina zamu sani tunda duk a tare muke da kai? Al’amin yayi murmushi yace ai se Kaje ka tambayeta lover boy !! Ko ba haka bane??” Duk suka yi kwanciyar su suka kyaleshi a gurin. Yaji zuciyar shi ta kasa danne wa kawai ya sa riganshi ya fice yasan inda zai sameta a wannan lokacin saboda haka ya wuce kai tsaye zuwa wajen da suka saba shan iska ta bayan wani lalataccen motar yak’i ,tun suna yara a nan suka saba zama lokacin zafi ko lokacin wasannin su ,gurin ya zame musu tamkar gida don wataran Imtihaal har bacci take yi a gurin.
      Zama Yayi a gefen ta yace” Haba my precious!! Can’t you tell me what wrong I have done to you da zan yi deserving such a punishment? ” wani mahaukacin kallo ta watsa masa ta mike tsaye,ba shiri shima ta mik’e.” Haba don Allah! Yanzu saboda Allah ni nake punishing naka ko kuma kai kake azabtar da zuciya ta ? Tun da ka samu Ilham na zama kamar kashi a gurin ka ,ka yada friendship namu, ka manta da ni , you don’t even come over to say sorry !! Now tell me ,ka fad’a min tsakanina da kai wa yake wahalar da wani ? In da kasan akwai wata wanda matsayin ta zai fi  nawa da baka sa ni a ranka yadda zan kasa daurewa ba!!!” Rasheed cikin mamaki ya ce ” Ban fahimce ki ba Imtihaal, what are you trying to say?!!me kuma ya kawo wannan maganar? Imtihaal na zaci mu best friends ne kawai?!!” Cikin hawaye Imtihaal tace ” Best friends kawai!!? Did you know how much I go tru when I see you roaming about with that bloody bitch you call Ilham??!! Did you know how much pain it got me into ??” Rasheed ya daka mata tsawa yace WHY!!WHY DID YOU FEEL THIS WAY IF I ONLY SEE YOU AS MY BEST FRIEND??!!!! cikin razana da k’arfin hali tace “Because I LUV YOU RASHEED!! DATS WHY!!!” Rasheed yayi k’asa ‘kasa da murya ya ce ” am sorry Imtihaal ,ban san yaushe hakan ta faru da ke ba ,koma yaushe ne I can’t lie to you ban d’auke ki a matsayin wata abar ba sai a matsayin abokiya ta wanda muka taso tun yarinta , I am in luv with Ilham na zaci kece ta farko da zaki nuna farin cikin ki akan hakan but sai na samu akasin haka, am sorry Imtihaal bana ganin hakan zai d’aure a tsakanin mu ,pls ki tsaya a limit naki as my best friend. Ko kin manta cewa kikayi kin min alk’awari in dai abu zai sa ni farin ciki toh kece kan gaba a nema min shi? My precious Ilham na d’aya daga cikin su ,I loved her so much am sorry my precious. Yana kai Wannan bata saurari me zai fad’a a gaba ba ta ruga a guje ta yi cikin gida yayinda shi kuma ya bi bayanta da kallo har ta 6ace ,ya juya shima zai koma gida ya ci karo da su Al’amin suma cikin k’walla. Ya wuce su ba tare da ya furta ko kalma d’aya ba ya shige gida. Hannun Sadiq rik’e da wannan takardan da Imtihaal ta dad’e tana bayyana soyayyar ta ga Rasheed a ciki…

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/14, 6:25 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄???? 5⃣6⃣〰6⃣0⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

       Daren nan babu wanda ya runtsa a cikin su, ba ita Imtihaal ba har Rasheed, Sadiq, da kuma Al’amin! Da sassafe Imtihaal ta fita aiki yau, shirin ta de yadda ta saba ne yau kam ko d’an kwallin ma da ta saba sawa bata saka ba ,idon a kod’e ta fito.
  Ya kai kusan minti talatin yana tsaye a bakin office nata  yana ganin halin da ta ke ciki ,jiya kad’ai amma yau bazaka d’auketa a sisi ba ,k’arasawa ya kasa yi don ya fi so tayi kukan ko zata d’an samu relief, a hankali Sadiq ya fice ya rufo mata k’ofar,shi kanshi ya mugun tausaya wa baiwar Allah, kuma da yana da hali ko ikon sa Rasheed yayi da ya saka ya aureta ko baya so.

   Tun daga wannan ranar Rasheed ya daina sa Imtihaal a ido ,duk guraren da yasan zai ganta ma baya samun ta, ta 6angarenshi komai yana tafiya yadda yake so soyayyar su sai ‘kara girma take shida Ilham. Sadiq kuwa baya wani shiga harkarshi sosai balle kuma Al’amin da baya ma gida ya koma aiki……

         Tana Kwance a Falo ta k’urawa TV ido duk da ma bata san me suke yi ba don hankalin ta baya jikinta Sam,ta shiga wata duniyar tunanin ta daban, knocking d’in k’ofa da akayi ne ya sa ta dawo hayyacin ta wannan ma har me bugawan ya gaji da bugun, da sauri ta tashi ta bud’e k’ofar tana share d’an hawayen da ke fuskar ta.

Rukey kaxs ce tsaye da y’ar jakar ta a hannu an sha kyau, abunka cosmetologist???? ta shigo sai azalzalar Imtihaal take yi da masifa Wai ta barta tana ta knocking sai yatsun ta sunyi ciwo. Imtihaal tayi murmushin dole tace my ‘kawas kenan yi hak’uri ban ji ki bane shiyasa ” a take Ruky ta gane Imtihaal is off mood ,Tace “k’awata me ke damun ki ne haka gaba d’aya kin rame kin chanza ,ke matsalata da ke ko dan powder baki san ki shafa ba???? , bama wannan ba pls tell me me ke damun ki ne??

  Imtihaal ta rungume Ruky tana ta kuka sai da tayi mai isarta sannan ta kwashe labarin komai ta fad’a mata ,Ruky ta tausaya mata sosai domin itama shaida ce yadda Imtihaal ke matuk’ar k’aunar Rasheed ,a iya sanin ta kusan shekaru goma yanzu kenan. Ruky tayi murmushi na takaici tace kar ki damu k’awata!! If it is your destiny to Marry Rasheed ko ta wane hali ne zai aureki in kuma ba haka bane babu yadda zakuyi ko da kuwa yana son ki ,amma kafin nan ,ina so ki nuna min wannan Ilham d’in in gani ,zan ga me ya gani tattare da ita da har zai ‘ki  ki duk yadda kukai matuk’ar shak’uwa!!  Imtihaal ta share hawayen fuskar ta tace yanzu dai my dear tashi Kije kiyi freshening up ,gacan abinci a dining sai kici ki huta kafin magariba tayi. Ruky ta mik’e ta shiga ciki itama duk ranta a dagule don haka kawai jinin su ya had’u da Imtihaal jin ta takeyi kamar yar uwarta na Jini…….

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/18, 6:05 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄???? 6⃣1⃣〰6⃣5⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

        Tafiya suke suna shek’a hirarsu irin ta yaushe gamo ita da Ruky kaxs, suka hango Rasheed tsaye yana waya da ta fuskanci ya hango su har ma ya fara tahowa kawai suka koma suka shige mota, duk ranshi a dagule ya bi motar tasu da kallo cike da mamakin precious d’in shi ,bai yi zaton akwai abunda zai rabasu cikin sauk’i haka ba ,saidai kash!!! Bai san halin da zuciyar ta ta shiga ba dalilin shi ,shi a ganin shi zata yi supporting soyayyar shi da Ilham ta mance da soyayyar ta a gareshi wanda hakan ba mai yiwu wa bane Sam, Rasheed bai san me so yake nufi ba bai kuma iya babanta tsakanin so da kuma k’auna ba!!”

  Rukey kaxs tace , Haba ‘kawas ban ga abunda wannan Ilham din ta fiki da shi ba, kyau? Matsayi? Ko kuma me? In ma akwai bai wuce na wanka da take d’auka ba kuma nasan hakan ne zai ja hankalinshi zuwa gareta in ba haka ba menene? Gaskiya dole ki bar irin wannan shigar hauka da kike yi ,ki duba fa ki gani kwata kwata ko d’an gyaran gashin nan ma bakya yi kema ki fita a matsayin ki na mace me class! Ni na tabbata Rasheed na k’aunar ki ,bai iya banbance tsakanin kauna da kuma so ba , da wani ne bazai ma damu ya dinga kiranki duk da bakya d’aga wa kuma in ya ganki ya nufi inda kike ba! Ina tabbatar miki kawai saita mishi zama zamuyi sai ya dawo hankalin shi. Imtihaal tayi murmushi kawai ta shiga d’aki.
         Satin Imtihaal d’aya tare da Ruky suka yi shirin tafiya India don attending auren wata friend nasu RASIKA CHANDRA wanda sukayi schl tare a Malaysia da imtihaal duk da ma Ruky bata Santa ba don a London tayi nata karatun amma zata rakata. Suka yi sallama da mutanen gida driver ya kaisu har airport basu wani dad’e ba jirgin Yayi take off ????sai ????????

      Rasheed ya gaji da trying numbern Imtihaal shiru tun yana zaune ya mik’e tsaye daga bisani ya wurgar da wayar ya dafe kanshi, hakan yayi daidai da shigowar Ilham yau itace d’auke da files din da Imtihaal ta saba kawowa,ya dubeta sama da kasa yace ” ina my precious na ganki da files haka?” Tayi murmushi tace En… Bata nan ne ,sun jj eee India dazu suka shine Major yayi assigning d’ina kafin ta dawo don zata kai at least three weeks a can.
Rasheed ya mik’e a fusace yace why won’t my precious even inform me about that?? ” yayi maganar cikin 6acin rai ya karb’i files d’in daga hannun Ilham yace ” pls zaki iya tafiyah gami da nuna mata k’ofa ” cike da mamaki da takaici ta juya ta fita ba musu ta rufo mishi k’ofa . a cikin ranta tace “wato har yanzu bai cire ranshi a kan yarinyan nan ba ko? Amma ba komai na lashi takobi bazan sake na koma ruwa ba har da me tafini da zai wani damu da ita haka ? Kazama da ita!!!:roll:”

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/19, 8:39 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN
RASHEED☄???? 6⃣6⃣〰7⃣0⃣
Na ????Jeeddah ja’o????

        Satin su uku a India su Imtihaal suka yi haramar dawowa Nigeria , cikin wadannan satikai kuwa haukacewa ne kad’ai Rasheed bai yi ba ya rasa gane meyasa ya kasa fitar da Imtihaal a zuciyar shi, duk da dai yana son Ilham ne kad’ai,Sadiq de ya zuba mishi ido ne don ya tabbata Rasheed bai san me ake nufi da asalin k’auna ba!!

       Taku take irin na k’asaita d’aya bayan d’aya take sauk’owa daga benen takalmin k’afarta blue mai tsini (high heels) designer na Manolo, doguwar rigarta fitted ce na wani hadadden material shima turquoise blue designed by Jimmy choo ,sai purse nata shima design na Manolo, sark’a dankunne, bangles kuma design na Megna ne (wata indian designer) sannan tayi rolling da gyale kalan stones d’in rigar wato dark blue, tana tafe tana y’ar hirarta ita da Kawarta….. Wani kyakkyawan mutum sanye da suite bak’i da rigar ciki kuma fara ce ya d’aura black and white polka dot necktie, hannun shi rik’e da briefcase ya fito daga cikin jirgin shima sai uban sauri yake dokawa ya kara wayar shi a kunne , daidai exit na airport d’in ya ci karo da ita wayar hannun nashi ta fad’i, IMTIHAAL ta juyo da sauri tana cewa “oops!!! Am very sorry sir! Actually I didn’t notice you coming this way ” ta durkusa ta d’auko mishi wayar ta mik’a masa. Ya karb’a cike da murmushi yace ” it’s alright thanks ” Muryar shi ma kad’ai abun sauraro ne. Suka fice daga airport kowa yayi nasa waje.

     Abun mamaki shine waje d’aya suka nufa, Ruky kaxs tace “My Frnd kiga wancan mutumin kamar fa biyo mu yayi ,Imtihaal tayi dariya tace ba biyomu yayi ba ga dukkan alamu wani babba ne a nan don naga tag d’in a jikin suit nashi” Ruky tace *Better!!!.
       K’afarta ta fara jefowa daga motar, fuskarta ta saka sunglasses saboda rana da ake yi saidai brown colour ne ba bak’i ba, tana fitowa duk kallo ya koma kansu basuyi tsammanin an taru haka ba is like General yana expecting bak’i, kowa neat cikin uniforms tsaro ta ko ina an sa tsaro shi yasa ma bata wani damu ta k’arasa ciki da motan ba suka sauk’a don k’arasawa ciki. Kaf cikin wad’anda suka Santa babu wanda ya gane cewa Imtihaal ne duk kowa ya sake baki don basu tab’a ganin kyau irin Wannan ba. Babban abun mamakin shine even Captain Rasheed doesn’t seem to recognize Imtihaal!!!:oops:.

    Ana wata ga wata!!!! Shin waye mutumin da suka yi clash a airport? Is captain Rasheed really captain Rasheed?? And if he is me yasa ya kasa nuna k’auna ga Imtihaal?? This really change the story my dear readers coz this is where the truth unveils!!!!!

  Masu karatu ayi min afuwa kun Jini shiru kwana biyu I was very busy dis day’s, but I’ll try and make it up to u. L????v you all!!!

☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/20, 9:42 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
????7⃣1⃣〰7⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

      Mutumin da suka ci karo a airport da shi bai zame ko ina ba sai inda General (Abbah )yake tsaye suka yi wata maganar su k’asa k’asa sannan mutumin ya yi cikin gidan General d’in wato gidan su Rasheed, yayin da captain Rasheed ma ya bi bayanshi. Major Ahmad Suraj (baban Imtihaal)ya hau stage ga press a gaba ya gama speech nashi ,haka dai suka gama aka watse daga taron kowa yayi nasa guri.

      Band’aki ya shiga ya tsaya gaban mirror yana kallon fuskar shi,a hankali yake shafa fuskar yana murmushi domin ya tuna da abun da yafi mishi sauyuwa a zuciyar shi wato Imtihaal, ya gama kallon fuskar shi sannan ya fara yage mask din dake fuskar abun mamaki fuskar babu wanda wanda zai gani yace ba nashi bane ashe na roba ne!!! Dagowan da zaiyi nima Hauwa’u saida na tsorata???? domin kuwa babu abunda ya raba shi da captain Rasheed !!! Ya sani cikin zullumi domin masu karatu in baku manta ba captain Rasheed ba yan biyu bane ,sannan bashi da wa balle kani !!!muje zuwa!!………

      Imtihaal na zaune a palour tana ganin video na auren da sukaje a India d’in sai dariya take yi,taji an buga k’ofa ,tana lek’a wa taga Captain ne sai ta k’i bud’ewa ta koma tayi zamanta, ya gaji da tsayuwa ya jiya ya tafi duk ranshi a dagule domin kuwa  bai san me ya faru ba. Yana tafiya hannun shi rik’e da wani Jan jewelry box mai kyau kawai yaji an ja riganshi ta baya a fusace ya juya yace ” and who the hell are you?!! Cike da mamaki Ilham ta ce “Haba captain!! Yau kuma baka ganeni ba ko? Toh Sannu sarkin zolaya gaskiya Muryar ka ta chanza!!” Rai a 6ace ya daka mata tsawa yace ” look I don’t know who the hell you are ! Just get out of my way!! A firgice ta matsa gefe idanuwan ta suka kad’a sukayi jaa ta bi bayanshi da kallo.

  Dakin shi ya shiga ya zauna shiru sai ga Sadiq ya shigo d’akin ba tare da ya kulashi ba ya hau cire kayan jikin shi, Rasheed ya dubeshi yace ” dude Wai nikam my precious bata nan ne? Ko bata dawo daga Malaysia bane?? Sadiq ya juyo cikin sauri ya rungume shi yace ” its you dude!! Ashe kai ne ,yaushe ka dawo ko kira bakayi ba? Duk a lokaci guda yayi maganganun nan. Rasheed yayi wani latest murmushi wanda ya kara fitar masa da kyau yace ” ai numbern ne yak’i shiga kasan Pakistan sai a hankali !! Especially chan Kashmir d’in. Sadiq Yayi darya yace ” abokina am glad you are back don wallahy abubuwa sun kusa dagule wa a nan fa , Duplicate Rasheed din nan yaso ya 6ata rawar shi da tsalle!!!:oops::oops: Rasheed ya mik’e da sauri yace ” me yayi? Imtihaal ta dawo ne?? Ina shi duplicate Rasheed din yake?? Duk a lokaci guda Rasheed yayi tambayoyin. Sadiq ya sauk’e Ajiyar zuciya ya kwashe labarin abunda ya faru tun daga farko har zuwa dawowan Imtihaal da had’uwa duplicate Rasheed da Ilham…………..

????????Jeeddah ja’o????????
[4/20, 10:45 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????7⃣6⃣〰8⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

       Rasheed ya mike a fusace as well very heart broken saboda bai yi tsammanin har duplicate Rasheed din nan zai yi affecting love life nashi ba ,tabbas zuciyarshi tayi bak’i!! Suna cikin haka sai ga duplicate Rasheed ya shigo ,yana faman cire mask na fuskan shi wanda akayi shi mai kama da Rasheed Sak!! Fari ne kam kuma shape na fuskarshi irin na Rasheed ne abunda yasa ma aka za6eshi kenan duk cikin sauran captains domin har tsayin su d’aya ne!! Yana gama cire mask din captain Rasheed ya zuba masa wani uban mari wanda saida yaga wuta???? a take ya rik’e kuncin shi yana kallon Rasheed. “Am very disappointed in you khaleel!!! Sunan da RASHEED din ainihi ya K’ira duplicate Rasheed da shi kenan. Amana fa na baka ! Just because I trusted you I left you amanar abunda yafi soyuwa a zuciyata ,na zaci zaka nuna mata gata har in dawo sai ka chusa mata tsananin tsanata a zuciyarta! Ka lalata min rayuwa ta!!! Rasheed ya sake chukume kwalar rigar khaleel yace ” kasan Allah in har Imtihaal is not able to forgive the mistakes you have made in my position I am going to teach you a lesson that you will never forget in a hurry!! Ya fadi hakan ne cikin rawar murya idanuwan shi sun ciciko da k’walla jikinshi har rawa yake yi.

   Hayaniyar da Inna ta jiyo ne yasa ta hauro sama domin ta duba ko me yake faruwa, a gigice ta k’arasa inda suke ta kama hannun Rasheed wanda da kyar ta iya janye shi daga jikin khaleel tayi waje da shi ,yayin da khaleel ya nemi bakin gado ya zauna sai maida numfashi yake duk jikinshi na rawa ,cikin zuciyar shi yace ” kai Wannan mutumin akwai k’arfin bala’i” yana yi yana shafa gurin da aka shak’e shi……..

    “My son! Lafiyar ka kuwa? Yau khaleel d’in kake shak’e wa kamar zaka kashe? Ko kayi hauka ne, mutumin da ya karb’i matsayin ka ya goge duk wani personality nashi don kawai ka je ka gama assignment d’in da ke gaban ka har ma ya kula maka da duk wasu business naka bai yi wa iyayen shi ba shine zaka yi wa haka?? Rasheed bai yi wata wata ba ya kwashe labarin duk abubuwan da khaleel (Duplicate Rasheed)ya aikata ya fad’a mata ,Inna tayi mamaki matuk’a kuma ta san yadda d’anta ya ke k’aunar Imtihaal duk hankalin ta ya tashi domin kuwa tasan akwai matsala babba idan har ya rasa abun da yake k’auna. Tayi shiru jiki a sanyaye shima ya tashi ya mik’e ya fice daga d’akin daidai ana shiga sallar maghrib,tare suka yi sallan da Sadiq suna idarwa bayan sun yi adduoi basu zame ko ina ba sai k’ofar su Imtihaal akayi sa’a house maid d’in ce ta bud’e musu k’ofar ,suka gaisa sannan tace su zauna zata yi magana da Imtihaal d’in. Suna zaune suna jira wajen minti talatin har sun fara cire rai zata ma fito sai gata,saukowa take daga stairs tana danna wayarta, hannun ta yasha henna tattoo (lalle) riga na atamfa dinkin high waist da skirt ne a jikinta tayi dauri irin me step step din nan ,k’afarta slippers ne baki me kyau tabbas sai lokacin yayi recalling cewa da Imtihaal d’in shi suka yi clashing a airport ! Lallai precious d’in shi ta chanja Sam !! She’s so beautiful but yayi missing crazy looks nata:D.

   Guri ta nema ta zauna tana k’are musu kallo d’aya bayan d’aya sannan suka gaisa ,ta amsa musu babu yabo ba fallasa. Abun takaici shine duk yadda Rasheed yaso yayi explaining abubuwan da suka faru ,Imtihaal ko sauraron shi bata yi hasalima cewa tayi dama ba son tsakani da Allah yake mata ba ,ta gane kawai yanzun ma don yaga tayi kyau ne shiyasa ya biyota kamar yadda yake bibiyan Ilham!! Ta mik’e ta fice abunta ta barshi a gurin baki a sake.

Jikin a sanyaye ya ajiye wannan jewelry box d’in da ya kawo mata da yamma ta ‘ki bud’e kofar a kan center table suka fice house maid d’in ta rufo k’ofar…….

????????Jeeddah ja’o????????
[4/20, 1:34 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????8⃣1⃣〰8⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

    Yana Kwance kan gadon shi daga shi sai 3quater trouser sai faman kirga ceiling yake yi ya yi zurfi sosai a cikin tunanin da yake yi ,har Abbah ya shigo ya zauna kusa da shi bai sani ba ,ya ajiye files din hannun shi sannan ya had’a hannun shi da na d’an nasa duk da haka Rasheed bai ko kifta ido ba ya dauko wani glass cup da ruwa a ciki ya zuba mar a fuska. A d’an firgice Rasheed ya tashi ya zauna sannan ya jingina da gadon yana ajiye numfashi sama sama. Abbah ya fara da cewa ” my dear I know you are having hard times tun da ka iso garinnan d’azu ,kuma nasan game da Imtihaal ne coz Sadiq ya fad’amin komai in fact I have spoken with the Major about issue naka da Imtihaal,soon zamu je nema maka auren ta ” Rasheed na jin haka ya zaro ido ya gyara zama. Kafin yace wani abu Abbah ya ce  yanzu dai ga wad’annan files din ka duba su don gobe akwai possibility za’a buk’acesu during the meeting kuma akwai issue na wad’annan Sargent guda biyu Ezekiel da simon make sure an gano wanda yayi laifin!!” Abbah yana kai wannan ya nufi kofar fita ,gami da turo masa k’ofar d’akin ,shi dai Rasheed murna fal ransa Imtihaal ta kusa zama mallakin shi.

        Yau da ruwan sama mai k’arfin gaske aka tashi tun bayan sallar asubah ,babu wanda ya shirya fita aiki kowa yana Kwance ,Imtihaal na tsaye a saman balcony tana ta mik’a hannu tana wasa da ruwan sama ,sai dariya take yi a haka har kusan k’arfe tara na safe ruwan ya d’auke, garin yayi matuk’ar sanyi ba kamar jiya ba! Bai ma gama d’auke wa ba ta hango Rasheed ya fito da motarshi yayinda mai gadi ya mayar da gate ya rufe shi kuma ya yi parking motar ya fito waje yana waya ,hannun shi guda kuwa yana buga key d’in motar da ke hannun shi. Duk abun da yake yi tana tsaye tana gani, ta tuna da gift d’in da ya ajiye mata jiya a Falo ta ruga ta nufi gurin ta k’urawa box din kallo kafin ta sa hannu ta bud’e. Wani hadadden silver ring ne me dutsen diamond a saman shi da kuma necklace nashi???? mai matuk’ar kyau ,designed by Michael korrs. A k’asan zoben akwai wani card mai kyaun gaske an rubuta, ” will you marry me? ” ???? ta dad’e a gurin tana kallon card d’in ashe Ruky kaxs na bayan ta. Ruky ta wafce card d’in ta gudu tana dariya Imtihaal ta bita da gudu itama suka fara zagaye falon tana cewa ” Oooh my Frnd pls ki bani mana !! Ai kuwa bata bata ba sai da ta gama karantawa duk suka zube a kasa tsabar gajiya suna maida numfashi kamar wanda aka sasu gudun dole. Ruky ta mik’e da wuri tace ” k’awata duk da wannan fa ba cewa nayi kiyi giving up so easily ba!! Ki nuna masa baki ma san da zancen ba kuma by the way plan d’in mu zai fara aiki yau, kin san na yarda da Ahmad sosai ,saurayina ne zai iya yin komai for my sake saboda haka zai zama acting boyfriend naki ,har sai Mun tunzira Rasheed dinki ya gane kuskuren shi !! Duk suka bushe da dariya sannan suka cigaba da hirarsu………

   Rasheed na zaune a office nashi sai fama yake da computer yana duba files d’in da Abbah ya bashi,jin karar bud’e k’ofar shi da akayi ne yasa ya d’aga kai don ya gane ma idon shi wanda ta shigo…….,………….

????????Jeeddah ja’o????????
[4/21, 6:38 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????8⃣6⃣〰9⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

Previous page 1 2 3Next page

Leave a Reply

Back to top button