HAUSA NOVELMAYE GURBI Complete Hausa Novel

MAYE GURBI Complete Hausa Novel

*Shafi na d’aya*

Zaune ta ke a tsakar d’akin ta barbaza takardu a gabanta, hannunta ri’ke da jan biro, abinda zai tabbatar ma ka da cewa marking jarrabawar d’alibai ta ke.

Sanye ta ke da doguwar rigar atamfa mai gajeren hannu, da ta ‘kara bayyana kyawun siffarta, ba’ka ce amma ba can ba, irin kalar fatarta ake kira da chocolate colour, kanta babu d’an kwali, hakanne ya taimaka gurin bayyanar ba’ki sid’ik d’in gashinta, wanda aka yiwa kalba manya, da jelarta ta sauka har kan kafad’arta.

Hankalinta ya yi nisa akan aikin da ta ke, sam ba ta ji sallamar da akai a ‘kofar d’akin ba, har mai sallamar ta shigo, jin alamun zama da akai akan katifar da ke shimfid’e a cikin d’akin ne ya ankarar da ita cewa an shigo d’akin.

‘Daga kanta ta yi tana kallon wadda ta shigo d’in da alamar harara-harara.

Fuskarta d’auke da murmushi ta ce, “wallahi Aunty Halima na yi sallama, hankaliki ya na kan takardu ne, shiyasa ba ki ji ba.”

Murmushin itama ta yi, ba tare da ta ce komai ba, sai ta maida hankali kan aikin da ta ke yi.

“Aunty Hafiz ne fa ya zo. Don Allah yau dai ki daure ku gaisa, ya dad’e ya na son ku had’u, ke kuma kin ‘ki ba shi dama.”

Biron da ke ri’ke a hannunta ta ajje, ta d’ago tana kallonta ta ce “haba Sumayya, bakya ganin aikin da na ke yi ne? Ya kamata ki dinga yi min uziri, duk lokacin da zai zo ina cikin uziri, kuma ko ba komai gotai-gotai da ni sai na tafi gurin saurayin qanwa wai mu gaisa?

Ina laifin idan mun had’u a wani guri sai mu gaisa d’in, ba wai ni na fita takanas don gaisawa da shi ba.”

“Shikenan, amma ni a gani na babu wani abu a ciki don kin fita kun gaisa, musamman ganin yadda ya damu akan son ku gaisa d’in.”

Da kyar ta samu ta lalla6a ta ta ha’kura akan wani lokaci idan ya zo za su gaisa, bayan fitar ta daga d’akin ta bi ‘kofar da kallo kamar mai yin nazarin wani abu. Duk wanda ya san ta da ya kalle ta a lokacin ya san akwai wani abu da ke damun ta a zuciyarta.

Haka ta maida hankali kan aikin da ta ke, bayan ta yi ‘ko’karin danne damuwar da ke cikin zuciyarta.

Kafin lokacin sallar magriba ta kammala komai, ta tattare takardun ta zuba a cikin wata jaka, sannan ta fita tsakar gida don yin al’walar sallar magriba.

Dai-dai lokacin da ta fito, Sumayya ta shigo cikin gidan hannunta d’auke da babbar leda mai d’auke da tambarin shoprite.

“Har kin gama?” Sumayya ta tambaye ta.

“Eh wallahi, amma dai na sha wahala, don aikin akwai cin rai.”

“Hhhhh’ Aunty Halima kenan, to kuma da ace ke form mistress ce ya za ki yi? Tun da bayan wannan akwai aikin had’a report sheet?”

“Ke dai bari, ai Alhamdullih da ba itan ba ce.”

Gaba daya sai suka saka dariya.

Dai-dai lokacin da mahaifiyar Sumayya ta fito daga kitchen ta na zabga musu harara, don duk maganganun da su ke a kunnenta.

Cikin fad’a ta cewa Sumayya “ya yi miki kyau, kin fita kin dawo, amma kin fi ‘karfin ki sanar da ni, sai dai ki tsaya a gurin ‘kanwar uwarki ko? Wallahi Sumayya ki fita daga idona, na rufe, idan kina da hankali wannan har abar a tsaya a yi magana da ita ce, ki bari sai ta san ciwon kanta, ta sami ma’auri tukun, don ko banza kin yi mata fintinkau, tun da nan da d’an kokaci ‘kan’kani darajarki za ta d’aukaka fiye da ta ta, ai aure dai shine darajar ‘ya mace.”

Duk da a cikin su babu wadda maganganunta ba su yiwa ciwo ba, amma babu wadda ta nuna ko a fuska, sai ma wucewa da suka yi, ita Sumayya ta shige d’akinsu yayinda ita kuma Halima ta d’auki buta ta shige band’aki, bayan ta fito ta yi alwala ta shige d’akinsu.

Mahaifiyar Halima da ke jin duk abinda ya faru murmushi kawai ta yi, idan da sabo ya ci ace ta saba da halin Saratu, don mace ce fitinanniya, sai kuma Allah ya had’a ta zama da mutane ma su ha’kuri.

Misalin tara da rabi na dare suna zaune a d’akinsu Sumayya ta dubi Halima da hankalinta ke kan wayar hannunta, da alama charting ta ke, sai ta ce “Aunty na ce ba?”

‘Dago kanta ta yi tana kallonta, sai ta ce “ki ka ce me?”

“Dama fa Hafiz ne ya ce in sanar a gida ranar asabar mai zuwa idan Allah ya kaimu za’a kawo lefe.”

Duk da fad’uwar da gabanta ya yi bai sa ta bari sumayyan ta fahimci halin da ta ke ciki ba, sai ma wani murmushi na ‘karfin hali da ta yi, cikin nuna tsantsar farin ciki, ta ce “Allah ya kaimu da rai da lafiya.

Tun lokacin ta ji charting d’in da ta ke ya fita daga ranta, sai kawai ta kashe wayar ta nemi guri ta kwanta.

 

 

*_Follow me on Wattpad_*
*_Comment_*
*_Vote_*
*_Share_*
[9/27, 9:49 AM] Wasila Ummu Aisha: ????????????????????????????????
*_MAYE GURBI_*
*_BY_*

*_UMMU AISHA_*

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Shafi na biyu*

Washegari bayan sun yi sallar asuba, Sumayya ta koma ta kwanta kamar yadda ta sabi, ita kuwa Halima bayan ta gama azkhar d’akin mahaifiyarta da suke kira da Mama ta shiga, daga parlour ta tsaya ta share shi tas, bayan ta kawar da duk abinda ba’a bu’katar ganinsa a gurin, sannan ta shiga uwar d’akin.

A zaune ta same ta akan sallaya, tana lazumi, ba ta yi mata magana ba, ta fara gyran gadon, sai da ta tabbatar d’akin ya yi dai-dai yadda take bu’kata, sannan ta d’auko tsintsiya ta share.

Zuwa lokacin Maman ta kammala lazumin, bayan sun gaisa Maman ta fita parlour don ba ta dama ta yi shararta cikin nutsuwa.

Sai da ta gama duk abinda ya kamata, sannan ta shiga kitchen ta d’ora ruwan zafi, kafin wani lokaci, har ya yi zafi, ta juye shi a bucket ta sirka ta shiga wanka, zuwa bakwai na safiya ta gama shiryawa tsaf, sai ta je d’akin Mama ta d’ebi ruwan zafi a cikin flask da Maman ta ke ajewa, ta had’a tea, ta had’a da bread ta ci, don ta san indai Aunty Saratu ce da girki har ta fita ba zata sami abin karyawa ba, don haka ta ke tanadin bread a duk ranar da ta san itace da girki.

Misalin 7:30 ta fito da shirin fita daga gidan sanye da hijabi akan kayan da ta saka a jikinta na atamfa riga da zani plain, sai jakarta da ke ri’ke a hannunta, wadda ta zuba takardun jarrabawar yara, da kuma abinda ta san za ta bu’kata.

Sai da ta le’ka d’akin mahaifinta wanda suke kira da Baffa su ka gaisa, sannan ta fice daga gidan bakinta d’auke da addu’ar fita daga gida wato (Bismillaahi tawakkaltu alallaahi walaa haula walaa ‘kuwwata illaa billaahi.)

Ba ta jima a ba’kin titi ba ta sami adidaita ta tsayar, bayan ta gaya ma sa inda zai kaita ta hau.

Misalin sha biyu da rabi na rana ta shiga gida bakinta d’auke da sallama. Aunty Saratu da ke wanke tukunyar da ta gama abincin rana da ita ko kallonta ba ta yi ba bare ta amsa ma ta sallamar, sai ma dogon tsaki da ta ja, ta ci gaba da abinda ta ke.

‘Dakin Mama ta fara shiga, bayan ta sanar da ita cewa ta dawo, sai ta wuce d’akinsu, nan ta sami Sumayya da Sadiya (‘yar Aunty Saratu ce, amma ita babanta ya rasu) zaune suna ta hira.

Fuska a sake ta ce “a’a Sadiya ashe kin dawo.”

Sai Sadiyan ta d’ago ta fube ta a kai-kaice ta ce “eh, wallahi, ta na magana kamar wadda aka yiwa dole.”

Ganin yanayin yadda ta ba ta amsa, sai ba ta sake yi ma ta magana ba, ta kama sabgar gabanta, don ko babu komai bai kamata ta bari yarinya ‘karama ‘kanwar bayanta, ta kawo ma ta raini ba.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button