NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 3) 26

????HASKE WRITERS ASSO….

    RAINA KAMA…!!
              (Kaga gayya)
          Bilyn Abdull ce????????
BOOK 3 ????????25
……………..Da mamaki Na kalli Munubiya ina kwantar da Amaturrahman. Nace, “Komawafa Munu?”.

        Tsayawa tayi daga shirya kayan da take tana kallona da mamaki, “Ban ganeba, bakison komawar ne? Dakikemin wannan banzar tambayar?”.
       Baki Na zum6ura ina fad’in “Nikam dai bazan koma haka siddan ba, sai inhar yazo ya warwarema iyayena komai gameda tubalin daya k’ulla aurenmu a farko, yakuma basu hak’uri”.
        Kasa magana Munubiya tayi, saima ta zauna a bakin gadon, ita batasan wajen ubanwa Munaya ta d’akko halin taurin kai ba wlhy, ita tama rasa mizata ce mata.
       Nima d’auke kaina nayi gefe Dan ina kan bakana, ina tausayinsa Dan koba komai ya k’yautatamin a lokacin da nima banida lafiya, kuma ta silata yake kwance yanzu, to ammafa hakan bazai zama yasha a banzaba, kenan ma anan gaba wasu zasu iya aikata hakan ga kowacce mace?.
      Laraba dataji komai dake faruwa tana niyyar shigowa saita koma da baya gabanta Na fad’uwa, ita bataga laifin Munaya ba, dan wannan shine martaba da sanin ciwon kai, kuma wannan ya tabbatar mata da ba kwad’ayine yasata zama da shiba, amma bata fatan abinda zai girgid’a wannan Auren komai k’ank’antarsa waya ta d’auka ta kira Mom ta sanar mata komai, hankalin mom ya tashi, danba ta wanann hanyar takeson Munaya ta hora Galadima ba, bakuma taso iyayenta su Sani, suma sunada burin d’aukar mata mataki itada Momma, Dan bazasu bar wannan gangancin Na Galadima ya wuce a banzaba.. Momma ta kira tace Dan ALLAH ta kira Munaya tabata hak’uri akan ta koma, Dan babu mai kula da Galadima d’in, insha ALLAHU daga baya wannan maganar za’ayita.
          Momma ma duksai ta damu, dan har cikin ranta tana k’aunar Munaya, bazataso wata matsala ta tasoba bayan hankalinta ya kwanta akan zamansu.
         Munaya suna tare da Munubiya har yanzu a d’aki, ta balbaleta da masifa kamar ta daketa, Munubiya tanada hak’uri, shiyyasa idan tana masifa dolene kasan takai k’arshen 6acin rai, Munaya saita zuba mata ido kawai takasa cewa uffan, ana cikin hakane kira ya shigo wayar Munaya.
     Harzata share saikuma ta d’au tana dubawa, ganin Momma tai saurin d’agawa tana share hawayen da suka zubo mata. Cikeda girmamawa kamar yanda ta saba ta gaisheta.
    Daga can Momma ta amsa cikin kulawa itama, face, “Kun dawo lafiya d’iyata?”.
       “Alhmdllh Momma ya jikin Abie”.
        “Jiki kan Alhmdllh d’iyata, dama Abbanki ne ya kirani akan zaki koma, saboda Muh’d babu lafiya, da farko dai nayi tunanin cewa a barki harsai yazo yafad’a musu laifin daya aikata agaresu, saikuma nayi wani tunani daga baya, kiyi hak’uri ki koma yaud’in Dan ALLAH, saboda Mura bataima Muh’d da sauk’i, namiki alk’awarin zan d’auki mataki da kaina, zan sanar masa Ku tahoma gobe idan ALLAH ya kaimu kinji”.
      Bazan iyama Momma musuba har abada, Dan nasan bazata cutar daniba, saidai kuma nayi mamakin dama tasan auren Contract mukayine?…….
      Katsemin tunani tayi da fad’in “d’iyata idan kinga zaki cutu abari kawai, bazan ta6a bari Muh’d ya cutar dakeba wai danni Na haifesa wlhy”.
       “A’a Momma Na amince”.
    Daga can Momma ta sauke ajiyar zuciya tana fad’in, “Alhmdllh, d’iyata nagode sosai, ALLAH yay miki albarka kinji”.
       Idona cike da kwalla Na amsa da amin.
    Tace Na gaida mata kowa ta Yanke wayar.
    Munubiya dukda ta fahimci dawa Munaya tayi waya batace da ita uffanba, tacigaba da had’a musu kaya kawai.
        Ciwonsa ne yasani Na danne zuciyata Na amince, dakuma Kimar mahaifiyarsa danake gani, Dan sun nunamin dukkan k’aunar da inhar Na bitilcemusu banma kaina adalciba nima.
       yinin ranar gaba d’aya a hidimar shirin komawa mukayisa, ga gajiyar tafiya Na nuk’urk’usarmu, amma ya muka iya, da yamma dole su mama Rabi’a suka dawo domin mana rakiya.
    
     A gurguje please????????.
******
           Abin mamaki sai gamu da rusar kuka ni da Munubiya, saikace wasu sabbin amare, bayan nasiha da Abba da baba k’arami, daddy sukai mana Na ajiye musu keys d’in motocinsu, da farko sunce bazasu kar6aba Na sanya musu kuka.
    Innaro tahau musu fad’a babu k’yau maida hannun k’yauta baya ai, wannan aikin shaid’anne.
     Albarka dai munshata kam, yayinda zukatan matan gidanmu yakusa babbakewa saboda bak’ar hassadarsu, kowa son samunshi ace d’ansane yayi.
      Laraba ma harda hawayen sabo, dan bak’aramar girmamawa aka mata a gidannanba, har abada bazata ta6a mantawa da dattako irinna inna ba.
    Kaf matan gidanmu dasu aka tafi, innarmu da Innaro kawai aka bari, amma hardasu Siyama.
     Ni suka fara rakawa, ALLAH ya somu muka iske Muftahu yadawo daga yawonsa zai shiga masarautar, da taimakonsa muka shiga, yayi mamakin dawowata, dan Galadima ya sanar masa muna Niger, shi baisan yadawoba ma, hasalima babu Wanda yasan Galadima ya dawo masarautar, tunda ko salla bai fitaba, sai hadimansa kawai.
       Ba sashenmu akai kainiba, Muftahu ya sanar musu sai an fara kaini wajen mama Fulani sannan, haka al’adar masarautar take.
      Aikam dai hakan akayi.
        Tarba ta mutunci mama Fulani tasa akaima dangina, tana nandai yanda kuka Santa da mulkinnan nata da izza, amma ni a yanzu tunda Na fahimci ita ba muguwa bace sai salon nata yake k’ayatar dani.
          An min dukkan yanda al’adar masaurat ta tanadar, sannan mama Fulani dakanta tamin rakkiya sashena tareda bayi da dangina, ko ina k’al tamkar muna nan.
      Bayan fitar mama Fulani y’an gidanmu suka kuma shishshiga suna kallo gida wai, dan ranar suna da suka fara zuwa basu sami wannan damarba saboda idon mutane, nidai batasu nakeba, hankalina nakan mijina, burina naje naga halin da yake ciki.
        Munubiya takuma min nasiha da bani wasu dabaru, tunda su sinzama tsoffin hannu, muko yanzune zamuyi zaman auren tsaftatacce, takuma nunamin nabi komai a hankali, tasan yayi kuskure amma bata hanyar tonama kanmu asiri zan nuna masa kuskurensa ba, kodan matsalar gidanmu ai saina duba, ni macece inada damar juya komai cikin sauk’i, nama iya zama dashi a lokacinda yake ik’irarin auren yarjejeniya bare kuma yanzu daya furta yana sona da bakinsa.
    Naji dad’in shawarwarinta, nakuma fahimceta sosai, Naimata godiya kuma, da alk’awarin amfani da shawararta insha ALLAH.
      Hakama mama Rabi’a tak’aramin nasiha da gargad’i mai yawa akan karsuji karsu gani, Na tsare musu mutuncinsu, Dan kowa da tarbiyyar gidansu yake ado.
      Itama na amsa mata da insha ALLAH zan kiyaye.
     A y’an gidanmu kam Maman Fauziyya Ce kawai tamin fad’a, amma sauran babu wadda tace nayi mai k’yau ko mummuna, wannan ba matsalarsu baceba, nima ban damuba, Dan wad’anda suka Isa dani sunmin kuma ya wadatar. yayinda zasu tafi rungume juna mukayi da Siyama da Munubiya, Zarah muna hawaye, jimuke tamkar karmu rabu.
     Dan wlhy yanzu nikam tausayi suke bani, koma miye dai iyayen su mata da k’addara Ce taja musu.
      Inaji ina gani suka tafi suka barni da kewa, danma laraba Na nan.
    Suna wucewa laraba ta kalleni, cikin dabarunsu Na tsoffi tace, “koyaya jikin magajin garin?”.
      Kaina a k’asa nace, “inaga barci yake iya”.
      Tayi murmushi, Dan kunyar Munaya da kawaicinta Na burgeta, yanda idon yaran yanzu ke a bud’e da rashin kunya a halinyanzu, da watace tuni tanufi d’akin mijin.
      tace, “yakamata to kiduba koya tashi, da saiki samu kayan k’amshi ki dafasu, insha ALLAH yasha Na kwana biyu sai murar ta barshi”.
     Godiya Na mata sannan Na mik’e a kunyace Na fita.
       A falon dazai sadani da sashensa naci karo da Muftahu, barka da zuwa yakuma yimin muka kuma gaisawa amutunce.
    Yace, “Boss d’in Na ciki kuwa? Dan sarkin k’ofa yace yayi sallama Dan nemamin iso yaji shiru”.
       Nace, “Ai bashida lafiyane, maybe ma barci yakeyi, mura ke damunsa, amma bara Na duba ka shigo”.
         Cikeda tausayawa Muftahu yake fad’in “Kai aikam mura Na wahal dashi sosai Idan ta damk’esa, shiyyasa bayason zuwa Nigeria lokaci irin wannan Na sanyi, aini banga ta shigaba, bara naje muzo da doctor jalal daganan nasamo muku abinda zakuci, yanzu haka yinin yau baici komaiba”.
       Godiya namasa ya juya ya fita, nikuma na nufi k’ofar falonsa.
         Tun a falon na tabbatar mai d’akin babu lafiya, Dan komai a kashe yake har AC, Wanda inhar yana gidan AC yini yake yana aiki, koda uake akwai sanyi yanzu, shi ko damunsa bayayi ma, Na k’arasa k’ofar Bedroom d’in, harna kai hannu zanyi knocking kuma saina fasa, tura k’ofar nayi a hankali da sallama Na shiga, d’akin dund’um da duhu gashi bansan ina makunnar fitilar take bama ni, tsaye nayi ina tunanin mafita, na komane ko nayi magan…?
    
         Galadima dake kwance yau yini guda cikin halin ciwon kai da zazza6i, salla Ce kawai ke tadashi, abincima da k’yar ya had’a shayi yasha bayan sallar la’asar, tunda ta shigo yana jinta, saidai baisan wanene ba, shi a tunaninsa ma wanine yazo cutar dashi, jin anyi shiru ankuma k’i magana ya mik’a hannunsa da k’yar ya kunna fitilar dake dirowar gefen gadon.
         Baya nad’anyi kad’an danni tsoratama nayi, harma na fara zaton kobaya d’akin, sai kuma na nutsu waje d’aya ina kallonsa, yana cikin bargo ya lullu6e har kansa,  janye bargon dake lullu6e da fuskarsa yayi yana kallona ta cikin d’an hasken fitilar.
     Idanu ya zuba mata cikeda mamakin yaushe tazo gidan? Ya ciro hannunsa daga bargon yana min alamar nazo.
     A hankali na cigaba da takawa, zuciyata cike da d’unbin tausayinsa, koba komai ta sanadina ciwon ya sameshi, na zauna a bakin gadon idona a kansa, hannuna ya kamo cikin nasa dakeda zafi alamar zazza6ine ma a jikinsa. Ina had’iye kukan daya tahomin nace, “Sannu, ya jikin?”.
      Idanunsa ya lumshe da cije lips.
    Na kama bargon zan yaye yakuma rik’e d’ayan hannun yana girgizamin kai, ahankali yace, “Sanyi”.
     Sannu na kuma masa, sannan na zare hannuna zan mik’e, amma saiya rik’oni da sauri, jiyowa nai ina kallonsa.
     Ahankali Yace, “Ina zakije?”.
     Badan ina kallon la66ansa ba dabama zan fahimci miyace d’inba, Dan banjiba.
    Dawowa nayi na zauna, nad’an matsa hannunsa, “zan had’a maka ruwane kasamu kad’anyi wanka, kaci abinci kuma”.
        “Zan daiyi wankan kawai?”.
     “Abincin fa?”.
Kansa ya girgizamin alamar a’a.
     Kamar zanyi magana saikuma na fasa, tashi nayi na shiga toilet, dukda babu wani datti dai sai naga yakamata na wanke, na cire mayafin jikina na tsaftaceshi, na saka air freshener sannan na had’a masa ruwa mai d’an zafi ba canba dai, yanda zai masa dad’i.
      Zaune na iskeshi a bakin gadon ya dafe kansa, kallo d’aya namasa na d’auke kai, Dan dagashi sai boxer.
      “Ga ruwan na had’a”.
   ‘Dago idonsa yay ya kalleni yana sauke hannunsa daya dafe kai,  yanda tawani k’asa dakai kamar tana gaban surukinta, yad’an murmusa danshi kunyar nan tata birgeshi take.
       Duk saina takura da kallon dayakemin, gashi kunyar motsawa nake daga wajen, Dan sket d’in jikina ya kamani sosai, maganarsa Ce ta katsemin tunani.
      Na d’ago ido naimasa kallon fisha na janye ina fad’in “Towel?”.
       “Uhumm”. Kawai yace yana cigaba da kallonta.
    Ahankali na dunga tafiya saikace wata mai tatata, Dan inaji a jikina kallona yakeyi har yanzu, saida na d’akko gyalena dake jikin k’ofar bayi na yafa sannan na d’akko towel d’in.
    Duk abinda takeyi idosa na kanta, towel d’in da hannunna ya had’a ya rik’e, na kallesa fuska a marairaice ina f’ad’in, “karfa ruwan ya huce yalla6ai”.
     Ya zubamin jajayen idonsa ga jijiyoyin kansa sunyi rad’a-rad’a, baice komaiba ya zare towel d’in ya yafa a jikinsa yana mik’ewa da k’yar, saiya kuma bani tausayi, Dan na lura k’arfin haline kawai yakeyi.
           Bedsheets d’in saman gadon Na cire bayan Na kunna fitilar d’akin ya gauraye da haske, Na bud’e wardrobe d’in kayansa Na d’akko wani bedsheets d’in Na shinfid’a, Na share d’akin, banyi morping ba tunda darene, nasaka turare sanann Na fita.
    
        Yauce rana ta farko dana shigo kitchen da nufin dafama miji abu, sainakejin karsashi da alfaharin nimafa yanzu matar aurece tamkar kowacce mace, natashi daga matar Contract yanzu, wasu hawayen jin dad’i suka zubomin, nasa bakin mayafin Na share, a kayan da mukazo dasu Na ciri kayan k’amshi, ina d’auraye tukunya laraba ta shigo, juyowa nai ina kallonta.
    Tace, “ya jikin nashi?”.
       Ajiyar zuciya nad’an sauke. Nace, “da sauk’i iya, amma kwance Na iskeshi rijib ga zazza6i, zan dafa masa ruwan zafinne da d’an abinda zaici”.
        “ALLAH ya k’ara sauk’i, dama mura bata masa da sauk’i, dan yasha zuwa can yanayi kota sameshi a can, namiki karambani Na dafa ruwan zafin gashinan”.
        “Nagode iya, wlhy babu wani karbani, taimako dai, mun saki aiki ga gajiyar tafiya”.
     Dariya tayi tana gyara tsayuwa. Tace, “Aini gajiyarnan kam ta gudu, ras nakejina, kunedai dayake ba wahalar kuka saniba koyaya kuka motsa sai jiki yayta ciwo”.
      Nima dariya nad’anyi, ina cigaba da had’a komai akan k’aramin tire.
     Laraba tace, “To yanzu Yaya za’ayi kenan da abinci? Kinga dai ba’a barshi da yunwa ba?”.
    Nace, “Iya ga  Muftahu can ya tafi samo masa abincin”.
     Tace, “To shikenan hakanma yayi”.
       ‘Daukar tiren nayi natafi kai masa.
      Har yanzu bai fitoba, mamakin dad’ewarsa ta kamani, ajiye tiren nayi a k’aramin table glass d’in dake gaban gadon nima Na zauna ina tsumayen fitowarsa. Kusan mintuna 3 da zamana saigashi ya fito.
         Ban kallesa bama gudun karnaga abinda yafi k’arfina, kaina a k’asa ina wasa da stones d’in jikin mayafina.
      Shikam tunda ya fito idonsa Na kanta, ya zauna kusa da ita yana tsane ruwan fuskarsa zuwa kai da towel.
       Kallonsa nayi kad’an, ganin bathrobe ce a jikinsa saina samu nutsuwa.
          Da hannu yay min nuni da mansa, na mik’e Na d’akko, amma saiyak’i kar6a.
       Nad’anyi shiru da tunanin miyake nufi?…
   Katsemin tunani yayi da fad’in “Manma nizam shafa?”. A hankali yayi maganar, kuma fuska babu walwala.
     Ni mamakima yabani, amma to da banzo ba waye yake shafa masa?, bance komaiba na zauna kusa dashi ina zuba man atafin hannuna da mutsukashi, kunya tasa narasa dama ina zan fara?.
     Lura da hakan dayayi saiya mik’amin hannu kawai, banida za6in daya wuce cika umarninsa, anutse na shafa masa man dan banida yanda zanyi.
       Kaya na d’auka masa marasa nauyi, ya tashi zaune daga kwanciyar da yayi ya saka, nidai kauda idona nayi gefe harya gama.
    Natashi na had’a masa tea d’in da ruwan kayan k’amshinan, yana zaune akan sofa ya zubamin ido saikace wata television, dana mik’a masa mug d’in saiya had’a harda hannuna ya rik’e, da ido namasa alamar da zafifa cikin marairaicewa.
    Shima saiya min nasa salon da ido alamar da gaske.
     Nakuma narke fuska tamkar zanyi kuka, zame mug d’in yayi yana wani miskilin murmushi.
     Ya d’ora cup d’in akan bakinsa yana kallon yanda take tatta6a tafin hannunta, a ransa yace hajiyar tsiwa kenan, andawo koya kuma zamu kwashe?.
       Tea d’in yamasa dad’i, Dan saiya tuna masa da inno, itace kan masa wannan had’in inhar yana mura, yanasha yana kallona a k’asan ido, saika rantse kuma ba kallon nawa yakeba, amma ni inaji a jikina.
      Knocking k’ofar da akaine ya sashi kallon cctv, ganin Muftahu da Dr jalal sai ya juyo ya kalleni da alamar tuhuma. Uffan bance da shiba, na mik’e da nufin fita na bud’e musu saiya dakatar dani ta hanyar d’agamin hannu.
    Komawa nayi na zauna, shikuma ya mik’e rik’e da mug d’in ya fita.
    Ajiyar zuciya nad’an sauke ina binsa da kallo.
      Saida ya zauna cikin kujera sannan yabama su Muftahu izinin ahigowa.
     Duk suka zauna suna masa sannu, ya amsa musu cikin d’aga kai da basu hannu sukayi musabaha.
    Magunguna Dr jalal ya bashi na mura. Sannan ya buk’aci yimasa allura, amma saiya nuna bayaso.
       Cikin dafe kai yace, “bar Allurarnan Jalal, bara nasha maganin kawai”.
     Murmushi Dr jalal yayi, Dan yasan dama Galadima bayason allura. Basu wani dad’eba sukai masa sallama suka fita.
      Fitarsu dana gani yasani fitowa falon, kallonsa nayi ina zama, shima idonsa a kaina, da hannu ya nunamin ledojin da Muftahu ya ajiye.
    Bance komaiba na bud’e, d’aukar d’aya nayi na fita, na kaima laraba dakema su Abdurraheem shirin barci.
    Cikin tsokana tacemin “kodai murufe d’akinmu kawai”.
      Dariya nayi na fita ina fad’in “kai iya yanzufa zan dawo”.
      Inajiyo dariyarta daga falo. Nidai nashiga kitchen na d’auki plate da spoon na koma wajensa.
        Farfesun kifi na zuba masa, dan zaifi masa sauk’in ci, da farko ma cayay bazaiciba, saida naita rok’onsa harda kwalla sannan ya amince nabashi da kaina, yad’anci babu laifi, nabashi drugs d’in da Dr jalal yabashi”.
       Koda yagama sha saiya jingina jikinsa da kujerar yay shiru, yad’anji dad’in jikinsa kam ba laifi, falon saiya d’auki shiru, muna a hakane kiran Momma ya shigo wayarsa.
     Yabud’e idanu yana d’aukar wayar, yay picking, gaisawa sukayi, bansan mitace da shiba daga can najidai ya amsa da “Insha ALLAH goben muna hanya”. A hankali yake maganar saboda kansa, bama su dad’eba ya yanke wayar ya mik’e, hannu ya mik’omin alamar na kama.
    Banyi musuba na saka hannuna cikin nashi ya mik’ar dani, bedroom d’in muka koma, ya zaunar dani bakin gadon sannan ya cire kayan jikinsa, ya hau gadon ya kwanta.
   Nidai k’in kallonsa nayi, saida ya kwanta sannan ya kirayi sunana a hankali can k’asan mak’oshi, kallonsa nayi.
       Yace, “Please mammatsamin jikina kozai rage ciwon da yakemin”.
       Tausayi yabani, dan haka banyi musuba na hau gadon sosai nafara masa tausa a nutse, idonsa ya lumshe yanamai jin dad’in tausar, ahankali drugs d’in dayasha yafara cin k’arfinsa, barci mai nauyi yay a won gaba dashi, saida na tabbatar barcin yayi nisa sannan naja bargon na kuma lullu6a masa har saman kafad’a, nai masa addu’a na mik’e Na lalla6a na fita a d’akin bayan na kashe masa fitila.
     Koda na koma d’aki laraba har tayi barci, nima shirin kwanciyar nayi kawai na kwanta, cikeda kewar y’an uwana da jiya iyanzu duk muna a tare????.
 ********
            Iyayen Su Munaya maza sunyi farin ciki da labarin da Abba yabasu akan dangin inna, dan suna tausayinsu sosai, innaro ta tarasu duka tasa aka kira mata inna, harda hawayenta tana Neman gafararta bisa ga abinda tamata tsawon shekaru.
      “Kiyafemin Ai’sha, dan lallai son zuciya ya rufe idona ruf, banason ara6i y’ay’ana koni saboda abin duniya, nata k’ask’antar dake agaban wad’anda duk kin rigasu zuwa gidan, wlhy wani lokacin su mero ne suke zugani, dan ALLAH kiyi hak’uri, nasan dai da wuya ki yafemin ma…..”.
       Da Sauri inna tace, “Wlhy na yafe miki nikam, dama ban ta6a rik’eki a raina ba, dan matsayin uwa mahaifiya nake kallonki, inhar bazan iya musawa mahaifiyata magana ba ko jin zafinta to lallai kema baki cancanci na musa mikiba, ni dukanku ma na yafe muku wlhy, ALLAH ya kare gaba, yakuma yafe mana baki d’aya”.
     Su Abba duk suna amsa da amin, kowanne yanajin dad’i har cikin ransa, lallai idan kaga halin girma to daga tsatson d’an masu girma ya fito, duk cin kashin da innro tama innarsu Munaya hakan baisa ta gagara yafe mataba, ya rabbi kabamu k’yak’yk’yawar zuciya gaba d’aya.
    Masu samun fawar cin zarafin inna a wajen innaro duk sai suka nutsu suma, dan yanzu kam babu dama.
     Haka su inna sukaita rabon tsaraba akaita rabo, har gidajen iyayen su Maman safara’u duk saida aka kai, kafin kacemi labarin tushen inna yabaje anguwa, mutane sai mamaki da al’ajabin hikimar ubangiji sukeyi, lallai Maman biyu tazamema matan gidansu RAINA KAMA, su sunata hura hanci y’ay’an wasune, da mata gorin rashin dangi Ashe gaba da gabanta, aifa matan anguwa suka dinga shigowa mata murna da sannu da zuwa.
      Matan gidansu Munaya bak’inciki tamkar zai karsu, saidai babu damar koda yin tari, saidai kukan zuci da bak’incikin hassada mai cinye farin cikin Bawa.
******
        Washe gari Galadima yatashi dad’an dama-dama, dan babu zazza6in sai ciwon kai, shima bamai tsananiba irin na jiyaba.
     Da safen yake sanarmin nayi shiri wai zamu koma, mamaki ya kamani, wannan wace irin tafiyace haka babu shiri, bayanma naji yanata kukan rashin kud’i a tsakaninnan, saidai banida damar Musawa, dan inason zuwa naga jikin Abie nima.
     
    Da yake tafiyar saida yamma, tashin hantsi muka shiga cikin gida gaida mutane, fada Ce kawai bamujeba, sai yaran aka kai can, kowa yana yaba k’yawu da girman da yaran suka k’ara, gimbiya zulfa dai bata yarda mun gantaba, wai batada lafiya tana kwance.
       Bamuce komaiba muka fito, mun iske Galadima yana fada, dan haka muka cigaba da shirye-shiye, sai a waya na kikkira mutane mukayi bankwana, naso had’uwa da Aunty Salamah dan inason ta warwaremin wasu tambayoyi, to amma hakan bata samuba, ko gidansu baba mai k’anwa ban lek’aba, kuma wlhy naso hakan matuk’a, to amma ga ayanda tafiyar tazo babu shiri.
      K’arfe 2:00 mukabar masarautar gagara badau zuwa masarautar su papi, tarba akai mana ta mutunci, ina mamakin yanda suke matuk’ar k’aunar Galadima, Sauban tamkar zaiyi rawa dan dad’i, ammafa yayi 6ul-6ul dashi alamar yanashan gata, dukda lokacinmu k’urarrene munsha fira, inno tsohuwar mutunci, yanda take jana ajiki abin ba’a magana.
    Galadima ma tunda suka gaisa da papi da mutane saiya shige cikin d’akin inno ya kwanta, dan bayason yawan hayaniya, saida akayi magrib muka baro masarautar cikeda d’unbin alkairin wad’annan bayin ALLAH, alkairi  sosai Galadima yay ma laraba, harda hawayenta nima haka, dan munyi sabo sosai, bansan miyasa Galadima baice mutafi har itaba, kokuwa matsalar kud’ice oho, lallai na yarda sabo Turken wawa, shi akema kuka ba mutuwaba. Nuren ya d’auke mu.
      Mun biya gidan Mom, itama dai haka tasha hidima damu, saidai akwai yarinyarta ta biyu nakula tun a wancan zuwan bata yina, dan ko gaisheni bama yi takeba, tata yatsine-yatsine kenan, a wancan zuwan abin yad’an dameni, amma yau ko a jikina, dan abinda na lura dashi son Galadima takeyi, dan haka na watsar da lamarinta ko kallo bata isheniba, babu mai takani na zauna, babu ruwana da arzik’inka ko ahalinka, ka mutuntani nima na mutuntaka saimu zauna lafiya.
    Wanda takeyi donshi d’inma ko kallo bata isheshiba, dan baya sakar musu fuska, duk shakkarsa sukeyi har babban wan nasu gaba d’aya, dan ko sauban ya girmeshi balle Galadima.
        Bamu bar gidanba saida time d’in tashin jirginmu ya matso, dan tacan zamu wuce, dukansu gidan sukai mana rakkiya har airport, har saida sukaga tashin jirginmu.
 ******
      Abin ya had’emin da yawa kam, ga yara ga babansu daba lafiya, sauk’inama basuda yawan rigima, Abdurraheem ne dai idan yaji ya takura babu zaman lafiya, Alhmdllh ALLAH dai ya taimakemu mun Isa lafiya, Khumar da Samha, aunty Mimi sukazo tararmu, bama tamu sukeba ta yaran sukeyi, ganin haka Galadima yaja hannuna muka shige mota, saida suka gama murnarsu sannan suka shigo, aunty Mimi na fad’in, “Oh shine kuka shige mota?”.
         Galadima yabata amsa da cewa, “Tunda batamu akeba mizamu zaunayi”.
     Dariya ta sanya da fad’in “yau naga kishi, to kuma dai sannunku badan halinkuba”.
     Murmushi nayi ina gaisheta, Samha ta mak’alk’aleni.
    Haka dai muka k’arasa gida.
       Momma da jakadiya duk suna a harabar gidan da sauran hadimai mazan da mata. Kowa burinsa yaga yaran. Momma dai Nita rungume tanamin oyoyo. Kunya dukta kamani, ina k’aunar wannan baiwa har cikin raina wlhy.
    Galadima kam jingina yay da mota kawai yana kallonsu cikeda jin dad’in yanda kowa ke farin cikin dawowar iyalansa.
     Saida muka shiga ciki sannan Momma kecewa “Ina uban gayyar wai?”.
      Galadima dake shigowa a k’arshe yace, “gani a anan, naga batani akeba Momma shiyyasa naja gefe”.
     Duk dariya mukayi, yayinda bayin sukai k’asa da kai duk suna k’umshe tasu, dan babu damar yi.
     
        An shiga gaishe-gaishe damana sannu da zuwa, hadiman gidan duk suka fice aka barmu mu kad’ai.
      Momma duk tana rungume da jikokinta wad’anda suke rikid’ewa ruwa biyu, kamannin Galadima da Munaya, Khaleel ma yabi ya mamuk’e mata.
     Galadima ya mik’e ya haye sama, danya d’an watsa ruwa, gashima magrib tagabato anan.
    Momma harda hawayenta najin dad’i da farin ciki.
      Tofa lamari ya canja salo, a wannan karon dai maimakon Momma tace nabi mijina saitace na shiga d’akinta nayi wanka na huta, aunty Mimi kuma ta kwashi yaran da taimakon Samha zata musu wanka.
     Nikam hakan yamun dad’i, dan dama banason zama d’aki d’aya dashi. A d’akin Momma nai wanka na canja kayana, ina shirin kwanciya Samha ta shigo kirana wainazo naci abinci.
      Galadima yay ta zuba idon shigiwar Munaya amma saiyaji bulum. Da farko bai kawo komai a ransaba yashiga toilet danya watsa ruwa, jikinsa babu k’arfi har lokacin, dayake d’akin tsaf yake an gyara ko ina fes yanata k’amshi.
     Mamaki yakuma kamashi daya fito har sannan babu Munaya babu dalilinta, ko mai bai shafaba ya zura jallabiya ya sakko, Momma na zaune a falo, harya gama sakkowa idonta na kansa, duk sai ya rame mata a ido, ga hancinsa yay jajir alamar mura tamasa ligif, tissue d’in hannunsa ya ajiye sannan ya zauna.
     Momma tace, “Sannu Muh’d dukka rame, mura na wahalmin da kai wlhy”.
     Murmushi yad’anyi yana shafa sajensa. Yace, “My Sweet Momma to yaza’ayi, yanzu hakama kaina ciwo yake, ya muka sameku?”.
     “Lafiya lau, sai kewarku, ya kuka baro manasu da autana?”.
       “kowa lafiya, Autanki nacan nama inno ta6ara, bakiga yanda yay k’iba ba ma”.
        Momma tayi dariya tanacewa, “Ja’iri, da yanata zum6ure-zum6ure bazaijeba, bagashi haryaci wata kusan uku ba, kwana nawa zai gama”.
     “Dama ai shagwa6ace Momma”.
      Momma tayi murmuahi tana maida kallonta ga jakadiya dake maganar ga abinci.
      Sannu Tamata, ta kalli Galadima daya jingina da kujera ya lumshe ido.
      “Muh’d tashi ga abinci ko, kasamu ka kwanta ka huta”.
      Idonsa ya bud’e yana mik’ewa, saiga Samha da aunty Mimi sun fito suma. momma tace, Samha ta kira Munaya tazo taci abinci.
       Galadima yanaji amma baice uffanba, saima maida hankalinsa yayi ga abincin da Aunty Mimi ke zuba masa.
      Ya faracin abincin Samha da Munaya suka fito, kallo d’aya yamusu ya d’auke kansa zuciyarsa na mamakin miya kaita d’akin Momma?.
    Duk Momma na kula dashi.
    Itama Munayar kallonsa tad’anyi ta d’auke kai.
  
        Haka akaci abincin duk hirar dasu Momma sukeyi da Munaya Galadima baice uffanba, cin abincin sa kawai yakeyi, baima wani ci da yawaba ya matsa gefe alamar ya k’oshi.
    Aunty Mimi tace, “my K’ani Yaya dai?”.
        Yad’an yamutse fuska da fad’in “Alhmdllh ya isheni”.
      “Ai kai dama tsiyar murarka kenan wlhy Sameer, ta jigataka ta hanaka cin abinci, ALLAH ya kara sauk’i”.
      Cikin lumshe ido ya amsa da amin a saman la66a.
    Muma duk sannu mukai masa, ya d’aga mana kai kawai.
    Koda muka had’a ido saiya zubamin wata harar gargad’i, murmushi nayi na kauda kaina gefe tamkar ban ganiba…………………????
ALLAH ya gafartama iyayenmu????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button